‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
Published: 7th, August 2025 GMT
Mazauna kauyen Chatta da ke karamar hukumar Hawul a jihar Borno sun fada alhini sakamakon rasuwar wasu mutum hudu ’yan gida daya.
Ba a dai tabbatar da ainihin musabbabin rasuwarsu ba, amma mazauna yankin da lamarin ya faru sun ce suna zargin hayakin injin samar da lantarki na janareta ne ya yi ajalin su.
Majiyoyin da ke kauyen na sun shaida wa rundunar ’yan sandan jihar cewa wadanda suka mutun sun hada da Yakubu Samanja, matarsa Esther Yakubu, da ’ya’yansu biyu, Amos Yakubu da Maryamu Yakubu.
Wani dan uwan mamatan mai suna Ibrahim Samanja, ya ce ya gano faruwar hakan ne a lokacin da ya ziyarci gidan da sanyin safiyar Talata inda ya tarar da gidan gaba daya ba a halin da aka saba gani ba.
“Na zo da misalin karfe 7:00 na safe na yi ta buga kofar gidan amma babu wanda ya amsa, sai na shiga damuwa kuma daga karshe dole na balle kofar, a lokacin ne na ga gawarwakinsu a kwance a cikin dakin,” in ji shi.
Ya kuma ce, “Bayan gano lamarin nan da nan na sanar da hukumomin ’yan sanda da ma’aikatan lafiya yadda ba tare da bata lokaci ba suka ziyarci wurin inda suka tabbatar da mutuwar dukkan ’yan uwan hudu.
“Daga baya an kwashe gawarwakin zuwa babban asibitin garin Marama, inda aka ajiye su a dakin ajiyar gawarwaki domin adanawa da kuma tantance musabbabin mutuwar su.
Mutanen kauyen sun bayyana lamarin a matsayin abin da ya dame su kuma sun ce mamatan kafin nan ba su nuna alamun wata rashin lafiya ko damuwa ba kafin mutuwarsu ta farar daya.
Sun ce binciken farko da aka yi a wurin ya nuna babu wani alamun tashin hankali, amma mazauna yankin na zargin yiwuwar kamuwa da guba ko shakar gurbatacciyar iska daga wani injin janareta da suke amfani da shi.
Rundunar ’Yan Sandan jihar ta bakin Kakakinta, ASP Nahum Daso ta ce tuni an fara bincike don gano ainihin musabbabin mutuwar mutanen.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno
Wata Kotun Soji ta yanke wa wasu sojoji uku hukuncin ɗaurin rai da rai kan sayar da makamai da harsasai ba bisa ka’ida ba a Maiduguri, Jihar Borno.
Kotun sojin ƙarƙashin jagorancin Birgediya-Janar Mohammed Abdullahi, ta bayyana cewa an yanke wa mutum uku daga cikin sojojin huɗu hukuncin ɗaurin rai da rai yayin da aka ɗaure mutum ɗaya shekaru 15 a gidan yari.
Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa Yarima Salman ya jagoranci jana’izar babban mai ba da fatawa na SaudiyyaSojojin da abin ya shafa sun haɗa da Raphael Ameh da Ejiga Musa masu muƙamin sajan, da kuma Patrick Ocheje mai muƙamin kofura.
Binciken kotun ya nuna cewa Ameh ya karɓi sama da ₦500,000 daga harƙallar sayar da harsasai kafin daga bisani a kama shi yana ƙoƙarin sayar da wasu ƙarin makaman.
Da yake yanke hukunci, Janar Abdullahi ya bayyana su a matsayin “ƙwayaye bara-gurbi” da suka ci amanar rundunar soji, suka karya ƙa’idar ladabi da biyayya, tare da wulaƙanta mutuncin da ake tsammani daga jami’an soja a yaƙin da ake yi da ta’addanci.
Bayanai sun ce wannan hukuncin na zuwa ne bayan amincewar su kan aikata laifuffukan da suka haɗa da “sata da cinikin makamai ba bisa ka’ida ba, da taimaka wa maƙiya” wanda duka laifuka ne ƙarƙashin dokar sojojin Najeriya.
Kotun ta bayyana cewa “irin wannan safarar da ba bisa ƙa’ida ba na zama haɗari ga sojoji da ayyukansu, da kuma tsaron ƙasa, don haka yana nufin taimaka wa maƙiyan ƙasar.”
Shugaban Kotun, Brigadier Janar Abdullahi, ya ce waɗannan laifuka da sojojin suka aikata ba matsala ce kawai ta karya doka ba, har ma da cin amana, da martabar da ake sa ran sojoji su riƙe.
Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta lamunci irin waɗannan rashin ɗa’a da halayen damfara ko rashin ƙwarewa ba.
Babu shakka Jihar Borno ce cibiyar rikicin Boko Haram a Najeriya wadda ta kwashe kimanin shekara 15 tana fama da shi, lamarin da ya laƙume rayukan dubban mutane da haifar da matsalar jin-ƙai.