‘Yan Sandan Nasarawa Sun Kama Mutum Shida Da Laifin Fashi Da Makami Da Garkuwa Da Mutane
Published: 11th, August 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa ta cafke wasu mutane shida da ake zargin ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane ne a karamar hukumar Doma da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Ramhan Nansel ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a lafiya, ya ce jami’an sun kuma kama wani makiyayi dauke da makamai a karamar hukumar Keana ta jihar.
Sanarwar ta ce, jami’an sashin Doma da ke aiki da sahihan bayanan sirri daga wani dan kasa mai kishin kasa, karkashin jagorancin jami’in ‘yan sandan shiyya, sun kai samame a wata maboyar ‘yan ta’adda da ke Yelwa Ediya inda aka kama wadanda ake zargin.
Ya ce a yayin da ake yi musu tambayoyi, wadanda ake zargin sun amsa laifin yin garkuwa da wani kansila mai ci inda suka sace wayoyin hannunsa guda biyu.
Sun kuma amince da cewa sun tare hanyar Doma zuwa Yelwa ne inda suka kai hari kan wani Ibrahim Haruna Yelwa Ediya tare da kwace babur dinsa kirar Bajaj wanda kudinsa ya kai ₦970,000 yayin da ake sayar da babur din da suka sace.
SP Ramhan Nansel ya bayyana cewa, a yayin aikin jami’an sun kwato kudi ₦100,000 – kudaden da aka siyar da babur din da aka binne a daji, tare da babur Bajaj daya.
A wani labarin makamancin haka, jami’an sashin Keana sun amsa kiran da suka yi na cewa makiyayan da ke kiwo a filayen gonaki a Gidan Zaki Hassan da ke karamar hukumar Kuduku a karamar hukumar Keana, yayin da makiyayan suka yi ta harbe-harbe kafin su gudu.
‘Yan sandan da ke aiki da jama’ar gari sun kama wani makiyayi mai shekaru 20, sannan sun kwato bindiga samfurin AK-47 guda daya dauke da harsashi guda shida.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Shattima Jauro Mohammed, ya bayar da umarnin mika duk wadanda ake tuhuma zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar domin gudanar da bincike mai zurfi tare da gurfanar da su gaban kuliya.
CP Mohammed ya jaddada kudirin rundunar na tabbatar da zaman lafiya ga kowa da kowa, yana mai gargadin cewa ba za a samu mafaka ga masu aikata laifuka ba.
Ya bukaci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda kuma su ci gaba da bayar da bayanai masu inganci a kan lokaci don taimakawa ayyukan ‘yan sanda.
Rel/Aliyu Muraki/Lafia.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Lafiya karamar hukumar
এছাড়াও পড়ুন:
An ceto ’yan mata 24 d aka yi garkuwa da su a makaranta a Kebbi
An ceto ’yan matan nan 24 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Makarantar sakandaren Gwamnati ta GGCSS da ke yankin Maga da ke Jihar Kebbi.
Gwamnan jihar Kebbi Nasiru Idiris a taron manema labarai a ranar Talata fadar gwamnatin jihar ya tabbatar da an karɓo ɗalibban da aka sace a farkon makon nan.
Ya ce “an karɓo ɗiyanmu ’yan makaranta waɗanda aka yi garkuwa da su a Maga. Shugaban ƙasa ya baiwa jami’an tsaro umarni a tafi a gano inda yaran suke kuma a karɓo su muna tabbatar wa uwayen yara da al’ummar Kebbi yara sun dawo.
“Muna godiya ga shugaban ƙasa da jami’an tsaro musamman sojoji da ’yan sanda da Sibil difens da sauransu da suka tsaya aka karɓo yaran nan cikin ƙoshin lafiya.
“Mu gwamnatin Kebbi ba mu biya kuɗin fansa don a saki yaran ba, a binciken da muka yi ba wanda ya biya kuɗin fansar yaran, mu ba mu ba da ko kwabo ba,” a cewar Gwamnan Idiris.