2025-09-17@21:53:48 GMT
إجمالي نتائج البحث: 30

«rayuwar matasa»:

    Wata budurwa mai shekaru 24 mai suna Kelechi Ebubechukwu, ta rasu a cikin wani yanayi da mai daure kai a gidan saurayinta da ke Gwagwalada, Babban Birnin Tarayya Abuja. Wani ƙwararren masani kan tsaro, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba. A cewarsa, lamarin ya faru ne a ranar Talata. Mota ɗauke da tabar wiwi ta yi hatsari a Kano, ta faɗa hannun jami’an NDLEA Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki  Majiyoyin ’yan sanda sun ce binciken farko ya nuna cewa marigayiyar na fama da zazzabin cizon sauro kafin rasuwarta. A cewar mjiyoyin, an samu takardar da ke dauke da rubutun magungunan da...
    Wasu mazauna unguwar Oworonshoki da ke ƙaramar hukumar Kosofe a Jihar Legas, sun datse wani sashe na gadar Third Mainland a ranar Litinin, a wata zanga-zanga da suka gudanar don nuna adawa da rushe musu gidaje. Datse hanyar da suka yi ya haddasa cunkoson masu ababen hawa da fasinjoji, lamarin da ya tilasta wa ’yan sanda tarar hanzarin lamarin, inda suka riƙa harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zangar-zangar. MDD ta buƙaci hukumomin Najeriya su kamo waɗanda suka kai hari a Bama Yarima Harry ya ziyarci kabarin Sarauniya Elizabeth II Aminiya ta ruwaito cewa, tun a watan Yulin 2023 aka soma rusau ɗin, lamarin da ya raba wasu mazauna unguwanni kamar Oke-Eri, Odunfa Lane, Ogo-Oluwa, Precious Seed, Coker da kuma...
    Yayin da makarantu a fadin Najeriya ke dawowa sabuwar zangon karatu ta shekarar 2025/2026 a yau Litinin, iyaye sun koka kan mummunar ƙalubalen tattalin arziki da ke hana su samun sauƙin biyan kuɗin makaranta da sauran kayayyakin karatu. Rahotanni daga jihohi daban-daban sun nuna yadda tsadar rayuwa da hauhawar farashin kaya suka zame wa iyaye da ɗalibai babban cikas, inda wasu ke neman rance domin ganin ’ya’yansu ba su zauna a gida ba. Kukan Iyaye A hirarraki da aka yi da iyaye da dama, sun bayyana cewa duk zangon karatu yanzu yana zama tamkar shiga jana’iza, inda suke binne albarkatunku da nutsuwarsu da farin cikin gida. Misis Victoria Edem, uwa ce mai yara uku daga garin Kalaba a Jihar Kuros...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.   “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.   “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    “A yau (Ranar Laraba) majalisar zartaswa ta yi la’akari da batun ƙarin kuɗin fansho ga tsofaffin ma’aikatan jiharmu da suka yi ritaya, hakan ya biyo bayan ƙarin mafi ƙarancin albashin ma’aikata da kuma mafi ƙarancin kuɗin fanshi na ƙasa da gwamnatin tarayya ta amince da su,” in ji shugaban ma’aikatan.   Barista Sani ya ƙara da cewa, tun ma kafin wannan ƙarin, hatta adadin mafi ƙarancin fansho da jihar Bauchi ke biya a baya na Naira dubu 12, wasu jihohi da dama ba su ma biyan irin wannan, ga kuma sabon ƙari da suka amince dukkan domin kyautata rayuwar tsofaffin ma’aikata a faɗin jihar.   Ya misalta amincewar a matsayin kyakkyawar yunƙurin gwamna Bala Muhammad na kyautata rayuwa da jin...
    Bankin Duniya ya amince da bayar da dala miliyan 300 domin aiwatar da wani sabon shiri da zai inganta rayuwar ’yan gudun hijira da kuma al’ummomin da suka ba su matsugunni a Arewacin Nijeriya.  Bankin ya bayyana cewa a ƙarƙashin shirin mai suna Solutions for the Internally Displaced and Host Communities Project wato SOLID, wanda aka amince da shi a ranar 7 ga Agusta, za a lalubo hanyoyin da za a bi wajen taimakon ’yan gudun hijira, da ma garuruwan da suke rayuwa a ciki. Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai Nijeriya ta sake ƙulla alaƙar tsaro da Isra’ila Ya bayyana cewa shirin SOLID zai ruɓanya ƙoƙarin da gwamnati ke yi da ma wanda...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara. Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar. A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba. Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi? NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu...
    Sai dai girma, kima da ɗaukakar da matasa ke da ita ga al’umma ta ja baya ƙasa sosai a bisa ga yadda rayuwarsu ke iyo da ninƙaya a kogin  zubar da mutunci ta hanyar aiwatar da abubuwan da ke da alamar ayar tambaya. Matasa da dama a yau ba su ganin kowa da gashi, ba su girmama kowa, ba su ganin mutuncin kowa, ba su daraja kowa ballantana har a tsawata masu ko a ba su shawara da ɗora su kan hanyar yadda za su daidaita rayuwar su daga gurɓatacciyar hanya zuwa madaidaiciyar hanya. Abin takaici ne da matuƙar damuwa yadda matasa suka gurɓata rayuwarsu mamakon amfani da lokaci da damar da suke da ita amma sai suka zaɓi biyewa...
    Ana zargin wata uwa a jihar Enugu da kashe ’ya’yanta biyu saboda tsananin kuncin rayuwa. Lamarin ya faru a unguwar Trans Ekulu da ke yankin birnin na Enugu. An kone babur din ‘barayin waya’ a Kano Natasha za ta sake komawa kotu kan hana ta shiga harabar majalisa An ga gawarwakin yara biyu a gidan lokacin da jami’an tsaro sukashiga ciki, lamarin da ya tayar da hankulan jama’ar unguwar. Yaran da ake zargin uwar tasu da kashewa sun hada da yarinya mai suna Esther Arinze mai shekara hudu da haihuwa da kuma kaninta mai suna  Chibusoma. Ana zargin an yi amfani da makami mai kaifin gaske wajen ji wa yaran raunuka a jikunansu kafin su rasu. Majiyar labarinmu da rundunar...
    Yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya saurari rahoton aiki na kananan hukumomin lardin Shanxi, tare da gabatar da wasu bukatu na ayyuka na mataki na gaba na wurin. Xi ya ce, gina wani yankin gwaji na gyare-gyare na kasa, domin kawo sauyi kan tattalin arziki bisa albarkatun kasar, wani muhimmin aiki ne da kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta Sin ya dorawa lardin Shanxi, don haka ya kamata a mai da hankali kan sauyin makamashi, da habaka masana’antu, da kuma samu ci gaba da ya dace. Bugu da kari, Xi ya jaddada cewa, dole ne a tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali yayin kawo sauyin ci gaba. Dole ne mu mai da hankali kan daidaita ayyukan yi, masana’antu, kasuwanni,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Zaɓaɓɓun shugabannin gwamnati sukan naɗa wasu muƙarrabai don su taya su sauke nauyin da aka ɗora musu. Wasu na zargin naɗin ba ya rasa nasaba da sakayya ga irin rawar ga waɗanda aka naɗa saboda rawar da suka taka yayin yaƙin neman zabe. Shin irin waɗannan nade-naɗe na da wani tasiri ga rayuwar al’umma? NAJERIYA A YAU: Shin Ko Hadakar Sabuwar Jamiyyar ADC Za Ta Fidda Wa ‘Yan Najeriya Kitse Daga Wuta? DAGA LARABA: Cutukan Da Sinadaran Yin Burodi Ke Haifarwa Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan nade-naɗen masu taimaka wa shugabanni da irin tasirin da suke da shi. Domin sauke shirin, latsa nan
    A ranar 28 ga watan Yuni, 2025, Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin fitattun ’ya’yanta, Alhaji Aminu Alhassan Dantata bayan ya shafe shekaru 94 a duniya.  Ya rasu a birnin Abu Dhabi na ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) wanda rasuwarsa ta kasance wani babban giɓi a tarihin ci gaban Najeriya, musamman a fannin tattalin arziƙi da tallafa wa marasa ƙarfi. Kebbi: PDP za ta yi haɗaka don ƙalubalantar APC a zaɓen 2027 Mutanen Sakkwato na neman ɗaukin gwamnati game da Bello Turji Wannan rashi na Dantata babban al’amari ne da ya shafi Najeriya da ma Yammacin Afirka baki ɗaya. Aminu Dantata ya kasance mutum mai tasiri a fannonin kasuwanci, hidimar jama’a, addini da ayyukan jin-ƙai. A wannan zamani da...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Babu makawa Amurka abokiyar laifukan da yahudawan sahayoniyya suke aikatawa ne a Gaza A safiyar yau Alhamis ne Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya gabatar da kira ga mahajjatan dakin Allah. Yana mai jaddada cewa; Aikin Hajji ba kamar sauran tafiye-tafiye ne da ake nufi kasuwanci, yawon bude ido, ko wasu abubuwa daban-daban ba, wadanda wani lokaci sukan hada da ibada ko ayyukan alheri. Motsa jiki ne na ƙaura daga rayuwar da ta saba zuwa rayuwar da ake so. Rayuwar da ake so ita ce rayuwar tauhidi, wacce ta kunshi muhimman abubuwa masu muhimmanci na dindindin kamar: dawafi akai-akai a kusa da kusurwoyin gaskiya, da jajircewa a tsakanin...
    Rundunar ’yan sandan Kano ta sanar da kama wani matashi bisa zargin kashe saurayin ƙanwarsa da ya wanke ƙafa ya tafi zance gidansu. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a shafinsa na Facebook. Mahaifin tsohon Gwamnan Kaduna ya rasu Kwalara ta yi ajalin mutum 4 a Filato Kiyawa ya bayyana cewa matashin ya fito da gora kuma ya buga wa saurayin da ya je zance gidansu a ƙauyen Kunya da ke Ƙaramar Hukumar Minjibir a Kano. Sanarwar ’yan sandan ta ce matashin wanda ɗan asalin ƙauyen Goda, ya je Kunya ne wajen budurwarsa domin zance. Sai dai jim kaɗan bayan zuwan nasa sai aka yi...
    Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto jagoran yana bada umurni ga ma’aikatar shari’aa a kasar ta gudanar da cikekken bincike don sanin abinda ya faru saboda daukar matakan da suka dace don hana irin wannan sake faruwa nan gaba, sannan idan akwai wadanda suka yi kuskure a hukunta su. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gobarar da ta taso...
    Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar. Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar. A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai. Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu. Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa...
    An tsinci gawar wani matashi da budurwarsa a tube bisa gado a cikin dakinsa a yakin Alo da ke Karamar Hukumar Ankpa a Jihar Kogi. An tsinci gawara masoyan ne a gidan hayan da saurayin ke zama ranar Juma’a da ta gabata. Mai gidan hayan mai suna Salisu Ibrahim ne ya nemi agajin jama’a sakamakon rashin ganin matashin ya bude kofarsa da safe kamar yadda ya saba. Daga nan ne ya sanar da dan uwan matashin da kuma ’yan sanda, inda suka so aka balla kofar dakin, inda aka samu masoyan sun kwanta dama. Mutanen da aka kashe a Binuwai sun ƙaru zuwa 72 HOTUNA: An yi zanga-zangar adawa da matsalar tsaro a Filato NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban...
    Hatsarin mota ya yi ajalin mutum biyar tare da jikkatar wasu takwas a yayin da suke bikin Ista a garin Billiri da ke Jihar Gombe. Hatsarin ya faru ne a safiyar ranar Litinin, lokacin da direban wata babbar mota mai ɗauke da buhunan hatsi daga Jihar Adamawa ya auka kan dandazon jama’a da ke tsaka da shagalin bikin Ista. An jingine wasanni a Italiya saboda mutuwar Fafaroma Francis An kama tsohuwa kan zargin lalata da almajiri a Bauchi A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi gaggawar kai ɗauki, inda suka kwashe waɗanda suka jikkata zuwa asibiti. Sanarwar ta kuma ce bayan faruwar hatsarin,...
    Ilimi Gishirin Rayuwa Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko...
    Rasuwar Sheikh Dakta Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi rasuwa ce da ta jijjiga al’ummar Nijeriya da ma ƙasashen ƙetare, bisa la’akari da irin faɗakarwarsa da karantarwarsa da gwagwarmayarsa. Hakan ya jawo dandazon al’ummar Musulmi suka halarci sallar jana’izarsa kuma fitattun mutane da malamai suka yi ta yin ta’aziyyar rasuwarsa. Lokacin da Malamin yake raye kusan a kulum sai ya gabatar da huɗuba ko darasi na wayar da kan al’umma ko kuma ilmantar da su kan wani abu mai muhimmanci a masallacinsa da makarantarsa. A ’yan shekarun nan Allah Ya jarrabe shi da rashin lafiya, wanda a sanadiyyar haka ya xauki tsawon lokaci ba a ji huɗubarsa ko karantarwarsa ba da suke xaukar hankalin dubban masu sauraro a faɗin Afirka, lamarin...
    Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi. Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    “Gwamnati gaba daya ta dogara ne kan yadda za ta kyautata rayuwar jama’a, mun dauki lamarin matasa da muhimmanci sosai.” Ya tabbatar wa matasan cewa gwamnatinsa a kowani lokaci a shirye take wajen yin ayyukan tukuru domin kyautata rayuwar matasa da saukaka matsalolin da Nijeriya ke fuskanta. Kan kwamitin da ya kaddamar, Tinubu ya kalubalancesu da su yi aiki tukuru domin ganin rayuwar matasa ya samu tagomashi a kowani lokaci. Shi kuma a jawabinsa, ministan bunkasa harkokin matasa, Ayodele Olawande, ya ce, kwamitin za su yi aiki sosai wajen ganin an samu inganta shigo da matasa cikin sha’anin mulki. Olawande ya lura cewa gwamnatin Shugaba Tinubu gwamnati ce mai saurare da ke shirye ta mai da hankali tare da hada...
    Rahotanni da ke fitowa daga kasar suna nuni da cewa, Yawancin fararen hula da aka kashe a tashe-tashen hankulan da suka faru a wannan Juma’a, dakarun sabuwar gwamnatin kasar ta Syria ne suka kashe su, kamar yadda binciken kungiyar kare hakkin bil Adam ta (SOHR) ya tabbatar. Ayyukan tashe-tashen hankulan sun yi sanadin Kisan mutuwar fararen hula 162 a lardunan gabar tekun Syria, ciki har da mata da kananan yara, in ji rahoton kungiyar ta SOHR. Akasarin wadanda aka kashe dai kamar yadda aka gani a wasu fayafayin bidiyo da aka dauka, jami’an tsaron sabuwar gwamnatin Syria ne da suke da alaka kungiyoyi masu tsatsauran ra’ayi irin su Tahrir Sham da makamantansu da suke da alaka da Alqaida ne suka...
    Ƙamshi abin so ne a wurin kowa. Mata su kasance suna saka turaren wuta a kullum. Su mayar da shi dole kamar yin wanke-wanke. Ko kun san cewa, wannan turaren wutar za a iya amfani da shi da kabbasa domin turara zanin gado da rigar sawa? An horas da masu unguwannin Katsina kan sasanta jama’a Ramadan: Gwamnatin Jigawa ta rage lokacin aiki Bayan haka, akwai turaren humra wadda za a iya shafa shi a gashin kai. Akwai na hammata daban sannan akwai na shafawa kamar mai, wanda aka fi sani da kulacca da kuma na riga. Lallai duk macen da ta kasance cikin ƙamshi, za ta sami girmamamwa a cikin al’umma da kuma mai gidanta. Kuma akwai turaren kanti kamar...
    Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya. Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini. Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki....
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano Shigo da hatsi daga ƙetare ya karya farashinsa a Neja Idan aka dubi labarin Mariano Grinspun, ɗan shekara 23 daga González Catán, wani birni a lardin Buenos Aires na Argentina, wanda budurwarsa mai tsananin kishi ta caka masa wuka wanda ya yi sanadiyya mutuwarsa bayan ya gaisa da wata tsohuwar abokiyar karatunsa a titi, za a ga abin akwai ban mamaki. Abin ya faru ne...
    Shugaban Majalisar Wakilai Dr Abbas Tajuddeen, ya bayyana kaduwarsa bisa rasuwar fitaccen dan kasuwa kuma mai taimakon jama’a, Alhaji Bala Abdulwahab da ke Zariya, wanda aka fi sani da Albabello. A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai Malam Musa Abdullahi Krishi ya fitar, Dakta Abbas Tajuddeen, ya ce masarautar Zazzau da jihar Kaduna sun yi rashin babban dan kasuwa wanda ya sadaukar da rayuwarsa gaba daya wajen yi wa al’umma hidima. Shugaban majalisar ya jaddada cewa, Albabello, ta hanyar sahihancinsa na kasuwanci, ya samar da ayyukan yi ga dubban jama’a a Zariya da ma fadin kasar nan, ta hanyar amfani da rassan kamfaninsa daban-daban. Ya ci gaba da cewa Albabello, ya kuma...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta kashe sama da naira miliyan dubu dari da sittin da hudu wajen tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da rabon katin cire kudi na ATM ga wadanda suka ci gajiyar shirin inganta rayuwar al’umma na gwamnatin tarayya da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar Dutse. Malam Umar Namadi ya bayyana cewar, hukumar bunkasa tattalin arziki ta jihar ce ta fitar da ta hannun shirin farfadowa daga annobar cutar corona. A cewar sa, kusan mutane dubu ashirin da uku ne za su amfana da tallafin naira dubu saba’in da biyar a jihar. Yana mai cewar, hakan na daga cikin kudirin shugaban kasa na Renewed Hope agenda...
۱