Aminiya:
2025-08-09@17:56:38 GMT

Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi

Published: 9th, August 2025 GMT

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da suka rasu.

Wannan biyan zai shafi tsoffin ma’aikatan jihar, ma’aikatan wucin-gadi, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da malaman firamare.

Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara 

Ana sa ran biyan kuɗin zai fara daga kan watan Disamba 2024 zuwa Maris ɗin 2025.

Gwamna Idri, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar ma’aikata da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima.

Ya ce biyan haƙƙoƙin ma’aikata ba wasa ba ne, kuma gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen ganin an biya su a kan lokaci.

Wasu tsoffin ma’aikata sun yaba da wannan mataki, amma sun roƙi gwamnan da ya ci gaba da biyan sauran waɗanda ba su shiga jerin wannan sahun ba.

Sun ce akwai ɗimbin masu jiran haƙƙinsu, kuma idan ana biyan kowa a hankali, cikin lokaci kaɗan za a rage yawan masu jiran kuɗi.

Sun kuma buƙaci gwamnati ta duba tsarin fansho na jihar don inganta shi.

A cewarsu, yawancin masu karɓar fansho a Kebbi na cikin halin ƙunci saboda kuɗin da ake ba su ba ya wadatarwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Garatitu gwamnati Walwala

এছাড়াও পড়ুন:

Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano

“Ko da yake lamarin ya faru ne a wajen harabar jami’a, Hukumar Gudanarwa ta jami’ar na cikin jimami matuƙa da wannan mummunan lamari, kuma tana miƙa ta’aziyyarta ga iyalan marigayin, abokansa da sauran ɗalibai,” in ji sanarwar.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya bayyana cewa jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin a kama waɗanda suka aikata wannan laifi.

An binne marigayin a garinsu da ke Zariya a Jihar Kaduna.

Jami’ar ta buƙaci ɗalibai su kwantar da hankalinsu tare da kasancewa masu lura da abin da ke faruwa a tare da su.

Haka kuma ta roƙi jama’a da su taimaka wa jami’an tsaro da duk wani bayani da zai iya taimakawa wajen gudanar da bincike.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za a biya ma’aikata 445 garatitun sama da biliyan ɗaya a Kebbi
  • Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara 
  • Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja
  • Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu
  • Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
  • An kama bama-baman da aka boye a cikin kayan gwangwan a Kaduna
  • Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano
  • Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC
  • Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama