NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026
Published: 7th, August 2025 GMT
Hukumar NAHCON mai kula da sha’anin aikin Hajji a Nijeriya NAHCON, ta bayyana cewa an ƙayyade naira miliyan 8.5 a matsayin kafin alƙalami na kuɗin kujerar aikin Hajjin 2026.
NAHCON ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar a yau Alhamis, bayan gudanar da taro da shugabanni da kuma sakatarorin hukumomin aikin hajji na jihohin ƙasar.
Mai magana da yawun NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta ce an ƙayyade ƙafin alƙalamin kuɗin kujerar domin fara shirye-shiryen ibadar ta wannan shekarar ta Musulunci.
Hajiya Fatima ta ambato shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, yana cewa an ƙayyade miliyan 8.5 ɗin ne a matsayin kafin alƙalami na aikin hajjin baɗi, kafin a kammala tattaunawa don sanin haƙikanin kuɗin.
Ya ce Saudiyya ta sake bai wa Nijeriya gurbin kujeru 95,000, kamar yadda ta samu a bara.
Farfesa Usman ya kuma yaba wa shugaba Bola Tinubu bisa irin goyon baya da yake bai wa hukumar da kuma alhazan Nijeriya.
A cewarsa, ƙoƙarin da gwamnatin tarayyar ta yi ne ma ya sa kamfanonin jirage suka amince suka karɓi biyan kuɗi da naira daga wajen alhazai a bara maimakon dala, domin saukaka musu.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Birtaniya Zata Amince Da Falasɗin A Matsayin Ƙasa
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp