Ba Gaskiya Ba Ne Rahoton Da Ke Cewa An Yi Sulhu Da Bello Turji – Guyawa Isa
Published: 8th, August 2025 GMT
“Shin an taɓa yin sulhu a na cin zarafin jama’a, an taɓa yin sulhu a na sa manoma noman dole, an taɓa yin sulhu a na karbar harajin dole, an taɓa yin sulhu ba a ajiye makamai ba?”
Ya ce Turji da sauran ‘yan bindigansa irin su Kachalla Choma da Kachalla Haru ba za su ajiye makami ba, ya ce suna da kwamandoji da makaman da sun fi a kirga.
Guyawa ya bayyana cewa Malamin bai san Turji ba, bai kuma san yankinsu ba, ya ce su da suke a yankin sun tabbatar Turji bai ajiye makami ba, kuma bai yi sulhu da kowa ba.
Ya ce a kwanan baya Turji ya kashe jami’an tsaro tare da ƙone motarsu, don haka idan ya yi sulhu ba zai yi hakan ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: an taɓa yin sulhu
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗan sandan bogi a Kano
Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi.
An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar.
An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno Sanata Natasha ta koma Majalisar DattawaSanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ’yan sanda domin damfarar jama’a.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce “binciken farko ya tabbatar cewa wanda ake zargin ba ɗan sanda ba ne, kuma ba shi da alaƙa da rundunar kwata-kwata.”
A wata hira da rundunar ta yi da mutumin wanda mazaunin Kofar Waika ne, ya ce sha’awar aikin ce ta sanya yake yi wa ’yan sandan sojan gona, inda yake bayar da hannu a kan titi domin samun na ɓatarwa.
Ya shaida cewa shaye-shayen da yake yi bai wuce na sigari da tabar wiwi ba, inda ya nemi a yi masa afuwa duk da ya nanata cewa duk duniya babu aikin da yake sha’awa kamar aikin ’yan sanda tare da neman a taimaka a dauke shi aikin.
Kazalika, ya bayyana cewa muradin ganin ya zama ɗan ya sanya shi sake aikata wannan laifi na sojan-gona duk da an taɓa kama shi da laifin a baya.
Tuni dai rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bayan kammala bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai ko ƙorafe-ƙorafe idan sun san wani abu game da wanda ake zargi ko makamantansa.