Idris ya ce a tsawon shekaru ‘yan Nijeriya suna tafiya Amurka saboda dalilai daban-daban, ciki har da yawon buɗe ido, kasuwanci, karatu, da kuma neman magani.

 

Ya ce: “An san Nijeriya a duniya a matsayin ƙasar da ‘yan ƙasar ta suke yawan yin tafiya zuwa ƙasashe daban-daban, suna hulɗa da ƙasashen duniya ta fuskar harkar kasuwanci, ilimi, yawon buɗe ido, da sauran muhimman fannoni.

Amurka na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin wuraren da ‘yan Nijeriya suka fi ziyarta, abin da ke nuna zurfin dangantaka mai tsawo tsakanin ƙasashen biyu.

 

“Yawancin ‘yan Nijeriya suna zuwa Amurka ne domin karatu, aiki, neman magani, ziyartar ‘yan’uwa, yawon buɗe ido, da damar zuba jari.

 

“Wannan mu’amala mai ƙarfi tana ci gaba da bunƙasa al’ummomin biyu.

 

“Sababbin abubuwan da Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana game da sauye-sauye a ayyukan ofishin jakadancin da hanyoyin neman bizar sun jima suna cikin labarai kwanan nan.

 

“Waɗannan sauye-sauyen, kamar yadda Ofishin Jakadancin Amurka ya bayyana, wani ɓangare ne na ƙoƙarin inganta bayar da sabis, ƙara saurin aiki, da mayar da martani ga sauye-sauyen buƙatun ayyukan jakadanci.”

 

Ministan ya yaba wa gwamnatin Amurka bisa ƙoƙarin yin bayani kai-tsaye ga ‘yan Nijeriya a wannan taro tare da tabbatar da samun sahihan bayanai na zamani ga kowa.

 

Haka kuma ya jaddada girmamawa da haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Amurka da kuma jajircewar Ofishin Jakadancin wajen sanar da matafiya ‘yan Nijeriya.

 

A nasa jawabin, Jakaden Amurka, Ambasada Mills, ya ce bin ƙa’idojin neman biza da dokokin Amurka na ‘yan Nijeriya abu ne mai muhimmanci wajen ƙarfafa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

 

“Bin dokokin neman biza na Amurka ba kawai wani nauyi ba ne, amma ginshiƙi ne na amincewa da girmama juna tsakanin ƙasashen biyu,” inji Ambasada Millis.

 

Ya ƙara da cewa: “Kamar yadda Minista ya bayyana, ni da shi mun yi tattaunawa mai amfani game da dokokin biza na Amurka da kuma yadda za mu isar wa ‘yan Nijeriya muhimmancin bin waɗannan dokokin.

 

“Bari in fayyace cewa Amurka tana daraja ƙarfaffar dangantakar ta da Nijeriya da kuma nau’o’in hulɗa da yawa da ke tsakanin ƙasashen biyu.

 

“Bizar Amurka na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da riƙe waɗannan lamurran dangantaka da ƙarfafa su, ko ta hanyar bai wa mutane damar tafiya domin ilimi, kasuwanci, yawon buɗe ido, ko musayar al’adu.”

 

Jakaden ya jaddada cewa ya zama dole a yi amfani da biza bisa ga dokoki da ƙa’idojin Amurka.

 

Ya ce: “Tabbas, muna maraba da baƙi ‘yan Nijeriya a Amurka kamar yadda Nijeriya take maraba da ‘yan Amurka masu zuwa wannan ƙasa. Dukkan gwamnatoci suna son baƙi su girmama dokokin ƙasashen mu da ƙa’idojin mu.”

 

Ya gargaɗi masu neman biza cewa yin amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba ko bayar da bayanan ƙarya yayin neman ta yana iya rage amincewar juna a tsakanin ƙasashen biyu.

 

Ya ce: “Muna kira ga dukkan masu neman biza da su bayar da sahihan bayanai kuma su bi sharuɗɗan biza ɗin su, domin na sani, mafi yawan ‘yan Nijeriya suna yin hakan. Ta yin haka, za mu ƙarfafa ɗorewar zumunci tsakanin ƙasashen mu.”

 

Ambasada Mills ya kuma yaba wa Idris bisa jajircewar sa wajen kare ‘yancin faɗar albarkacin baki a Nijeriya, yana mai jaddada cewa wannan ɗabi’a ce da ta yi daidai da manufofin Amurka.

 

Ya kuma yaba wa haɗin kai da ake samu daga hukumomin Nijeriya, ciki har da Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya, Hukumar Kwastan ta Nijeriya, da Fadar Shugaban Ƙasa, wajen wayar da kan jama’a kan ƙa’idojin biza.

 

Haka kuma ya shawarci ‘yan Nijeriya da su nemi sahihan bayanai daga shafin soshiyal midiya na Ofishin Jakadancin Amurka kuma su tabbatar da cewa duk wata tambaya da suke da ita za su samu amsa cikin lokaci.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yawon buɗe ido yan Nijeriya

এছাড়াও পড়ুন:

Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC

Ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar da sojoji ke mulki sun sanar cewa sun fice daga Kotun Duniya ta Hukunta Manyan Laifuka (ICC).

A sanarwar da suka fitar ranar Litinin sun bayyana ICC a matsayin “kayan aikin mulkin mallaka na zamani.”

Ƙasashen ukun, waɗanda aka yi juyin mulki a cikinsu tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023, sun kafa ƙawance mai suna Kungiyar Kasashen Sahel (AES) domin haɗa kai da nisantar da kansu daga ƙasashen Yamma, musamman tsohuwar mai mulkinsu, Faransa.

A cikin sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar, ƙasashen sun ce kotun da ke birnin Hague “kayan aikin danniya ce a hannun masu mulkin mallaka.”

’Yan sanda sun kama mutum 4 kan kai wa Lakurawa babura a Kebbi Faransa ta amince da ’yancin ƙasar Falasɗinu a hukumance

Sun ƙara da cewa, “ICC ta kasa tabbatar da shari’o’in manyan laifuka da suka haɗa da laifukan yaƙi, kisan gilla ga bil’adama, kisan ƙare dangi da kuma laifukan cin zarafin ƙasa.”

Sun ce suna shirin kafa “hanyoyin cikin gida domin tabbatar da zaman lafiya da adalci.”

Doka ta tanadar cewa ficewar kowace ƙasa daga ICC zai fara aiki ne shekara guda bayan an miƙa sanarwar ficewar ga Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya.

Tun bayan kafa AES, Burkina Faso da Mali da Nijar sun ƙara kusanci da ƙasashe irin su Rasha, wadda Shugabanta Vladimir Putin ke fuskantar sammacin kame daga ICC tun watan Maris 2023 kan yaƙin da ake yi a Ukraine.

Sai dai ƙasashen ukun na fama da hare-haren ta’addanci daga ƙungiyoyin masu alaƙa da Al-Qa’ida da Daesh, yayin da ake kuma zargin sojojinsu da aikata laifuka kan fararen hula.

Kotun ICC dai an kafa ta ne a 2002 domin gurfanar da waɗanda suka aikata manyan laifuka — musamman na yaƙi — a inda gwamnati ba ta da ikon ko kuma ba ta da niyyar ɗaukar mataki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kasar Sin Ta Mallaki Kusan Tashoshin Fasahar 5G Miliyan 4.65
  • Jakadan Amurka Ya Amince Da Cewa Amurka Tana Nufin Hada Yaki Tsakanin Sojojin Lebanon Da Hizbullah
  • Burkina Faso, Mali da Nijar sun fice daga Kotun ICC
  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • Babu Gwamnatin Sojin Da Ta Kai Ta  Tinubu Muni A Tarihin Nijeriya
  • Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi                         
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Hau Turbar Hadin Gwiwa Da Samun Moriyar Juna A Sabon Lokaci
  • Ko Ka San Dalilin Da Zai Bai Wa Nijeriya Damar Zuwa Gasar Cin Kofin Duniya?
  • Gwamna Lawal Ya Raba Kayan Karatu 408,137 Ga Makarantun Gwamnatin Zamfara
  • Ko Ƙasashen Musulmi Za Su Iya Kafa Ƙawancen Tsaro Don Tunkarar Abokan Gaba?