2025-08-10@23:18:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6311

«wani abu ne»:

    “Na taɓa zama abar kwatance, musamman a ɓangaren da shafi kuɗi, suna, girmamawa, amma kuskuren da na yi ya zama dalilin da yasa masana’antar ta juya min baya, sakamakon babu abin da na iya ko na sani face; harkar ta fim. Halin da ake ciki yanzu, babu wani tallafi, babu aikin yi, akwai lokacin da ina da ɗimbin masoya da suke son aurena da kuma nuna min soyayya, amma sai na kasa zaɓen wanda zan ci gaba da rayuwata da shi a wancan lokaci. Babban dalilin da ya jawo min koma-baya a harkar fim shi ne, hatsarin da na samu na mota, wanda Allah ya jarrabce ni da shi, na yi hatsarin mota da har sai da na samu karaya...
    Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali, sun ce sun kama wasu sojoji kusan 30 da ake zargin suna shirin kifar da gwamnati ƙasar. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti da ke tsakiyar ƙasar. Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba game da lamarin. Ita ma gwamnatin da ke mulki yanzu ta karɓi mulki ne ta hanyar juyin mulki a shekarar 2021. Wannan zargi ya ƙara nuna cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tsakanin gwamnatin sojin. Yanzu haka dai gwamnatin na fuskantar matsalar hare-haren masu...
    Sunana Comr, Nr. Ibrahim Lawan Stk Lokaci wani abu ne da yake nuna yanayi a kodayaushe, sannan yake bada damar aiwatar da abubuwa masu kyau da mararsa kyau a rayuwa. Haka kuma yanayi ne da yake bada damar rayuwa a cikin daƙiƙu, mintuna, da kuma, awowi, ranaku, makonni dakuma shekaru. Ana amfani da lokaci ne ta hanyar da ya kamata kamar gudanar da rayuwa maikyau da zamantakewar yau da gobe, da kuma hanyoyin da ya dace na gudanar da rayuwa. Lokaci na yana da matuƙar muhimmanci wajen gudanar da rayuwa. Amfanin lokaci na nufin amfani da lokaci ko kuma yadda ake amfani da shi wajen cimma burin mutum ko gudanar da ayyuka. Ga wasu daga cikin amfanin lokaci; inganta...
    Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan yankunan na kasar Siriya shi ya sa bata son ganin an sami zaman lafiya a kasar ta Syriya gaba daya, har zuwa lokacinda zata mamaye yankin. Gwamnatin kasar Siriya mai ci ta tabbatar da cewa samuwar sojojin HKI a duk lokacinda suka ga dama a wadannan yankuna alamace ta rashin zaman lafiya a kasar. Kowa ya san cewa HKI ba zata taba barin kasar Siriya...
    Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bada sanarwan cewa alkalan wasan kwallon kafa ta mata kuma ta Salon guda biyu ne ta zama a kasar Iran don alkalanci a gasar FIFA ta kwallon Saloon ta masa na wannan shekara ta 2025, wanda za’a gudanar a kasar Philipine. Zaben Zari Fathi da kuma Gelareh Nazemi a matsayin alkalai a wannan gasar mai muhimmanci ya nuna irin matsayinda Iran take da shi a hukumar ta FIFA. A ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa ne, zuwa 2 ga watan Decemban shekara ta 2025 ne za’a gudanar da gasar kwallon salon ta mata da kuma duniya a biranen Manila da Negros,na kasar Philipine. Inda kungiyoyin kwallon kafa ta mata 16 daga kasashen...
    Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi. Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas  Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
    Hukumar Shari’a ta Jihar Borno ta ƙara wa ma’aikatanta 97 girma bayan wani taro na kwanaki huɗu da ta gudanar a Maiduguri. Muƙaddashin sakataren hukumar, Saleh Khala Jidda ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa ma’aikatan sun samu ƙarin girma ne saboda ƙwazonsu. EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato Waɗanda abin ya shafa sun hada da Majistare 10 daga matakin Majistare mataki na ɗaya zuwa Babban Majistare mataki na biyu. Sai Majistare daga matakin farko zuwa Babban Majistare na biyu. Sauran sun haɗa manyan Magatakarda daga mataki na ɗaya zuwa na biyu. Sai dai a gefe guda, hukumar ta ɗauki mataki kan wani alƙalin Babban Kotun Majistare...
    Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin haramtattun ayyuka, inda suka mayar da su gidajen karuwai. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke maƙwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matuƙar haɗari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan Jihar a Legas. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    Ya bayyana cewa, gwamnatin da ta gabata ce ta rufe cibiyoyin da aka kafa a gwamnatin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, amma gwamnatinsa ta yanke shawarar farfado da su domin magance matsalar rashin aikin yi. “Don haka ne a yau, kowane Dalibi wanda ya kammala karatun, ba kawai takardar shaida za a bashi ba har ma da kayan aikin sana’ar da ya koya” in ji Yusuf. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
    An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin. An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr Aminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato. Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka...
    Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas. NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi...
    Wata kotu a N’Djamena, babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon firaminista kuma madugun adawa, Succes Masra, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito kotun ta samu tsohon firaministan da laifin kalaman ƙiyayya, nuna wariyar ƙabilanci da kuma tayar da tarzomar da ta rikiɗe zuwa kisan kiyashi. Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Kotun a ranar Asabar ta ce ta sami Mista Masra da laifi kan rawar da ya taka wajen tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga Mayu — waɗanda galibi mata da yara ne a yankin Mandakao da ke kudu maso...
    A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League. Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi. MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara. Kafin haka,...
    Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali.   Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE suna neman sani “ko a sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 2(1) (t) na dokar NBC, NBC na da hakkin kare ‘yancin Badeggi FM da gwamnan Neja ya rufe.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a hare-haren Isra’ila lokacin da yake jiran karɓan kayan tallafi a kudancin Gaza. “Ko za ku faɗa mana ta yaya ya mutu sannan a ina,” kamar yadda Salah ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar. Obeid wanda ɗan wasan gaba ne, ya zura kwallaye sama da 100 a tsawon rayuwarsa ta tamaula.
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza. Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi. Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka. DW ya ruwaito cewa, dukkan...
    Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar.   A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin wani mai hatsarin gaske kuma dilan kwyaan maye, Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar kwamitin da ya gabatar a gaban...
    Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi manoma da mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya cikin gaggawa domin ceto jarin da suke zubawa.   A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar noma da raya karkara, Ashaolu Omotola ya fitar, ya ce. Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kwara tsakanin ranakun 7 zuwa 21 ga watan Agustan bana.   A cewar hukumar ta gano al’ummomi da dama a jihar daga cikin wurare 832 a fadin kasar da ke fuskantar hadarin ambaliya a wannan lokaci.   Ta ce ambaliyar ruwan da ake sa ran za ta iya tarwatsa hanyoyin sufuri tare da yin barazana ga filayen noma,...
    Ya ƙara da cewa an kama aƙalla mutane uku da ake zargin suna da alaƙa da kayan a wani samame da aka kai musu. Babafemi ya ce, “Kashi na farko na kayan, wanda ya kunshi kwayoyin Tramadol 57,420 na tramadol 225mg da 57 na hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.60, an kama su ne a cikin wani kaya da zai je kasar Gabon a Air Cote d’Iɓoire a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli, 2025. Wani shahararren dan kasuwan nan mai suna Benkwee Ihesi Osina, shi ne wakilin cargo, wanda aka kama. Shipment, an kama shi nan take, wani bincike ya kai ga kama wani wanda ake zargi, Uzochukwu Godspower Chukwurah, a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuli. “An gano...
    Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Tel Aviv na Isra’ila ranar Asabar, domin yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin Isra’ila ta lashi takobin faɗaɗa rikicin tare da ƙwace birnin Gaza. Masu zanga-zangar da ke riƙe da hotunan waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a yankin Falasdinawa sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da sakin su ’yan uwansu. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki ’Yan jaridar AFP a wajen gangamin sun ƙiyasta adadin waɗanda suka halarci taron a matsayin dubbai, yayin da wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta ce mutane kusan 100,000 ne suka...
    Garima wanda har ila yau shi ne, and Jakadan Gwandu ya yi nuni da cewa, cibiyoyin na CNG da gwamnatin taraya ta samar a jihohin Kano da Kaduna, za su taimaka wajen samar da Iskar Gas ɗin a Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta Gabas. Kazalika ya ce, samar da cibiyar a jihar Sokoto wadda take kusa da Jamhuriyyar Nijar, hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar Garima ya sanar da cewa, Iskar Gas ɗin ta CNG tsafatattaciya ce kuma bata da wani tsada, inda kuma ta rage gurɓatar muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Kungiyar Al Hilal ta Saudiyya ta dauki dan wasan gaban Liverpool, Darwin Nunez, kamar yadda kungiyoyin biyu suka tabbatar ranar Asabar. Masu ruwa da tsaki a harkar tamaula na ganin wannan matakin za bai wa zakarun Premier League damar sake mika tayin neman dan wasan gaban Newcastle, Alexander Isak. ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno Shekaru uku da suka gabata ne Nunez ya koma Liverpool daga Benfica kan farashin Yuro miliyan 75 ($87m, £65m), sai dai bai iya cika tsammanin da aka yi wa darajar da aka saye shi ba. Nunez wanda dan kasar Uruguay ne ya zura kwallaye 40 a wasanni 143 da ya haska a Liverpool, amma daga baya...
    Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da kuma zafi, wanda hakan na iya shafar Ƙwan da za su yi kai tsaye. 3- Abinci Mai Gina Jiki: Ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda ke ɗauke da sinadaran ‘protein, amino acids’, waɗanda za su sanya su yi nauyi tare kuma da buƙatar a riƙa yi musu allurar ƙara musu lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba,  sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu. Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran ta dage kan cewa batun biyan diyya a kan barnar da aka yi mata a yakin baya-bayan nan ya zama wani muhimmin bangare na duk wata tattaunawa a  nan gaba.” A ranar  Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta duk wata Magana kan wani takamaiman lokaci ko wurin da za a yi shawarwari da Washington, yana mai jaddada cewa “dukkan jita-jita game da hakan...
    Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
    Hukumomin tsaro a kasar Venezuela sun kama wasu tarin bama-bamai a gabashin birnin Maturin na jihar Monagas, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin yunkurin da wasu bangarori masu tsatsauran ra’ayi suka yi na kai hare-haren ta’addanci da nufin kawo cikas ga gwamnatin shugaba Nicolas Maduro. Ministan harkokin cikin gida, Diosdado Cabello, ya sanar a jiya Asabar cewa, jami’an tsaro, bayan gudanar da ayyukan leken asiri, sun gano wasu kayyayakin fashewa da abubuwan harhada bama-bamai da aka boye a wasu shaguna biyu.Kayan sun dai sun  hada da akwatuna 1,137 da ke dauke da wasu nauyin bama-bamai da ba a taba ganin irinsu a kasar ba, da  rokoki 35, da igiyoyin tayar ta bama-bamai da ababen fashewa,  na’urorin kashe...
    Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7. Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen abinci a ƙasar. Shi kuwa a nasa jawabin a wajen ƙaddamarwar, Gwamnan Jihar Biniwai, Hyacinth Iormem Alia, ya jaddada muhimmancin da za a amfana da shi a tsarin. “Dabarun faɗaɗa noman Waken Soya na ƙasa, mataki ne da ya dace wajen yin haɗaka, domin samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar a duk shekara da suka kai kimanin Naira tiriliyan 3.9 da ƙara ƙirƙiro da ayyukan...
    Yayin ziyararsa a kasar Indiya kwanan nan, shugaban kasar Philippines ya bayyana cewa, idan Sin da Amurka suka yi taho-mu-gama kan batun yankin Taiwan, Philippines ba za ta iya killace kanta daga ciki ba. Irin wannan furucin nasa yana da ban mamaki, wanda ya saba da alkawarin da Philippines ta yi na tsayawa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, zai kara illata dangantakarta da kasar Sin, da zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya. Rura wutar rikici kan yankin Taiwan, yunkuri ne da Philippines ta yi na dogaro kan Amurka tare da ba ta hadin-kai, don hana ci gaban kasar Sin. Amma batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma...
    Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya (ASUU), ta yi gargaɗi cewa za ta iya sake tsunduma yajin aiki saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗauka. Shugaban ƙungiyar, Christopher Piwuna, ya ce gwamnati ba ta kula da walwalar malamai, ba ta samar da kuɗaɗen gudanar da jami’o’i yadda ya kamata, kuma ba ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma ba. Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Wannan na zuwa ne bayan Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ya bayyana cewa “Babu wata jami’a ko malaman ASUU da za su sake shiga yajin aiki” idan aka ci gaba da tattaunawa da kuma cika buƙatun malaman. Sai dai ASUU ta ce hanyar da za...
    Mambobin haɗakar jam’iyar sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, da sauran manyan mutane da dama. A cikin wannan tsarin, haɗakar jam’iyyar ta naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban da sakatare na riƙon ƙwarya. Tun daga wannan lokaci, jam’iyyar tana ta karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyun adawa da kuma gudanar da tarurruka domin ƙara masun mambobi a faɗin ƙasar nan kafin zaɓen 2027. El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin asalin mambobin APC, ya...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar.   Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.   A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon.   Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin...
    Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno. A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann. Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi. Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196. Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa shugaban yay aba da ayyukan da yan jarida a kasar suka yi a lokacin yakin kwanaki 12, na samar da hadin kai tsakanin iraniyawa duk tare da banbanci-bambance da ke tsakaninsu da kuma fadin labaran gaskiyan abinda yake faruwa ga mutanen kasar da kuma duniya gaba daya dangane da yakin. Shugaban yay aba da yadda suka nuna zanga-zangar hadin kai...
    Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
    Falasdinwa 11 suka rasa rayukansu a yau Asabar a Gaza saboda yunwa, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kasashe a Gaza tun lokacinda HKI ta hana shigowar abinci yankin zuwa 212. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza na fadar haka, sannan masana sun bayyana cewa mai yuwa wannan adadin ya wuce haka, saboda ita yunwa tana hana garkuwan jiki aiki, don haka karamin cuta tana iya kashe mutun saboda yunwa.  Sun kara da cewa akwai wasu Falasdinawa da dama a wasu wurare a cikin gaza wadanda basa da lafiya amma yunwa ta karasa su a gida ba tare da sun zo asbiti ba. Larabarin ya kara da cewa a cikin...
    Shugaban kasar Kwango democradiyya Félix Tshisekedi, a gabatar da sauye-sauye a gwamnatinsa a jiya jumma’a inda ya shigo da sabbin ministoci guda biyu daga bangaren yan adawa. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika News’ ya bayyana cewa gwamnatinn kasar kwango ta fara wannan sauye –sauyen ne tun farkon wannan shekarar kuma har yanzun akwai wasu sauye –sauyen da zai gabatar a dai-dai lokacinda ake ci gaba da tattaunawa da jam’iyyun adawa da kuma yan tawayen M23. A wannan karon dai shugaban ya shigo da sanannun yan adawa guda biyu cikin gwamnatinsa, kuma sune, Adolphe Muzito, wanda ya taba zama firay ministan kasar, ya bashi matsayi na mataimakin firay minister, kuma shi ne zai kula da kasafin kudin kasar. Sai kuma...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kara da cewa, masana’antar abinci ta Afrika na amfani da dabarun masu samar da kayayyaki na Sin, wajen samar da kayayyaki masu inganci. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma.   Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun yan siyasa na yankin da suka rasu.   Yayi bayanin cewar, za’a gina makarantun tsangayar ne a garuruwan Danzomo da Shabaru da kuma Rukutu wadanda za’a sanyawa sunan wadanda suka rasu da suka hada da marigayi Sanata Dalha Ahmad Dan Zomo da marigayi Musa Waziri Kamus da kuma marigayi Ali Ado.   Haka kuma majalisar ta amince da gyaran masallatan Juma’a na Hannun Giwa da...
    Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar duniyar wata da aka raba ma wasu hukumomin bincike 7 na kasashe 6. Kana bisa gudanar da bincike kan kasar da na’urorin binciken duniyar wata na kasar Sin, wato Chang’e-5, da Chang’e-6, suka dawo da ita, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na sauran kasashe, sun gabatar da sakamakon bincike fiye da 150. An ce, tsarin da ake bi wajen neman samun...
    Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.! Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima. An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin. Bayanai sun...
    Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga jama’a da Gwamnatin Jihar Binuwai bisa rasuwar Cif Audu Ogbe tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Cif Audu Ogbeh. Ya kuma yi wa iyalansa, abokansa da dukkanin ’yan uwansa ta’aziyya kan rashin da suka yi. Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Cif Ogbeh, ya rasu yana da shekaru 78 a duniya, ya hidimta wa Najeriya a ɓangarori daban-daban ciki har da Ministan Sadarwa a lokacin Jamhuriya ta Biyu. Sannan daga baya ya zama Ministan Noma a Gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari. A cewar sanarwar Bayo Onanuga, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labaru, Ogbeh mutum ne mai basira da zurfin...
    Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku. Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019. Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Gwamnatin...
    Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara. Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024. Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno  Ana tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba. A...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon shugaban jam’iyyar PDP kuma tsohon ministan noma daga 2015 zuwa 2019, Audu Ogbeh, ya rasu a ranar Asabar, 9 ga Agusta, yana da shekaru 78 a duniya, kamar yadda iyalinsa suka tabbatar. A cikin wata sanarwa, iyalan sun ce: “Ya rasu cikin kwanciyar hankali, ya bar mana gado na gaskiya, hidima da jajircewa ga kasa da al’umma. Mun sami kwanciyar hankali daga yadda ya shafi rayuka da kuma yadda ya kafa misali.” Ko Nawa Za A Bani Ba Zan Iya Fitowa A Matsayin Kwarto Ko Dan Daudu A Fim Ba -Dan Asabe Olala Jihar Gombe Za Ta Rungumi Shirin Farfado Da Noman Auduga Na Gwamnatin Tarayya – Inuwa Iyalan sun bayyana cewa za a sanar da yadda za a...
    Kwamandan Dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gudun da Amurka ta yi daga Yemen wani shan kaye na soji da ba a taba ganin irin sa ba Kwamandan Dakarun Quds na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani, ya kaddamar da wani kakkausar suka kan Amurka, yana mai bayyana sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na janyewa daga fagen daga a Yemen a matsayin “Halayen soja mafi wulakanci da kunya” a tarihin Amurka. A cewar wani faifan bidiyo da kafar yada labaran “Dakarun Qudus” suka wallafa a shafinsu na Telegram, Birgediya Qaani ya ce: Shugaban Amurka Donald Trump, da kansa ba wani ba—ba kawai kakakin...
    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira da a gaggauta janye shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na mamaye Gaza Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya soki shirin gwamnatin mamayar Isra’ila na kwace iko da birnin Gaza a jiya Juma’a, inda mai magana da yawunsa ya bayyana matakin a matsayin wani abu mai hadari. A nasa bangaren, Volker Turk, babban jami’in kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya, ya yi kira a jiya Juma’a da a dakatar da shirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke da nufin wanzar da cikakken ikon soji a zirin Gaza ta hanyar mamaya. A cikin wata sanarwa da ta fitar sa’o’i kadan bayan da majalisar ministocin tsaron gwamnatin mamayar Isra’ila ta amince da kudurin...
    Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki, kuma dukkansu sun jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa. A tattaunawar ta wayar tarho, Ali Akbar Welayati, mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasa, ya yi tambaya game da lafiyar tsohon Fira ministan Iraki Nouri al-Maliki. A cikin kiran, Velayati ya yi fatan samun koshin lafiya ga al-Maliki da samun sauki cikin gaggawa, inda ya...
    “Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba. Ejah ya ƙara da cewa ana sa ran kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar wakilai za su kaɗa ƙuri’ar amincewa ko kuma ƙin amincewa da gyaran. Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin ne kawai, biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, cewa a biya kason kuɗaɗen da majalisun za su samu kai tsaye a asusunsu. A cewarsa, wannan ba gyara ba ne, domin...
    Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun.   ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai. “Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba,...
    Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo. Lashen ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da sabani da suka samu da sojan. A yayin da yake kokarin warware rikicin, sai sojan mai suna Dauda Dedan, ya soka masa wuƙa. Ya ce, “Mun samu rahoton lamarin daga hedikwatar Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da tabbacin cewa za a kamo sojan da ya tsere domin...
    A ranar Juma’a da yamma, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare motar haya a mararrabar Ogbabo, kan titin Itobe-Anyigba a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da fasinjoji 9. Direban motar da wasu fasinjoji 6 kuwa sun tsere ba tare da an sace su ba. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:20 na yamma a yankin ƙaramar hukumar Ofu, lokacin da ƴan bindigar suka fito daga daji suka tare titin. Sun tilasta direban motar Toyota mai ɗauke da fasinjoji tsayawa, sannan suka yi harbi cikin iska domin tsoratar da mutane. Direban motar, Sunday Okechi, ya yi dabara ya tsere tare da wasu fasinjoji 6, yayin da sauran 9 suka faɗa hannun ƴan bindigar da suka tafi...
    Shugaban Hukumar Yaki da Cin Masu Karya Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa yawancin gidajen da aka yi watsi da su a Babban birnin Tarayya, Abuja, an gina su ne da kuɗin da ma’aikatan gwamnati suka sace. Olukoyede ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba a wani taron tattaunawa da zauren lauyoyi na Law Corridor ta shirya, mai taken “Muhimman Matsaloli da ke Addabar Harkar Gidaje a Najeriya.” Ya shaida wa mahalarta taron cewa EFCC ta kafa wata tawaga ta musamman da za ta fara binciken irin waɗannan gine-gine. “Za mu fara bibiyar dukkan gidajen, ba a Abuja kaɗai ba, har da sauran sassan Najeriya. Muna son sanin wa ke da su,” in ji Olukoyede....
    Waɗan nan sune suka keɓe makomar Nijeriya, kuma suka yi garkuwa da ita. Har ila yau, a cewar majalisar dattawa ta 9 da ta yi bincike na sayar da ƙaddarorin gwamnati, wanan ɓarnar dukiyar ƙasa ne a rana tsaka, kuma kamar yadda ɗaya daga cikinsu ya bayyana kafin ya koma cikinsu, ya ce: “PRIƁATIZATION” ba komai ba ce face “PIRATIZATION” — wato sata da rabon ganima ce a fili. Waɗannan su ne masu kuɗi na yaki haram -yaki halas ,da suka ƙwace jam’iyyu, suka wawure zaɓuka, suka yi watsi da kowa sai nasu, suka kashe baitul-mali, kuma yanzu suna neman dawowa bisa kan Karagar Mulki da sunan dimokuraɗiyya. Wannan cutar dimokuraɗiyyar Nijeriya ce da ke ƙara bazuwa, kuma yaudara ne...
    A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana. Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada da shirye-shiryen sojojin Isra’ila na mallake birnin Gaza. Shirin ya tanadi wasu ka’idoji guda biyar na kawo karshen yakin, wanda ya fara da “kwace makaman Hamas,” sannan a dawo da dukkan fursunonin wadanda ke raye ko a mace. Hakan zai biyo bayan kwance damarar zirin Gaza gaba daya, da kafa wata sabuwar gwamnatin da ba ta karkashin ikon kungiyar Hamas ko kuma hukumar Falasdinawa. Za...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon. A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa. Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi...
    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza. Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin kwace birnin Gaza tare da mamaye shi, Shugaban gwamnatin Jamus Merz ya ce Berlin na ci gaba da ba da goyon baya ga ‘yancin “Isra’ila” na kwance damarar Hamas tare da ganin an sako fursunoni, amma kuma duk da haka basu goyon bayan duk wani mataki zai kai ga kara tabarbarewar lamurra na jin kai a Gaza. “Gwamnatin Jamus ta yi imanin cewa matakin soji...
    Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda al’ummar yankin ke fuskantar barazanar wanzuwa da kuma ‘yancinsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na yau da kullun, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da na larabawa, a wani bangare na yunkurin sake fasalin yankin da kasar Lebanon. Babban abin da kungiyar tafi nuna takaicinta  akansa shi ne amincewar da gwamnatin Lebanon ta yi a baya-bayan nan da  shawarar da manzon Amurka Tom Barrack ya gabatar. Kungiyar...
    Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.   Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni. Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.   “Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.   “Wannan mu’amala mai ƙarfi tana...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus. Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, Babban Birnin Jihar. A cewar sa, tuni rukunin farko na dalibai mata su 31 suka tashi ta filin jirgin saman ikko zuwa Istanbul inda za’a dauke su zuwa kasar Cyprus don fara sabon zangon karatu. Alhaji Sa’idu Magaji wanda yake tare da daliban kafin tashin su, ya yaba da kulawar Gwamna Umar Namadi kan tallafawa daliban jihar domin ci gaba da karatun su....
    An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa. Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo. Alhaji Binyaminu Kafur ya sake tabbatar da kudirin majalisar wajen yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da kayayyaki more rayuwa, don tabbatar da ganin kowa ya  amfana da mulkin dimokuraɗiyya. Ya yi kira ga jama’a da kada su gaji wajen yin addu’a domin samun nasarar shugabanni wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu. Shi ma a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin jakadancin kasar a Philippines, sun gabatar da korafi da babbar murya dangane da kalaman da aka jiyo jagoran Philippines na yi game da batun yankin Taiwan na Sin. Kakakin wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce, yayin ziyarar da ya gudanar a kasar India, shugaban na Philippine ya shaidawa ‘yan jarida cewa, idan har yaki ya barke tsakanin Sin da Amurka, tabbas kasarsa za ta shiga, saboda kasancewarta a kewayen yankin, da ma ‘yan Philippines da dama dake zaune a Taiwan, wadanda ya zama wajibi a aiwatar da matakan mayar da su gida. Jami’in Sin ya kara da cewa kasar Sin daya ce tak...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi. Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe. Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe Bayan saukarsa ya wuce Makarantar Kiwon Lafiya da Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Malikiya da ke Bauchi. A yayin ziyarar, Obi ya gana da ɗaliban makarantar, inda ya roƙe su da su dage wajen karatu domin aikin jinya da kula da lafiya yana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa. Ya ce: “A yau, nasarar...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33. Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da...
    A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin ya sauya sheƙa zuwa ADC, ya koka kan yadda gwamnatin Kaduna ba ta kula da haƙƙoƙin ma’aikatan jihar da rashin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu da ƙalubalen rashin tsaro wanda hakan ke hana manoma zuwa gonakansu. Ya soki tsarin rabar da takin zamani na gwamnatin jihar ke gudanarwa ba tare da ta magance ƙalubalen rashin tsaro ba daga tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Tattaunawar ta biyo bayan bukatar shugaba Putin na yiwa shugaba Ramaphosa bayanin shirin zaman lafiya da Ukraine da kuma magance batutuwan da suka shafi moriyar juna.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {}...
    Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda. Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama. ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara guduws bayan yunƙurinsu na kai hari sansanin sojoji ya ci tura. Da suka hangi jiragen yaƙi na sojojin sama, sai suka fara tserewa daga maɓoyarsu, amma an kashe da yawa daga cikinsu ta hanyar ɓarin wuta. Wani mazaunin Rann ya ce da farko sun...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu An kama su lokacin da suke ƙoƙarin yaudarar wani mutum a wajen ATM na bankin Fidelity da ke Damaturu. Ana zargin matasan da amfani da wasu dabara wajen damfarar mutane ta hanyar nuna kamar suna taimaka musu, amma daga baya sai su sauya musu katin ATM. A wani...
    Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar. A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya ce...
    “Shin an taɓa yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taɓa yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taɓa yin sulhu a na karbar harajin dole, an taɓa yin sulhu ba a ajiye makamai ba?” Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su ajiye makami ba, ya ce suna da kwamandoji da makaman da sun fi a kirga. Guyawa ya bayyana cewa Malamin bai san Turji ba, bai kuma san yankinsu ba, ya ce su da suke a yankin sun tabbatar Turji bai ajiye makami ba, kuma bai yi sulhu da kowa ba. Ya ce a kwanan baya Turji ya kashe jami’an tsaro tare da ƙone motarsu, don...
    An samu mummunan iftila’i a garin Pulka na ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno, inda fashewar Gurneti ya kashe yara uku a yammacin jiya Alhamis. Yaran da suka mutu sun haɗa da Fati Dahiru, Aisha Ibrahim da Fati Yakubu. Rahoton wani masani kan yaƙi da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa, wani ɗan ƙungiyar CJTF, Buba Yaga, ya ce yaran na wasa da wani bam da ake zargin Boko Haram sun bari, kafin ya fashe da misalin ƙarfe 2:20 na rana. Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno Bayan faruwar lamarin, jami’an kunce bam (EOD) na Ƴansanda, da Sojojin Operation Haɗin Kai, da...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki daya sannan a samar wa fararen hula agaji a wajen yankunan da ake gwabza yaki.” Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 Kazalika, wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk hukuncin da majalisar tsaron kasar ta yanke zai bukaci...
    Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya, don sayarwa”, in ji Ibrahim. Kazalika, Ibrahim wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ya jaddada cewa; idan aka samu goyon bayan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma goyon bayan sauran hukumomin, hakan zai bayar da damar gyara Gandun Dazukan da ake da su, musamman wajen kare su daga kwararowar hamada. Shugaban ya ƙara da cewa, akasarin noman...
    Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Abubakar Kabir Abubakar, ya ce Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira tiriliyan daya da rabi don gina layin dogo na zamani domin saukaka harkar sufuri a cikin birnin Kano. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a Kano, inda ya ce aikin zai saukaka wa mazauna birnin wahalar da suke sha a harkar sufuri. Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano Ya ce, “Wannan aikin na gina layin dogo na zamani ya kai Dalar Amurka biliyan daya, kwatankwacin Naira tiriliyan daya da rabi. “Ga wadanda suke tafiye-tafiye zuwa kasashen waje, musamman kasashen Turai da nahiyar Asiya,...
    Idan aka dubi wannan, bai kamata a riƙa ɓata karatu ana cewa Masallaci ne za a ziyarta amma ba Annabi (SAW) ba. Ya kamata a gyara karatu, a gyara wannan fahimtar. Saboda irin wannan fahimtar ce ta haifar da a zamanin nan an samu rashin girmama Manzon Allah (SAW) har aka dasa bom kusa da shi. Ko ɗaga murya Allah ya hana a yi a gaban Annabi (SAW), to ina ga tada bom? A huɗubar sallar Idil Fiɗir da Limamin Makka ya yi a Harami, ya ce Yahudawa ne suka tada bom ɗin, amma sai ga shi da Saudiyya ta nuna wanda ya yi abin, da sunanshi da kamanninsa har da dogon gemu, ɗan ƙasar ne mai iƙirarin bin Salafiyya...
    Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da Agusta 2024 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa. Farkon kashe kuɗaɗen a ranar 14 ga Yulin 2023, lokacin da aka biya naira miliyan 846.03 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na wucin gadi. Kwanaki biyu daga bisani, an sake kashe naira miliyan 674.82. A wannan watan kaɗai, jirgin ya laƙume sama da naira biliyan 1.5. A watan Agusta, kashe kuɗaɗen sun ƙaru. An kashe...
    Nijeriya ta kasance ƙasa ce, mai girman gaske, wadda kuma ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi, Al-kamar irinsu; Al- Ƙaeda da ISIS da ke aikata ayyukan ta’addancinsu a yankin Sahel ke kutsowa cikin ƙasar, domin aikata ta’addanci. Bugu da ƙari, ba tun yau ne, wasu ƙwararru a ɓangaren tsaro na ƙasar nan, suke yin gargaɗin cewa, yadda aka bar iyakokin ƙasar sakakai ne, ke ƙara ta’azzara matsalar tsaro a ƙasa, inda wasu’yan ta’adda daga wajen ƙasar, ke yin amfani da damar, wajen shigowa tare da kuma shigo da muggan makamai da yadda masu ra’ayin riƙau na addini, daga ƙasashe kamar su, Mali da Jamhuriyar Nijar da Chadi, ke shigowa ƙasar, su kuma ci Karensu ba babbaka. Misali, ‘yan ta’addar ƙungiyar Lakurawa,...
    Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci da nufin ƙarfafa harkar yawon buɗe ido da hanzarta gudanar da shari’a a faɗin jihar. Shugaban majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ne ya sanar da amincewar majalisar  yayin zaman, ta wanda aka gudanar a harabar majalisar da ke Kaduna.   Dokar farko mai taken “Dokar Kafa Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido, Gidajen Tarihi, Shata Wurare, Lambuna da Wuraren Hutu na Jihar Kaduna, 2024”, na da nufin bunƙasa harkar yawon buɗe ido da raya al’adu a  jihar. Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Harkokin Fasaha, Shari’a da Ilimi, Magaji Suleiman, ya bayyana cewa kwamitin ya...
    Kungiyar Hizbullah da Amal na kasar Lebanon sun bayyan amincewar gwamnatin kasar Lebanon wajen kwance damarar kungiyar hizbullah wani abu ne wanda kasashen waje suka fada masu su yi haka, wanda ya yi watsi da diyaucin kasar Lebanon da kuma cikekken iko a kan kasar. Labarin ya kara da cewa shuwagabannin kasar ta Lebanon sun yi babban kuskre kuma ba zasu taba samun biyan bukata a wannan makircin a suka yiwa mutanen kasar ba. Sun bayyana cewa manufarsu itace, kawarda daga daga cikin kungiyoyi masu kare kasar Lebanon daga HKI da kuma makiyan kasar wato Daesha daga gabacin kasar. Sun ce raunta kungiyar Hizbullah zai mada kasar Lebanon mai mai saukinm mamaya. HKI ta mamaye yankuna masu yawa a kasar...
    Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari. Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin Child Nutrition Match Fund, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai. Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma...
    Kudirin gyaran dokar  fansho da sauran fa’idodi na tsaffin jami’an gwamnati ya wuce karatu na biyu a zauren Majalisar Dokokin Jihar Jigawa. Wakilin mazabar Malam Madori, Alhaji Hamza Adamu Ibrahim wanda shi ne shugaban Kwamatin kasafin kudi na majalisar, shi ne ya gabatar da wannan kudurin, ya kuma samu goyon bayan wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari. Alhaji Hamza Adamu Ibrahim ya yi bayanin cewar, daga cikin shugabanin da suka rike mukaman siyasa da ya kamata su amfana da irin wannan fansho sun hada da Gwamna da Mataimakan Gwamna da Shugaban Majalisar Dokoki da Kuma alfarmar da ya kamata su ci gaba da samu bayan sun bar mulki. Bayan Akawun majalisar, Barrister Musa Aliyu Abubakar, ya gudanar da...
    Ma’aikatar kudi ta kasar Sin, ta ce tallafin gwamnati na samar da ilimi kyauta ga daukacin daliban dake ajin karshe a makarantun share fagen shiga firamare a kasar zai amfani mutane kusan miliyan 12.   Yayin wata ganawa da manema labarai a yau Alhamis, mataimakin ministan ma’aikatar kudin kasar ta Sin Guo Tingting, ya ce karkashin wannan tallafi, iyalai da yaransu za su ci gajiyarsa za su samu ragin kashe kudaden makaranta da yawansu ya kai kusan yuan biliyan 20, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 2.8. (Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
    Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar. Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore. Mahaifin Ɗan Bello ya rasu Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano “Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ya saba wa ka’ida. Dole ne a yi tur da lamarin,” in ji Atiku. Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin shugabanci nagari da ake yi a Nijeriya. Wasu rahotanni...
    Alkaluman kididdiga na hukumar kwastam ta kasar Sin sun nuna yadda cikin watanni 7 na farkon shekarar nan ta 2025, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta kasar Sin ta kai kudin kasar yuan tiriliyan 25.7, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 3.5, wanda hakan ya nuna karuwar kashi 3.5 cikin 100 idan aka kwatanta da makamancin lokaci na shekarar bara. Daga cikin adadin, darajar mizanin fitar da kayayyaki ya kai yuan tiriliyan 15.31, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 2.1, adadin da ya karu da kashi 7.3 cikin 100, yayin da mizanin shigo da kayayyaki shi ma ya kai yuan tiriliyan 10.39, kwatankwacin dalar Amurka triliya 1.44, adadin da ya ragu da kashi 1.6 cikin 100.   A watan Yuli, jimillar darajar cinikayyar kayayyaki ta...
    Fitaccen matashin nan mai barkwanci, Bello Habib Galadanci, wanda aka fi sani da Ɗan Bello, ya yi rashin mahaifinsa a yammacin wannan Alhamis din. Matashin lauyan nan ɗan gwagwarmaya, Abba Hikima, ne ya bayyana hakan cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook. Abba ya yi alhinin hadiminsa da ’yan daba suka kashe a Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 “Innalillahi wa inna IlaiHi rajiun. Allah Ya yi wa Mahaifin Dokta Bello Galadanchi (Dan Bello) rasuwa yanzun nan. Allah Ya gafarta masa. Ameen,” a cewar saƙon da Abba Hikima ya wallafa. Kawo yanzu dai ba a bayyana dalilin rasuwar mahaifin Ɗan Bellon ba, amma wasu kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa marigayi ya...
    Wasu daga cikin tsoffin kansilolin da suka halarci tattakin sun bayyana goyon bayansu ga gwamna Abba Kabir Yusuf.   A nasa jawabin, Dahiru Yusuf daga Gezawa kuma tsohon kansila ya ce, shi ma yana cikin wadanda tsohuwar gwamnatin Ganduje ta hana hakkinsu, don haka maganar Abdullahi Abbas ba gaskiya bane! “Sun ga gwamna Abba zai jikanmu ne shi ne suke neman bata mana ruwa”.   Tun da farko, shugaban tawagar, ya tabbatar da cewa, mai girma Gwamna ya amince zai biya su hakkokinsu wanda gwamnatin baya ta kasa biyansu, kuma yace baya bukatar sakamakon komai daga gare su wai don su koma jam’iyyarsa, ya yi ne domin Allah.   A karshe dubban tsoffin kansillolin wanda suka yi tattaki dauke da...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini kan rasuwar Sadiq Gentle, wani hadiminsa kan harkokin yada labarai a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar, wanda wasu da ake zargi ’yan daba suka kai masa harin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a Facebook, ta bayyana Sadiq a matsayin jarumi, ƙwararre, kuma mai kishin kasa a fannin kafafen sada zumunta. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato Gwamna Abba ya ce mutuwar Sadiq Gentle ta girgiza shi sosai, inda ya bayyana mamacin a matsayin mutum mai kamun kai, haƙuri, da sadaukarwa ga ci gaban Jihar Kano....
    Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba.   Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana. Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma. NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti “Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula...
    Hukumar NAHCON mai kula da sha’anin aikin Hajji a Nijeriya NAHCON, ta bayyana cewa an ƙayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kujerar aikin Hajjin 2026. NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar. An kashe mutum huɗu da tayar da ƙauyuka 17 a Sakkwato ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an ƙayyade ƙafin alƙalamin kuɗin kujerar domin fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci. Hajiya Fatima ta ambato shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yana cewa an ƙayyade...
    Alummar duniya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu kan furucin firaministan Israila na fadada mamaya a Gaza. Sakamakon wani nazarin jin raayin jamaa da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar ya nuna cewa, kaso 86.6 na wadanda suka bayar da amsa sun bayyana adawa mai karfi da matakin firaministan, suna masu kira da Israila ta dakatar da bude wuta da kawo karshen rikici da Gaza nan take. Sakamakon ya kuma nuna cewa, kaso 80.8 na wadanda suka amsa na ganin cewa mafita ga rikicin Palasdinu ya dogara ne da kafuwar kasashe biyu, inda suka yi kira da a dawo da halaltattun hakkokin kasar Palasdinu. Kafar CGTN ta wallafa nazarin ne a dandalinta na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da...