Leadership News Hausa:
2025-11-27@23:00:18 GMT

‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno

Published: 11th, August 2025 GMT

‘Yan Ta’addar ISWAP Sun Kashe Shugaban Mafarauta A Borno

Wasu da ake zargin ‘yan ta’addar ISWAP ne sun kashe shugaban kungiyar mafarauta a kauyen Garjang da ke karamar hukumar Damboa a jihar Borno. Majiyoyi, a cewar Zagazola Makama, kwararre a fannin yaki da ‘yan tada kayar baya, ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na safiyar Lahadi. Kungiyoyin Kwadago Sun Tsunduma Yajin Aiki A Taraba Inganta Harkokin Gwamnati: Oyebanji Ya Sauke Kwamishinoni 19 Wanda aka kashe mai suna Habu Dala mai shekaru 53, ‘yan ta’addan ne suka dauke shi daga gidansa, inda suka bi da shi ta hanyar Mulharam zuwa kauyukan Forfot da ke karamar hukumar Damboa.

An tattaro jama’ar kauye ne domin neman Dala amma daga baya suka tarar da gawarsa dauke da raunukan harbin bindiga, inda Dakarun Operation Hadin Kai, ‘na Civilian Joint Task Force (CJTF)’, da kuma ‘yan kungiyar mafarauta suka ziyarci wurin. An kai gawar mafaraucin da ya rasu zuwa babban asibitin Damboa, inda aka tabbatar da mutuwarsa, daga bisani kuma aka mika shi ga iyalansa domin yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro da ta addabi dukkan sassa a Nijeriya.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar mai ɗauke da sa hannunsa, Tinubu ya bayyana cewa dole ne a ɗauki matakan gaggawa da suka dace domin fuskantar barazanar tsaro da ke ƙaruwa ƙasar nan.

Shugaban ya bayar da umarnin ɗaukar ƙarin jami’an tsaro da suka haɗa da jami’an ’yan sanda 20,000, lamarin da zai ƙara adadin jami’an da za a ɗauka zuwa 50,000, bayan umarnin da ya bayar a ranar Lahadi na ɗaukar jami’an tsaro 30,000.

Real Madrid za ta yi karon-batta da Olympiacos a Gasar Zakarun Turai Tinubu ya aike wa Majalisar Dattawa sunayen jakadu

Haka kuma, Tinubu ya bai wa rundunar sojin ƙasa da sauran hukumomin tsaro umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai.

Sanarwar ta ce za a yi amfani da sansanonin masu yi wa ƙasa hidima NYSC a matsayin wuraren horas da sabbin ’yan sandan.

Kazalika, shugaban ya bai wa hukumar ’yan sandan farin kaya ta DSS umarnin ɗaukar ƙarin jami’ai a rundunar kare dazuka wato Dakarun Gandun Daji ta Forest Guard.

Shugaba Tinubu ya kuma umarci DSS ta aika dakarun Forest Guard “domin zaƙulo ’yan ta’adda da ’yan fashi daga dazuka.”

“Babu wani sauran gidan ɓuya ga miyagu,” in ji shi kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewar, za a sake horar da jami’an ’yan sanda da aka janye daga gadin fitattun mutane kafin mayar da su aikin ɗan sandan gada-gadan.

Shugaban ya yi amfani da damar wajen jinjinawa hukumomin tsaro wajen kuɓutar da mutane 34 da aka sace a Mujami’ar Kwara da ɗalibai 24 da aka sace a makarantar jihar Kebbi, yayin da ya ce suna ɗaukar matakan da suka dace wajen kuɓutar da ɗaliban makarantar mabiya ɗarikar Katolika da ke Jihar Neja.

Tinubu ya jinjinawa rundunar sojin ƙasar a kan gudumawar da jami’anta ke bayarwa da kuma gabatar da ta’aziyar rasuwar Janar Musa Uba da ƴanta’adda suka yiwa kisan gilla, yayin da ya buƙace su da su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a yankunan da ake fama da tashin hankali.

Shugaban ya buƙaci majalisar ƙasa da ta sake fasalin dokokin tsaro domin bai wa jihohi damar samar da ’yan sanda na kashin kan su, yayin da ya ce gwamnatin tarayya za ta taimaka musu.

Tinubu ya kuma buƙaci Masallatai da Majami’u da su dinga neman taimakon jami’an tsaro a duk lokacin da za su gudanar da taron ibadun su, musamman a yankunan da ake fama da matsalar tsaro.

Shugaban ya kuma jajanta wa gwamnatoci da kuma mutanen jihohin Kebbi da Borno da Zamfara da Neja da Yobe da kuma Kwara saboda kisan gillar da ƴan ta’adda suka yiwa mutanen su.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Wakilai ta nemi gwamnati ta gaggauta dauko Jonathan daga Guinea Bissau
  • Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci kan matsalar tsaro
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Falasdinu Ta Sanar Cewa Akalla Yan Mata 33000 Ne Isra’ila Ta Kashe A Gaza
  • Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000
  • Ko sisi ba a biya ’yan bindiga ba kafin su saki ɗaliban da suka sace – Gwamnan Kebbi
  • ’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
  • Hizbullah: Isra’ila na kuskure idan ta na tunanin kashe-kashen kwamandodinmu zai kawo karshen kungiyar
  • Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza
  • Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a Katsina
  • Gobarar tankar mai ta ƙone gidaje a Jihar Neja