Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
Published: 12th, August 2025 GMT
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) ta yi wa tsohon gwamnan Jihar Sokoto, Sanata Aminu Tambuwal, tambayoyi kan zargin fitar da wasu kuɗi har Naira biliyan ₦189 ta hanyar cire kuɗin daga banki.
Rahotanni sun nuna cewa, Tambuwal ya isa shalƙwatar EFCC a Abuja da misalin karfe 11:30 na safiyar yau Litinin, inda yake ci gaba da fuskantar tambayoyi daga jami’an bincike kan zargin.
Majiyoyi daga EFCC sun tabbatar da cewa an tsare shi ne kan zargin fitar da kuɗi a bainar jama’a wanda ke saɓawa dokar hana safarar kudi masu nauyi ta shekarar 2022. An ce, “Mun ware dukkan zarge-zargen da suka shafi Tambuwal, saura ya bayar da bayani.”
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya ƙi yin bayani kan lamarin lokacin da aka tuntuɓe shi. Ana sa ran tsohon gwamnan zai bayar da amsa kan yadda aka samu irin waɗannan manyan fitar kuɗi a lokacin mulkinsa a Jihar Sokoto.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tambuwal
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar Cif Audu Ogbe tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh.
Ya kuma yi wa iyalansa, abokansa da dukkanin ’yan uwansa ta’aziyya kan rashin da suka yi.
Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasuCif Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya hidimta wa Najeriya a ɓangarori daban-daban ciki har da Ministan Sadarwa a lokacin Jamhuriya ta Biyu.
Sannan daga baya ya zama Ministan Noma a Gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari.
A cewar sanarwar Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Ogbeh mutum ne mai basira da zurfin tunani wanda ya taimaka wajen tsara manufofin gwamnati da magance manyan matsalolin ƙasa.
Ogbeh, ya fara harkar siyasa a shekarun 1970 a matsayin ɗan majalisa, sannan daga baya ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar APC.
Shugaba Tinubu, ya bayyana shi a matsayin “Ɗan ƙasa wanda hikimarsa, jajircewarsa, da ƙoƙarinsa na ci gaba suka bar tarihi a siyasar Najeriya.
“Kullum yana da hujjoji da alkaluma don kare ra’ayinsa. Ƙasa za ta yi matuƙar kewar gogewarsa.”
Shugaban ya yi addu’ar Allah Ya jiƙansa ya kuma bai wa iyalansa haƙuri da juriya.