Fafaroma Leon na 14 : Ina matukar bakin cikin abinda  ke faruwa a Gaza

Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza,

Sabon shugaban darikar ‘yan katolika na duniya Fafaroma Leo na 14 ya ce yana matukar bakin ciki da abin da ke faruwa a zirin Gaza, inda ya bukaci a tsagaita wuta nan da nan, a ba da agajin jin kai ga fararen hula da suka gaji, kuma a sako duk wadanda aka yi garkuwa da su.”

Fafaroman ya kuma yi kira ga “manyan kasashen duniya” da su dakatar da yaki, ya kuma yi kira da a samar da zaman lafiya “adalci” mai “dorewa” a Ukraine a wani jawabi da ya gabatar yau Lahadi a sallarsa ta farko bayan zama fafaroma.

Shugaban ‘yan katolika na duniya ya kuma yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma tsakanin Indiya da Pakistan, amma ya yi kira da a samar da maslaha mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments