Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga
Published: 8th, August 2025 GMT
Daruruwan mazauna kauyen Jimrawa da ke karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zangar lumana a Gusau babban birnin jihar kan matsalar tsaron da ta addabe su.
Hakan na zuwa ne mako biyu bayan mazauna Gusau din su ma sun yi irin wannan zanga-zangar kan cewa ’yan bindiga sun kashe sama da mutum 100 a kauyukan jihar.
Kauyukan da aka kashe mutanen sun hada da Mada, Ruwan Bore, Fegin Baza, Lilo da kuma Bangi.
NAJERIYA A YAU: Shekara nawa shugabanni ke bukata don cika alkawuran zabe? Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a KanoKauran Namoda da sauran kananan hukumomin jihar dai sun jima suna fama da hare-haren ’yan ta’adda, lamarin da ya yi sanadin kisan mutane da dama da kuma lalata kauyuka masu yawa.
Mazauna yankunan dai sun ce rashin kyawun hanyoyin jihar na taimaka wa matsalar tsaron saboda jami’an tsaro na shan bakar wahala wajen kai musu dauki.
Masu zanga-zangar dai sun yi wa gidan gwamnatin jihar da ke Gusau kawanya suna neman a kai wa kauyen nasu agajin gaggawa.
Kauyen na Jimrawa dai na cikin gundumomi guda shida da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta tsara gudanar da zaben cike gurbi ranar 16 ga watan 16 mai zuwa.
Da take jawabi a yayin zanga-zangar, daya daga cikin matan mai suna Maimuna Adamu, ta ce wasu daga cikin mazajensu yanzu haka suna hannun ’yan bindiga, dalilin da ya sa suka fito kwansu da kwarkwata don nuna bacin ransu.
“Mun zabi Dauda Lawal a matsayin Gwamna, amma tun da ya hau mulki a 2023 ya gaza cika mana alkawarin da ya dauka na inganta tsaro,” in ji ta.
Shi ma wani daga masu zanga-zangar mai suna Auwalu Umar, ya ce, “Sun kasha mahaifina da mahaifiyata da ’yan uwana maza da mata. Yanzu ni kadai nake rayuwa ba ni da mataimaki ko mashawarci.”
Shi ma wani dattijo da ya ki bayyana sunansa ya ce, “Ba za mu koma gid aba har sai mun samu tabbacin tsaro. ’Yan siyasa kawai kuri’armu suka damu da it aba rayuwarmu ba.”
Aminiya ta rawaito cewa ko a ranar Talata maharan sun sace sama da mutum 150 a wasu jerin hare-hare da suka kai kan kauyukan jihar daban-daban cikin kwana hudu kacal.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Zamfara zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.
KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.
Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.
Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.
Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.
Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp