An kashe manomi da dabbobi 39 a Bauchi
Published: 9th, August 2025 GMT
Wani rikici da ya ɓarke ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai suna Irmiya Yohanna, mai shekara 40, tare da hallaka shanu da tumaki 39, a ƙauyen Kaduna da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, a Jihar Bauchi.
Haka kuma ’yan sanda sun ceto shanu 249 da aka yi ƙoƙarin kashewa.
Obi ya ziyarci Bauchi, ya ba da tallafin N15m don inganta ilimi PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa, a ranar 7 ga watan Agusta 2025, Irmiya ya tafi gonarsa amma bai dawo gida ba.
Bayan yin bincike, aka gano gawarsa a kwance a gonarsa.
Bayan samun rahoto daga Sarkin ƙauyen, Emmanuel Bulus, ’yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO SP Fitoka Golda sun wajen domin yin bincike.
Sun ɗauki gawar zuwa Babban Asibitin Bogoro, inda likita ya tabbatar da mutuwarsa.
Bincike, ya nuna cewa wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kashe shi.
Daga baya, wasu fusatattu a yankin suka kai wa dabbobin Fulani hari a kusa da ƙauyen, inda suka kashe shanu 20 da tumaki 19, sannan suka jikkata wasu.
Sai dai rundunar ta kama wani mutum mai suna Ahmadu Mairiga da ake zargi da hannu a kisan.
Rahoton ’yan sanda ya ce rikicin ya fara ne lokacin da Irmiya ya tarar da shanu suna cin amfanin gonarsa.
Ya nemi makiyayan su fitar da su, sai faɗa ta kaure a tsakaninsu wanda hakan ya kai ga mutuwarsa.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya kai ziyara yankin, inda ya gana da shugabannin Fulani, sarakuna da shugabannin al’umma.
Ya gargaɗi mazauna yankin da su guji tashin hankali tare da tabbatar da cewa za su ɗauki matakan tsaro don kawo zaman lafiya.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
“Lamarin daya kai miliyan daya na wadanda suka nemi a basu bashin karatu, lalle abin ya nuna a gaskiya matasa sun son su kyautata yadda rayuwarsu data wasu zata kasance a gaba, musamman ma yadda suka maida hankali wajen neman ilimi.
Ya ci gaba da bayanin “Wannan yana nunawa a fili yadda jagorancin na Shugaban kasa Bola Tinubu ya damu da lamarin ilimi domin shi ne ginshikin ci gaban al’umma kamar yadda ya ce,”.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA