Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore
Published: 7th, August 2025 GMT
Ana zargin ‘yan sandan da karya hannun Sawore
Ana zargin wasu ‘yan sanda daga Sashen Binciken ‘yan sanda na Qasa sun kutsa inda Hukumar ‘Yan sanda ta Qasa ke tsare xan gwagwarmayar neman haqqin bil’Adama Omoyele Sowore a Abuja, inda suka fita da shi da qarfin tuwo zuwa wani wuri da har yanzu ba a sani ba.
Haka kuma kamar yadda Sowore ya sanar a shafinsa na sada zumunta na Facebook, ya yi zargin cewa an karya hannunsa yayin da jam’an suka finciko shi da qarfin tsiya daga inda yake tsare wajen qarfe 6:00 na safiyar yau Alhamis a qoqarinsu na kai shi kotu ba tare da sanar da lauyansa ba..
jiya Laraba ne dai Sowore ya masa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ‘Yan sanda na Qasa ya yi masa don ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaqa da zanga-zangar da tsofaffin ‘yan sanda suka yi a makon jiya da kuma zargin da Sowore ya yi na cewa, Babban Sufeton na Qasa ya qara wa jami’an ‘yan sandar da ke aiki a gidansa girma ba bisa qa’ida ba.
Sai dai xan rashin kare haqqin xan’Adan xin ya yi watsi da zarge-zargen inda ya bayyana su a natsayin borin kunya da hukumar ‘yan sandan take don xauke hankalin jama’a daga abin kunyar da Babban Sufeton na Qasa Kayode Egbetokun da kuma Hukumar ‘Yansada ta Qasa ke aikatawa.
Tuni dai Qungiyar Kare Haqqin Bil’Adama ta Duniya wato Amnesty International ta fitar da sanarwar yin Allah wadai da kamun da hukumar ‘yan sandan ta Nijeriya ta yi wa Sowore wanda ta ce ya sava wa ‘yancinsa na faxain albakacin bakinsa.
Haka kuma Amnesty International ya buqaci a sake Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharuxxa ba.
Shi ma Dakta Bello Galadanci xan gwagwarmayar rajin kare haqqin xan’Adama da aka fi sani da suna Xan Bello, ya yi tir da kamun da aka yi wa Sawore tare da kiran a sake shin an take kamar yadda ya rubuta a shafinsa na Facebook inda ya ce, “ana tsare mutum ba bisa ka’ida ba, sai a kuma karya masa hannu? A tafi da shi kamar dabba ba tare da sanar da danginsa ko lauyoyinsa ba?
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sanata Barau Zai Yi Ƙarar Zargin Karɓar Cin Hancin Dala Miliyan 10
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugaba Tinubu Da Shugaban Ƙasar Saliyo, Sun Yi Ganawar Sirri A Abuja November 8, 2025
Manyan Labarai Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC November 8, 2025
Manyan Labarai Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma November 7, 2025