Kauyuka 30 Sun Yi Zanga-zanga Kan Ta’addancin ‘Yan Bindiga A Zamfara
Published: 8th, August 2025 GMT
Mazauna kauyuka akalla 30 daga Dan-Isa da Kagara dake karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara, sun mamaye gidan gwamnati dake Gusau babban birnin jihar domin nuna takaicinsu kan yadda rashin tsaro a yankin na su “yaki ci yaki cinyewa” a ranar Alhamis. Masu zanga-zangar da suka hada da mata da kananan yara suna dauke da alluna dauke da rubuce-rubuce kamar: “Muna bukatar zaman lafiya a kauyukan Kaura-Namoda,” “Gwamna Dauda Lawal da Matawalle ku kawo mana dauki”, “Ana kashe mu kowace rana,” da dai sauransu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140
“Wannan babban shiri ne da zai sake fasalin Zamfara, ya tabbatar da ci gaba mai ɗorewa tare da inganta rayuwar al’umma,” inji shi.
Ya ƙara da cewa, a mafi yawan ƙananan hukumomin jihar ana gina sabbin hanyoyi na kilomita biyar a cikin birane, baya ga Gusau wadda ake gudanar da manyan ayyuka na musamman. Ya ce hakan zai rage cunkoso, ya haɗa al’umma, ya kuma farfaɗo da kasuwancin ƙauye da birane.
A fannin lafiya, gwamnati ta ƙaddamar da gina sabon babban asibiti a Nasarawa Burkullu a ƙaramar hukumar Bukkuyum, tare da sabunta cibiyoyin kiwon lafiya da dama a yankunan karkara, domin sauƙaƙa samun ingantaccen magani.
An kuma sanar da ci gaba da gyaran makarantu a dukkan ƙananan hukumomi, tare da samar da kujeru, littattafai, kayan koyo da horar da malamai domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yaran jihar.
Haka kuma, ana gina sabuwar kasuwa ta zamani a Nasarawa Burkullu, da ake sa ran za ta zama cibiyar bunƙasa sana’o’i da kasuwanci ga mazauna yankin. A bangaren ruwa da wutar lantarki kuwa, ana tono ruwan sha da kuma shimfiɗa sabbin hanyoyin rarraba wuta zuwa asibitoci, makarantun firamare da sakandare, da cibiyoyin gwamnati.
Dantawasa ya ce, an riga an kammala wasu daga ayyukan tare da ƙaddamar da su, yayin da sauran ke kan gaba, abin da ya tabbatar da cewa gwamnatin Lawal “ba ta tsaya kan magana kawai ba, tana aiki tare da sakamako a fili wanda jama’a ke iya gani da idonsu.”
“Wannan gwamnati ta tsayu kan gaskiya, amana, da samar da kyakkyawan sakamako ga al’umma. Ayyukan da ake gani su ne shaida,” inji Kwamishinan.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA