Manoma sama da 500 daga gundumomi 15 na karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu horo kan kiwon awaki na zamani da kuma yadda ake samar da abincin dabbobi, a wani yunƙuri na rage yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya tare da inganta rayuwar al’ummar karkara.

An gudanar da wannan horo a Idofian karkashin haɗin gwiwar karamar hukumar Ifelodun da shirin Livestock Productivity and Resilience Support Project (L-PRES).

Da yake jawabi a wurin taron, mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mista Kayode Alabi wanda Honarabul Ganiyu Afolabi, dan majalisar jihar mai wakiltar mazaɓar Omupo ya wakilta,  ya jaddada muhimmancin wannan shiri wajen magance matsalolin da manoman karkara ke fuskanta. Ya bayyana cewa shirin ba wai kawai zai rage rikici ba ne,  zai kuma ƙara yawan kudaden shiga ga manoma da kuma ƙarfafa cin gashin kansu.

Ya ja hankalin mahalarta da su yi amfani da damar wajen amfani da sabbin ilimin da suka samu domin faɗaɗa sana’arsu da kuma samar da abincin dabbobi cikin sauƙi ta hanyar amfani da shara daga amfanin gona.

Shi ma da yake jawabi, shugaban karamar hukumar Ifelodun, Honarabul Abdulrasheed Yusuf, ya bayyana cewa wannan shiri zai taimaka wajen samar da ayyukan yi da kuma rage kuɗin da ake kashewa wajen kiwon dabbobi ta hanyar samar da abincin dabbobi a cikin gida.

Ya kuma ƙara da cewa karamar hukumar tana aiki tare da masu ruwa da tsaki don samar da muhimman abubuwa kamar ruwa da wasu muhimman abubuwan raya ƙauyuka.

A nasa jawabin, sarkin Igbaja, Oba Ahmed Babalola (Elesie na Igbaja), ya yabawa wadanda suka shirya wannan horo, yana mai cewa an yi shi a  lokacin da ya dace. Ya tabbatar wa  mahalarta  cikakken goyon baya domin nasara da dorewar shirin.

A baya, shugaban shirin L-PRES a jihar Kwara, Mista Olusoji Oyawoye, ya ƙarfafa matasa da su rungumi dama a fannin noma domin su dogara da kansu maimakon jiran aikin gwamnati. Ya buƙaci mahalarta horon da su rungumi shirin da cikakkiyar niyya domin su samu ƙwarewa da za ta taimaka musu da al’ummarsu gaba ɗaya.

Wannan horo wani ɓangare ne na babban shirin L-PRES da ke ƙoƙarin ƙara yawan amfanin kiwo, rage rikice-rikice, da kuma inganta ɗorewar rayuwa a ƙauyuka a faɗin Najeriya.

Ali Muhammad Rabi’u

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Kwara karamar hukumar

এছাড়াও পড়ুন:

Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina

Wata uwa da ’ya’yanta biyar sun riga mu gidan gaskiya a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya wanda ya janyo ruftawar ginin gidansu a ƙauyen Dankama da ke Karamar Hukumar Kaita a Jihar Katsina.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe biyu na dare a ranar Litinin yayin da waɗanda ajalin ya katsewa hanzari ke tsaka da barci.

Kotu ta hana jagoran adawa Maurice Kamto takarar shugaban ƙasa a Kamaru Mulkin Tinubu ya fi na Buhari muni — Maina Waziri

Bayanai sun ce wasu mutum huɗu waɗanda su ma lamarin ya rutsa da su an gaggauta miƙa su asibiti domin samun kulawa.

Magidancin da aka yi wa wannan babban rashi, Muhammad Sani Garba, yayin ganawa da manema labarai ya ce ba ya gida lokacin da tsautsayin ya auku.

“Wannan tsautsayi ya rutsa da mutum goma, amma abin baƙin ciki, shida daga cikinsu sun rasu. A halin yanzu, mutum huɗu suna asibiti ana duba lafiyarsu,” in ji shi.

“Na ɗauki wannan a matsayin ƙaddara daga Ubangiji. Allah Ya jiƙansu, Ya sanya su a Aljannar Firdausi,” a cewarsa.

Daraktar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Hajiya Binta Dangani, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa ma’aikatan hukumar sun ziyarci wurin da lamarin ya faru domin tantance halin da ake ciki da ɗaukar matakin gaggawa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara
  • Gwamnatin Neja Ta Raba Motoci Ga Ma’aikata Da Hukumomi
  • Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan Daya Domin Ayyukan Jin Kai Sakamakon Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
  • Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
  • Ruftawar gini ta kashe uwa da ’ya’yanta 5 a Katsina
  • FG Za Ta Raba Naira miliyan 3.4m Ga Wadanda Suke Amfana Da Shirin ACReSAL
  • Gwamna Yusuf Ya Raba takardun daukar Aiki Ga Sabbin Ma’aikatan Gona Su 1 ,038
  • Sanata Buba ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi kyauta
  • An Kaddamar Da Shirin Dashen Itatuwan Dabino Miliyan 50 A Jigawa