Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyar Kasar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba
Published: 7th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Amurkawa sun yi kuskure idan suna tunanin cewa hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai canza matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Dole ne a fara wani sabon mataki na dangantaka tsakanin Iran da hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA saboda gaba daya sabbin al’amura sun bullo.
Ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana cewa, Amurkawa sun yi kuskure idan har suna tunanin kai hari kan cibiyoyin makamashin nukiliya zai sauya matsayin Iran ko kuma ya sa ta ja da baya.
A cikin shirin “Tehran, Iran, duniya” da aka watsa a tashar talabijin ta Tehran a yammacin jiya Laraba, yayin da yake amsa tambaya kan sabuwar hanyar tunkarar hukumar ta IAEA, Araqchi ya bayyana cewa: Majalisar shawarar Musulunci ta zartas da wata doka mai matukar muhimmanci, inda ta mai da hadin gwiwar Jamhuriyar Musulunci ta Iran da hukumar zuwa hukunce-hukuncen kwamitin koli na tsaron kasar, wanda hakan na nufin duk wani hadin gwiwa da hukumar daga yanzu dole ne a gudanar da shi ta hanyar majalisar koli ta tsaron kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya August 7, 2025 Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci Na Iran Sun Jaddada Shirinsu Na Tunkarar Duk Wata Barazana August 7, 2025 Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa August 7, 2025 Human Rights Watch Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Rusa Makarantu Fiye Da 500 A Gaza August 7, 2025 Amurka Ta Kwace Dalar Amurka Miliyon $584 Na Jami’ar California Saboda Gaza August 7, 2025 Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya August 7, 2025 Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya August 7, 2025 Kasar Masar Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka August 7, 2025 Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba August 7, 2025 Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: makamashin nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware
Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi maraba da amincewar da kasashen Birtaniya, Australia, da Canada suka yi wa kasar Falasdinu, tana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da hakkin al’ummar Palasdinu na kasarsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar jiya Lahadi, kungiyar ta yi kira ga kasashen duniya da MDD da su mayar da Isra’ila saniyar ware tare da dakatar da duk wani nau’i na hadin gwiwa da ita.
Hamas ta yaba da wannan amincewa da ita a matsayin wani muhimmin mataki na tabbatar da ikirarin da al’ummar Falastinu ke yi na neman kare filayensu da wuraren ibadarsu masu tsarki, tare da fatan samun kasa mai cin gashin kanta wacce take da Quds a mastayin babban birni.
Har ila yau kungiyar ta yi kira da a kara daukar matakan ladabtarwa kan Isra’ila tare da hukunta shugabanninta kan laifukan cin zarafin bil’adama.
Sanarwar ta soki gwamnatin Isra’ila kan yadda take ci gaba da yin watsi da dokokin kasa da kasa da kuma ka’idojin jin kai, tare da bayyana “mummunan cin zarafi” da ake yi wa Falasdinawa.
An fitar da wannan sanarwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da takun sakar diflomasiyya tsakanin kasashen dake amincewa da Falasdinu a matsayin kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci