Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza
Published: 9th, August 2025 GMT
Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza.
Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin kwace birnin Gaza tare da mamaye shi, Shugaban gwamnatin Jamus Merz ya ce Berlin na ci gaba da ba da goyon baya ga ‘yancin “Isra’ila” na kwance damarar Hamas tare da ganin an sako fursunoni, amma kuma duk da haka basu goyon bayan duk wani mataki zai kai ga kara tabarbarewar lamurra na jin kai a Gaza.
“Gwamnatin Jamus ta yi imanin cewa matakin soji mai tsauri da aka dauka a zirin Gaza da majalisar ministocin Isra’ila ta yanke shawara a kai a daren jiya ya kara dagula hanyoyin da za a iya cimma wadannan manufofin,” in ji Merz a cikin wata sanarwa.
“A cikin wannan yanayi, gwamnatin Jamus ba za ta amince da fitar da duk wani kayan aikin soja da za a iya amfani da shi a zirin Gaza ba.”
Matakin dai ya biyo bayan ci gaba da sukar da kasashen duniya suke yi wa yakin “Isra’ila” da aka kwashe kusan shekaru biyu tana yi kan al’ummar zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar Falasdinawa, yayin da kuma kusan dukkanin yankunan da suka zama kango.
Ministoci masu tsatsauran ra’ayi a cikin kawancen Netanyahu sun matsa kaimi wajen mamaye yankin na Gaza da karfin soji, duk kuwa da gargadin da jami’an soji suka yi cewa irin wannan mataki na iya jefa rayuwar sauran fursunonin da ake tsare da su a yankin cikin hadari.
Jamus, wacce ta dade tana kawance da “Isra’ila” wadda it ace ta biyu bayan Amurka wajen taimakon Isra’ila, ta fara nuna damuwa da irin halayen da gwamnatin Netanyahu take nunawa kan batun Gaza, wanda ya jawo mata bakin jinni da kyama a duniya baki daya.
Ko a cikin watan Yuni, majalisar dokokin Jamus ta amince da lasisin fitar da kayan soji domin taimaka ma Isra’ila, wanda kimarsu ta kai Euro miliyan 485 (dala miliyan 564).
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon August 9, 2025 Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwamnatin Jamus
এছাড়াও পড়ুন:
Fiye Da Falasdinawa 900,000 Ne Su Ka Yi Hijira A Cikin Gaza
HKI tana ci gaba da kai wa muhimman cibiyoyi da gidajen Falasdinawa a fadin Gaza.
Majiyar Falasdinawa ta ce daga safiyar yau Laraba adadin wadanda su ka yi shahadar sun kai 45 sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin ‘yan sahayoniyar su ka kai.
Har ila yau an sami wasu Karin shahidan biyar a wuraren karbar agaji dake arewacin Rafaha.
A wani labarin mai alaka da hakan shugaban hukumar lafiya ta duniya ( w.h.o) Tedross Adhanom ya ce; Kai hare-haren da ake yi a kusa da asibitin Rantisy, dake Gaza, ya yi sanadiyyar tsayuwar aikin Asibiti, domin rashin tsaro.
Har ila yau ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta kara da cewa; Jinkirin shigar da makamashi zuwa yankin yana barazanar tsayar da aikin injinan da suke bayar da wuta a asibitin idanu,wanda yake yi wa mutane da dama aiki.
Ofishin hukuma a Gaza ya sanar da cewa, mutanen da sun kai 900,000 sun fice daga gidajensu amma kuma suna ci gaba da riko da ci gaba da zamansu a cikin kasarsu.
Bugu da kari, ‘yan mamayar suna ci gaba da tilastawa mutanen na Gaza ficewa daga gidajensu, zuwa yankunan kudancin Gaza, ta hanyar kai musu hare-hare.
Haka nan kuma da akwai wasu Karin mutanen 334,000 da aka fitarsa fita daga gidajensu a cikin kwanaki uku, da hakan ya sa yawansu ya kai 60,000.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Imam Khamenei: Hadin kan al’ummar Iran a yakin kwanaki 12 ya sanya makiya kunya September 24, 2025 Larijani: Iran na kare tsaron kasa da azama September 24, 2025 Jagora: Iran Ba Za Ta Taba Yin Watsi Da Inganta Sinadarin Uranium Ba September 24, 2025 Larijani: Iran Tana Nazarin Shawarwarin Turai Da Na Rasha Domin Kare Muradunta September 24, 2025 Araqchi; Iran Da Norway Sun Tattaunawa Batun kyakkyawar Alakar Da Ke Tsakaninsu September 24, 2025 Groosi: Masu Binciken Hukumar Kula Da Makamashin Nukiliya Suna Hanyar Zuwa Iran September 24, 2025 Kasashen Afirka Uku Sun Sanar Da Ficewa Daga Kotun Hukunta Manyan Laifuka Ta Duniya September 24, 2025 Imam Khamenei Zai Yi Jawabi Ga mutanen Iran A Cikin Makon Tsaro Da Ya Shigo September 23, 2025 Lebanon: A yau Ne Aka Yi Jana’izar Shahidan Bitij Bail Wadanda HKI Ta Kai Ga Shahada A Ranar Lahadi September 23, 2025 Pezeshkiyan Ya Ce Tattaunawa Da Kasashe Masu Nuna Karfi Kan Wasu Ba Zai Taba Yi Yuwa Ba September 23, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci