An Maka Gwamnatin Neja Da NBC A Kotu Kan Barazanar Rufe Gidan Rediyon Badeggi FM
Published: 10th, August 2025 GMT
Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali.
Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE suna neman sani “ko a sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 2(1) (t) na dokar NBC, NBC na da hakkin kare ‘yancin Badeggi FM da gwamnan Neja ya rufe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Hisbah Ta Rufe Wani Wuri da Ake Zargin Ana Aikata Badala A Kano
Daga Khadijah Aliyu
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu samari bakwai da ke shiga irin ta mata da aikata badala a wani shahararren gurin nishadi da ke kan titin Zoo Road a karamar hukumar Kano Municipal.
Yayin tabbatar da faruwar lamarin ga Rediyon Nijeriya, Mataimakin Kwamanda Janar na hukumar Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar, ya ce an kama samarin da ke kasa da shekaru 23 bayan samun bayanan sirri daga wani mai kishin ƙasa.
Mai bayar da bayanan ya sanar da cewa mmatasn da aka fi sani da ‘Yan Daudu, suna yawan zuwa wurin, inda ake zargin cewa motocin mutane daban-daban ke zuwa su ɗauke su.
Sheikh Mujahid ya bayyana cewa binciken farko ya nuna cewa matasan sun fito ne daga jihohin Kogi, Bauchi da Kano.
Ya ƙara da cewa yayin gudanar da aikin, jami’an Hisbah sun kuma kama wani saurayi da wata budurwa da aka same su tare a cikin babur mai ƙafafu uku, sannan kuma an gano wata yarinya da aka ce ta bace a Sakkwato, aka kuma maida ta ga iyayenta.
Mataimakin Kwamanda Janar din ya ƙara da cewa hukumar za ta rufe wurin nishadin saboda zargin ɓoye ƙananan yara da ke aikata munanan ayyuka.
Ya ce za a mika matasan da aka kama tare da masu kula da wurin ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da daukar mataki.
Sheikh Mujahid ya tabbatar da jajircewar Hisbah na kawar da dukkan nau’o’in munanan dabi’u a jihar, tare da kira ga jama’a da su rika kai rahoton duk wata matsala ko abin da suke shakku ga hukumar Hisbah ko wasu hukumomi da suka dace.