2025-08-04@17:43:20 GMT
إجمالي نتائج البحث: 10

«cikin ɗari»:

    Hukumar da ke shirya jarabawa kammala karatun sakandire a Afrika ta Yamma (WAEC), ta saki sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2025. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 4 ga Agustan 2025, tana mai cewa dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar yanzu za su iya duba sakamakon nasu a shafinta na intanet. Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti “WAEC na farin cikin sanar da ɗalibai da suka rubuta jarabawar WASSCE a shekarar 2025 cewa an saki sakamakon a hukumance yau Litinin, 4 ga watan Agusta,” in ji sanarwar. WAEC ta buƙaci ɗalibai da su shiga...
    Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu, ya umarci dakarun sojin Najeriya da su murƙushe ’yan ta’adda, masu tada ƙayar baya, da ’yan awaren Biyafara da ke barazana ga zaman lafiya da haɗin kan ƙasa. Yayin bikin Ranar Sojoji ta 2025 da ya gudana a Jihar Kaduna, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima ya wakilci Shugaba Tinubu. Mutum 21 sun rasu a hatsarin mota a kan hanyar Zariya–Kano Zulum ya musanta shirin ficewa daga APC Tinubu ya ce: “Lokacin tashi ya yi. Ina tare da ku ɗari bisa ɗari don murƙushe masu yunƙurin rusa Najeriya. Ku ne ƙarfina, goyon bayana da addu’o’ina.” Ya gargaɗi cewa barazanar da ake fuskanta ba ƙananan abubuwa ba ne. “Waɗannan miyagun ba sa bambanta tsakanin coci da masallaci. Suna...
    Shugaban Amurka, Donald Trump na shan suka daga wasu jagororin mabiya ɗarikar Katolika, saboda wallafa hotonsa da ya samo daga manhajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, sanye da kayan fafaroma. Mista Trump ya wallafa hoton ne a shafukan sada zumunta na fadar White House. Matakin na zuwa ne yayin da mabiyar ɗarikar Katolika, ke shirin zaɓen sabon fafaroma, bayan alhinin da suke ciki na rasuwar jagoran ɗarikar, Fafaroma Francis, wanda ya mutu ranar 21 ga watan Afrilu. Taron mabiya ɗarikar Katorlika na birnin New York ya zargi Shugaba Trump da zolayar Addininsu. Wallafa hoton na zuwa ne kwanaki bayan da shugaban ya zolayi wani mai bayar da rahotonni da cewa ”ina son zama fafaroma” Ba Trump ne shugaban Amurka na farko...
    Ya kara da cewa, shugaban kasa Bola Tinubu da sojojin Nijeriya suna aiki tukuru domin ganin an ga sauye-sauye a yaki da ta’addanci da ake yi, a fili kuma a bayyane. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mazauna sun shiga zaman ɗar-ɗar a yayin da motocin yaƙi na sojoji suka mamaye Gidan Gwamnatin Jihar Ribas. Wannan dai na zuwa ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci a jihar. Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Tinubu ya sanya dokar ta-baci a Jihar Ribas Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa fiye da motocin soji 10 aka hanga suna sintiri a kan hanyar zuwa gidan gwamnatin yayin da wasu motocin yaƙi masu sulke suka tsaya wuri-wuri a hanyar. Majiyar ta ce titunan birnin na Fatakwal sun zama fayau a yayin da mazauna suka tsere gidajensu. Babu tabbaci ko gwamnan da aka dakatar, Similanayi Fubara yana cikin gidan gwamnatin a halin yanzu....
    A cewar Dunbai, gwamnatin kasar Sin tana kara inganta alakarta da jihar Kano a fannonin samar da abinci, kayayyakin more rayuwa, ilimi, tare da kasuwanci da gwamnatin jihar.   A fannin aikin gona, wakilin kasar Sin ya yi nuni da muhimmancin samar da abinci a jihar Kano, inda ya ce, jihar da ke da dimbin al’umma kamar kasar Sin, ta cancanci amfani da fasahohin zamani a fannin noma don karfafa samar da dimbin abinci. A cikin sanarwar, Mista Dunhai ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta ci moriyar damar da kasar Sin ta samar na zuba jari a Nijeriya na sama da dala tiriliyan 20, domin farfado da ci gaban masana’antu da kasuwanci.   A nasa jawabin, Gwamna Yusuf,...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar kasuwanci ta Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida game da shirin Japan na aiwatar da matakan hana fitar da kayayyaki zuwa Sin, ciki har da semiconductor. Kakakin ya bayyana cewa, shirin bangaren Japan na aiwatar da matakan, zai kawo cikas ga tsaro da kwanciyar hankali na tsarin masana’antu, da gurgunta mu’amalar kasuwanci na yau da kullum dake tsakanin kamfanoni, da kuma lalata muradun kamfanonin kasashen biyu. Dangantakar Cinikayya Da Sin Ta Budewa Afrika Kofar Samun Ci Gaba Ana ɗar ɗar Kan Mutuwar Sojoji Bayan Da Mota Ta Kwace A Legas Sin na fatan kasar Japan za ta ji ra’ayoyin masana’antu, ta kuma gaggauta gyara ayyukan da ta yi bisa tushen kiyaye ka’idojin tattalin arziki da cinikayya...
    Wani direba da ake zargin yana cikin maye ya kutsa da motarsa cikin wani gungu na sojoji daga barikin Myoung da ke Yaba dake jihar Legas, yayin da suke atisayen motsa jiki da safiyar yau Juma’a, lamarin da ake jin tsoron cewa ya yi sanadiyyar mutuwar Sojojin da dama. Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya haifar da tashin hankali a cikin sansanin Sojojin. Wani Soja da ya tsira daga harin ya bayyana cewa, “Jini ne ko’ina. Na tsira ne kawai saboda ina baya.” Mun Kashe Ƴan Ta’adda Sama Da 70, Kafin Mu Yi Rashin 22 – Sojoji Sojoji Sun Ƙwato Makamai, Sun Ci Gaba Da Neman Bello Turji A Zamfara Sojan (wanda ba a bayyana sunansa ba) ya ce a...
    An gudanar da taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ɗariƙar Tijjaniyya daga sassan Nijeriya daban-daban sun halarci taron Maulidin na Shehu Ibrahim Inyas na shekara-shekara da aka gudanar a Filin Wasa na Sani Abacha da ke ƙwaryar Birnin Dabo. An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania Sai dai tun a jiya Juma’a ce mai magana da yawun ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar da sanarwa mai ɗauke da gargaɗin cewa ’yan ta’adda na shirin kai hari a jihar saboda haka jama’a su ƙauracewa duk wani taro da shiga cunkoso. Daga bisani...
۱