Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza
Published: 11th, August 2025 GMT
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da zaman gaggawa a hedikwatar MDD da ke birnin New York a jiya Lahadi, bayan matakin da majalisar ministocin Isra’ila ta dauka na fadada ayyukan soji da kuma mamaye yankin zirin Gaza.
Mataimakiyar Sakatare-Janar mai kula da harkokin Turai, Tsakiyar Asiya da Amurka, Miroslav Jenča, ta jaddada a yayin zaman cewa, “ba za a iya dakatar da dimbin wahalhalun jin kai da ake fama da su a Gaza ba, sai ta hanyar tsagaita bude wuta nan take kuma mai dorewa,” tana mai kira da a gaggauta sakin dukkan fursunoni ba tare da wani sharadi ba.
Jenča ta yi kira ga Isra’ila da ta bi abin da ya rataya a wuyanta a karkashin dokar jin kai ta kasa da kasa, ta ba da damar isar da kayan agaji cikin gaggawa kuma cikin aminci, ba tare da tsangwama ko kawo cikas ga wanann shiri ba, da kuma barin isar da kayan ga jama’a, tana mai jaddada bukatar “kare fararen hula, gami da ma’aikatan jin kai da masu neman taimako.”
A nasa bangaren, wakilin Aljeriya a MDD Ammar Benjamaa ya ce Isra’ila ba ta damu da dokokin kasa da kasa ko kuma bil’adama ba, ya kara da cewa “Isra’ilawa suna nuna rashin tausayi, Rashin Imani da dabi’a na dabbanci, suna kawar da Palasdinawa daga matsayinsu na yan Adam tare da kaskantar da su zuwa matsayin dabbobi kamar yadda suke gani.”
A martanin da ta mayar, wakiliyar Amurka ta dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, Dorothy Shea, ta dora alhakin dukkanin abin da Isra’ila take aikatawa a kan Hamas.
Dangane da matakin da Isra’ila ta dauka na Shirin mamaye Gaza, ministocin harkokin wajen kasashen Australia, Jamus, Italiya, New Zealand, da Birtaniya sun sanar da kin amincewa da matakin na Isra’ila, tare da jaddada aniyarsu ta bai daya wajen aiwatar da yarjejeniyar kafa kasashe biyu ta hanyar yin shawarwari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari August 11, 2025 Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara August 10, 2025 Dangantaka Tsakanin Iran da Saudiya Yana Taimakawa Zaman Lafiya A yankin August 10, 2025 Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba August 10, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya August 10, 2025 An Zabi Alkalan Wasa Biyu Daga Kasar Iran Don Alkalanci A gasar Kwallon Kafa ta Mata August 10, 2025 Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12 August 10, 2025 Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Jefa Agajin Abinci Ta Sama A Zirin Gaza Ya Janyo Shahadan Falasdinawa 23 Tare Da Jikkata Wasu 124 August 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa.
Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi kasar Labanon, tare da jaddada muhimmancin kiyaye yanayin amincewa da daidaito tsakanin bangarori daban-daban na siyasa, da kuma kaucewa duk wani mataki da zai iya haifar da rikici a cikin gida.
Bangarorin biyu sun jaddada bukatar janyewar haramtacciyar kasar Isra’ila gaba daya daga yankunan da take ci gaba da mamayewa a kudancin kasar Lebanon da kuma dakatar da kai hare-hare a kan mutanen kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza August 9, 2025 Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon August 9, 2025 Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci