Iran: Babu wani abu da aka yanke game da tattaunawa da Washington
Published: 11th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa “babu wani abu da aka yanke ya yanzu game da tattaunawa da Amurka,” ya kara da cewa “babu wani tabbci kan zabar wata kasa da za ta karbi bakuncin tattaunawar.”
A jawabin da ya yi a gefen taron majalisar ministocin a jiya Lahadi, Araqchi ya yi jawabi kan ziyarar mataimakin babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya IAEA wanda ke shirin isa birnin Tehran a yau litinin.
Araqchi ya bayyana cewa “babu wani shiri na ziyartar wata tashar nukiliya kafin a cimma wata matsaya kan hakan,” ya kara da cewa wannan tsarin “zai dogara ne kan dokar majalisar dokokin kasar Iran kawa,” kuma “ba za a fara wasu ayyuka na hadin gwiwa tsakanin Iran da hukumar IAEA ba har sai majalisar ta fayyace matsayin haka a bisa dokar kasa.”
Bugu da kari, Araqchi ya yi nuni da cewa, ana ci gaba da tuntubar juna tsakanin kasarsa da kasashen Turai, inda ya kara da cewa, sun tabo batun mayar da takunkumin da aka kakaba mata wanda aka dauke bayan cimma yarjejeniyar nukiliya a shekarar 2015.
Araghchi ya bayyana cewa matsayin Iran kan shawara da Turai shi ne cewa, Iran Ba a daukar kasashen Turai a matsayin wani bangare a cikin yarjejeniyar nukiliya, amma dai a halin yanzu masana daga bangarorin biyu suna tattaunawa kan batutuwa da suka shafi bangaren fasaha ne kawai ba kan sauran batutuwa na yarjejeniyar nukiliya ba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza August 11, 2025 Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari August 11, 2025 Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara August 10, 2025 Dangantaka Tsakanin Iran da Saudiya Yana Taimakawa Zaman Lafiya A yankin August 10, 2025 Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba August 10, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya August 10, 2025 An Zabi Alkalan Wasa Biyu Daga Kasar Iran Don Alkalanci A gasar Kwallon Kafa ta Mata August 10, 2025 Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Iran Ta Cimma Matsayi A Yaki Kwanaki 12 August 10, 2025 Jami’an Tsaron Iran Sun Murkushe ‘Yan Ta’adda Kan Ofishin ‘Yan Sanda A Kudu Maso Gabashin Kasar August 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin
Miliyoyin mutanen kasar Iran sun gudanar da jana’izar shahidai kimani 300, a duk fadin kasar, a dai-dai lokacinda ake makokin shahadar diyar manzon Allah (s) Fatimah Azzahra (s).
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa, shahidan, wadanda har yanzun ba’a tantance su ba, an ganosu a wurare daban-daban a cikin kasar Iran inda suka yi shahada a yakin shekaru 8 tsakanin Iran da Iraki a farko-farkon nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran. (1980-1988).
Ya zuwa yanzu dai an gano gawakin shahidai fiye da 45,000, sannan akwai wasu fiye da 2000 wadanda ake neman inda suke a cikin kasar ta Iraki.
Labarin ya kara da cewa a nan Tehran kadai an yi jana’izar shahidai 100. Sannan sauran gawakin shahidan, wadanda aka ganosu a tsibirin Maimoon da Shalamce, an yi masu jana’iza a lardin Golestan, Qom, Fars, Sistan da Baluchestan, Ardabil, gabacin Azerbaijan da wasu wurare.
Wadannan shahidan sun yi shahada ne a ayyukan farmaki na Kheibar, Karbala-4, Karbala-5, da kuma Valfajr-1.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Tsirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Hamas Ta Ce Keta Hurumin Tsagaita Wutan Da HKI Take Yi Zai Iya Kawo Karshen Tsagaita Wutar November 25, 2025 Gwamnonin Kudu Maso Yammacin Najeriya Sun Ce Lokacin Kafa Yansandan Jihohi Ya Yi November 25, 2025 Hizbullah Ta na Juyayin shahadar Babban Kwamanda Haitham Ali Da Isra’ila Ta Kashe. November 24, 2025 Dubban Alummar Kasar Tunisia Ne Suka Gudanar Da Zanga-zangar Adawa Da Mulkin Kama Karya A Kasar November 24, 2025 Mutane 6 Ne Suka Mutu Sakamakon Harin Kunar Bakin Wake Da Aka Kai A Peshavar Na Kasar Pakistan November 24, 2025 Hamas Tayi Gargadi Game Da Rushewar Yarjejeniyar Bude Wuta Idan Israila Ta ci Gaba Da Kai Hare-Hare November 24, 2025 Amnesty International Ta Zargi Najeriya Da Gazawa Wajen Kare Rayukan Al’ummarta November 24, 2025 Wakilin MDD Ya Bukaci Goyon Bayan Iran Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya A Yamen November 24, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci