2025-10-13@20:18:52 GMT
إجمالي نتائج البحث: 224
«yaran da ba a»:
Garin Girfa (cinnamon), Garin kaninfari Clove) Yadda za a hada: Za’a samu garin girfa kamar cokali 5 garin kaninfari cokali 7 za a hade waje daya, sai a rika diban rabin karamin cokali ana zubawa a ruwan shayi ana sha sau 2 a rana ayi kamar sati daya. Za a samu waraka da yardar Allah. Ciwon Sanyi Abubuwan bukata: Hulba, Bagaruwa, Man Habbatussauda yadda za a hada: A hada Bagaruwa da Hulba a tafasa su, sai idan ya dan huce sai a zauna a ciki, sannan kuma za a shafa man Habbatussauda a gaban, a sashi kamar yadda za’a yi matsi. In sha Allah za a samu sauki. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Adon Gari Ko Kin San… Dalilin...
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce talauci da nuna bambanci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata damar samun ilimi a jihar. Ta bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Yara Mata ’Yan Makaranta ta Duniya ta shekarar 2025, wanda Shirin AGILE tare da Access Initiative Africa da Nudge Initiative suka shirya a Gombe. Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a Borno A wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba da yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a bar wata yarinya a baya wajen samun ilimi....

Kasar Sin Ta Samu Manyan Nasarori A Fannin Inganta Walwalar Yara Da Tsoffi Cikin Shekaru 5 Da Suka Gabata
Ministan kula da harkokin al’umma na kasar Sin Lu Zhiyuan, ya ce cikin wa’adin shirin raya kasa na shekaru 5-5 na 14 tsakanin 2021 zuwa 2025, walwalar yara da tsoffi a kasar, ta samu gagarumin ci gaba. Lu Zhiyuan, ya bayyana yayin wani taron manema labarai a yau Juma’a cewa, yayin wa’adin shirin, an samar da wani cikakken tsarin bayar da kariya da kulawa ga yara mabukata, wanda ya shafi yaran da ba sa gaban iyayensu saboda wasu dalilai, da yaran da iyayensu suka yi nesa da gida, da yaran da suka kaura, inda a yanzu dukkansu ke cin gajiyar hidimomin kariya da kulawa na kasar. Har ila yau a wa’adin, kasar Sin ta kammala gyarawa da sake fasalin kayayyakin...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10, kwatankwacin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana hakan a Maiduguri ranar Laraba yayin ƙaddamar da wani shirin farfaɗo da rayuwar yara da rikici ya shafa ta hanyar ba su horo da tallafi. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya An wakilta Saeed ta hannun Manajan Kare Yara na UNICEF, Shah Mohammad Khan, inda ta ce rikicin da ya daɗe ya rage girman tattalin arzikin ƙasar, ya kuma lalata...
An yi wa yara miliyan biyu da dubu takwas allura, yayin aikin rigakafin cutar Polio, kyanda, da kuma Gaida a jihar Sakkwato. Gwamna Ahmed Aliyu Sokoto ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin da aka gudanar a garin Bodinga da ke karamar hukumar Bodinga. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan hulda da manema labarai na ofishin mataimakin gwamnan jihar, Garba Muhammed, Alhaji Ahmed Aliyu ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa aikin polio din zai gudana ne a daukacin unguwanni 244 dake fadin jihar. Don haka ya yi kira ga shugabannin al’umma da na addini da kuma abokan ci gaba da masu ruwa da tsaki da su ba da himma wajen...
Wata Kotun Majistare da ke Kano ta bayar da umarnin a tura Ashiru Idris, wanda aka fi sani da Mai Wushirya, gidan gyaran hali na tsawon mako biyu saboda wallafa bidiyon batsa da ya shafi budurwa (dwarf) da ba a bayyana sunanta ba, a dandalin sada zumunta.Mai shari’a Halima Wali ta Kotun Majistare mai lamba 7 ce ta bayar da wannan umarni, tana mai cewa a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali kafin a dawo da ƙarar don ci gaba da sauraro.Kotu Ta Yanke Wa Ɗan TikTok Tsulange Hukuncin Ɗauri Kan Shigar Zubar Da MutunciSin Da Amurka Sun Yi Tattaunawar Keke-da-keke Kan Batutuwan Cinikayya Da Manhajar TikTokHukumar kula finafinai da ɗab’i ta jihar Kano ce ta kama...
Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
Uwargidan Gwamnan Jihar Ribas, Eyoanwan Bassey Otu, ta ce aƙalla mata da ƙananan yara 95,000 ne ke mutuwa a kowace shekara a Najeriya sakamakon shaƙar hayaƙin girki. Ta bayyana haka ne yayin wani taron wayar da kai da aka gudanar a ofishinta da ke Kalaba, inda ta jaddada buƙatar amfani da hanyoyin girki masu tsafta da aminci a Najeriya. Wike ya gana da Fubara da dattawan Ribas kafin kafa sabuwar majalisar zartarwa Rundunar Sojin Nijeriya ta cafke jami’anta 16 kan saɓa ƙa’idar aiki Uwargidan gwamnan, wacce Asi Akiba, matar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kalaba, Kalaba ta Kudu da Odukpani ta wakilta, ta ce hayaƙin itacen girki da sauran hanyoyin da ba su da inganci sun zama hanyar mutuwa ta...
Akwai amfani saboda watarana wani abu zai taso mai muhimmanci, iyayensa ba sa kusa za su saukaka ta hanyar kiransu. Matsalar sa lalacewar karatu, koyan dabi’un marasa kyau da masu kyau, basu ko siya musu ba laifi ba ne, amma dai a tsananta saka musu ido dan gudun baraka da lalacewa. Ya zamo kiran mai amfani ne da karatu za su rika yi da shi, ba tiktok ko Instagram ko Twitter ba. Allah ka shirya mana zuriya, ka sa mu dace. Sunana Anas Bin Malik Achilafiya, Karamar Hukumar ‘Yankwashi, Jihar Jigawa: Amfanin bayar da waya ga kananan yara; yana saukaka musu sadarwa ga iyaye, abokai, da sauran su, samun ilimi da bincike ta hanyar intanet. Iya jawo jaraba, ko dogaro...
An gudanar da wani samame na musamman wanda ya kai ga gano bindigar da kuma cafke wadanda ake zargin. Jami’in da ya jikkata yana karbar magani a halin yanzu.” “A Damaturu, jami’an sashen A’ na Hedkwatar ‘Yansanda sun cafke Ibrahim Alhaji Ahmadu, mai shekaru 24, bisa zargin shiga gona da dabbobi da kuma yi wa wani manomi barazana da bindiga. An kwato bindiga mai kananan harsasai daga hannunsa. Rundunar ta jaddada cewa mallaka da amfani da makamai wajen tsoratar da fararen hula babban laifi ne.” Haka kuma, rundunar ta bayyana cewa, “A Potiskum, an kama Dahiru Ali, mai shekaru 19, bisa zargin lalata da wata yarinya ‘yar shekara uku. Bincike ya gano cewa wanda ake zargin ya taba aikata irin...
Mista Fall ya jagoranci tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kunshi wakilai daga UNICEF, UNESCO, UNDP, UNFPA, da mata na Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron. Ya jaddada cewa canjin al’umma ya ta’allaka ne akan jarin dan’Adam musamman ta hanyar ilmantar da ‘ya’ya mata da karfafa wa mata. Ya kara da cewa, “tare da gwamnati da abokan huldarmu, mun himmatu wajen kawar da duk wani cikas da ke hana yara, musamman ma masu rauni damar samun ilimi”. Fall ya gano muhimman abubuwan da ke kawo cikas ga ilimi a Nijeriya, da suka hada da rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, sauyin yanayi, da kuma ka’idojin zamantakewa da al’adu. Ya yi kira da a kara himma wajen inganta daidaiton jinsi...

Shugaban Gidauniyar Malala, ya jaddada kudirin gidauniyar na bunkasa ilimin yara mata a fadin Najeriya.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya. Da yake jawabi, shugaban gidauniyar Malala, Mista Ziouddin Yousafzai ya yaba da kyakkyawar tarba da aka yi masa tare da tawagarsa, inda ya bayyana Masarautar Zazzau a matsayin babbar abokiyar tarayya wajen ciyar da manufofin Gidauniyar gaba. Ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa da cibiyoyin gargajiya domin bunkasa samun ilimi da karfafawa ‘ya’ya mata samun damar da suke da ita. A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, ya yabawa gidauniyar Malala bisa ci gaba da tallafawa wajen inganta ilimin yara mata, musamman a Arewacin Najeriya. Sarkin ya yi...
Mazauna unguwar Sabon Gero, dake bayan Millennium City a Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, sun roƙi gwamnatin jihar da ta gaggauta kammala aikin gyaran titin unguwar, wanda suka ce an bar shi a cikin mawuyacin hali duk da cewa an bai wa wani kamfani aikin kusan shekara guda da ta gabata. Mazauna yankin sun bayyana cewa halin da hanyar take ciki ya jefa su cikin matsanancin rayuwa, musamman mata masu juna biyu da ke tilasta musu hawa babura domin neman kulawa a wajen unguwar, kasancewar babu asibiti a yankin. Ɗaya daga cikin mazauna, Rashida Shehu, wadda ke da juna biyu, ta ce ta ji rauni a lokacin da take kokarin bin hanyar zuwa gari domin kula...
Aƙalla makarantu 188 na gwamnati aka rufe a Arewacin Najeriya sakamakon ta’azzarar matsalar tsaro. ’Yan bindiga sun kai wa wasu makarantun hari, yayin da wasu kuma yanzu ana amfani da su a matsayin mafakar ’yan gudun hijira ko sansanonin sojoji. Antoine Griezmann ya ci ƙwallo 200 a Atletico Kwamitin Shura ya dakatar da Malam Lawan Triumph daga yin wa’azi a Kano Rahotanni sun nuna cewa an rufe makarantu 39 a Zamfara, 30 a Jihar Neja, shida a Sakkwato da Kaduna, 52 a Katsina, sannan 55 a Benuwe. Adadin na iya haura haka saboda akwai yankunan da ba za a iya shiga ba don gudanar da bincike ba. Binciken bai haɗa da jihohin Borno, Yobe da Adamawa ba waɗanda Boko Haram...
Sama da al’ummomi 100 a karamar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara sun samu ayyukan raya kasa don kyautata rayuwa ga mazauna. Shugaban zartarwa na karamar hukumar Ifelodun, Alhaji Abdulrasheed Yusuf, ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai ayyukan gwamnatinsa a cikin shekara daya da ta gabata, yayin da ya ke gabatar da wani shirin Newskeg of the Correspondents’ Chapel na NUJ, majalisar jihar Kwara, wanda aka gudanar a Ilorin. Ya lissafta ayyuka da dama da aka kammala, wadanda suka hada da gine-gine da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko a Oke-Ode, Labaka Oja, Adanla, Ofarese, Ijaya-Share, da Ajapa, da samar da kayan aikin likita da samar da muhimman magunguna a fadin cibiyoyin...
Gwamnatin Jihar Gombe ta ƙaddamar da wani shiri na rajistar yara kyauta domin rage adadin waɗanda ke zaune gida ba tare da zuwa makaranta ba. Bincike ya nuna cewa fiye da yara 787,000 ne ba sa zuwa makaranta a faɗin jihar, wanda hakan ya sanya gwamnatin ta tashi tsaye wajen kawo sauyi a ɓangaren ilimi. Mata masu zaman kansu za su fara biyan haraji a Nijeriya An yi garkuwa da tsohon Shugaban SUBEB na Jihar Neja Uwargidan Gwamnan Gombe, Hajiya Asma’u Inuwa Yahaya, ce ta ƙaddamar da shirin a hukumance, inda ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na ganin kowane yaro ya samu damar karatu. A cewarta, shirin zai taimaka...
Hukumar kula da gyaran manyan hanyoyi ta ƙasa (FERMA) reshen Jihar Kaduna, ta ƙaddamar da aikin gyaran tsohuwar hanyar Zariya zuwa Makarfi wadda ta haura zuwa Kano. Aikin zai haɗa da tono ciyayi, cike ramuka, da yashe magudanan ruwa tare da samar da ayyukan yi na wucin gadi ga matasa da ke yankin. ’Yan sanda sun kama kwayoyin N165.4m da makamai a Kano ASUU ta bayar da wa’adin tsunduma yajin aiki a faɗin Nijeriya Da yake ƙaddamar da shirin a Basawa, Zariya, shugaban FERMA na jihar Kaduna, Injiniya Kabir Iliyasu Danmarke, ya bayyana cewa aikin umurni ne daga shugaban hukumar na ƙasa, Dr. Chuku Emeka Obasi, bisa kudurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na rage haɗurra a hanyoyi. “Mun ɗauki...
Shekara guda matafiya da direbobi a ƙauyukan Malori-Guskuri da Sabon Gari da ke Ƙaramar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi na ci gaba da fama da wahala bayan da ruwan sama ya karya babban titin Kano–Maiduguri. A ranar 7 ga Agusta, 2024 ne ruwa ya cinye babbar hanyar a Malori-Guskuri, ya kuma yanke babban ɓangare na hanya. Mako guda bayan nan kuma wani ɓangaren ya rushe a Sabon Gari. Shekara guda da wata ɗaya bayan faruwar lamarin, wanda ya mayar wuraren da suka rushe sun koma tarkon mutuwa da ke haddasa haɗurra da suka kashe mutane da raunata wasu da dama. Wakilinmu da ya kai ziyara ya samu wani kamfanin gine-gine ya dawo Malori da kayan aikinsa. Mazauna sun tabbatar da...
Shugaban kasar Argentina Javier Milei ya bukaci firaminista Benjamin Netanyahu da ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa kasar Argentina gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, saboda hakan na iya kara cutar da farin jininsa da tuni ya ragu. A cewar jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila, Netanyahu ya kasance yana shirye-shiryen tafiya zuwa Buenos Aires, amma Milei ya nemi ya jinkirta tafiyar. Da cewa da cewa Milei sananne ne wajen nuna goyon bayan ido rufe ga “Isra’ila”, an ba da rahoton cewa shugaban na Argentina ya damu da cewa ziyarar Netanyahu za ta yi masa mummunar tasiri a siyasance. Kasar Argentina dai na daga cikin kasashen da har yanzu suke da damar karbar Netanyahu, wanda kotun hukunta manyan laifuka...
Akalla yara miliyan 4.8 ne ake shirin yi wa allurar rigakafin cutar kyanda da cutar shan inna a jihar Katsina a wani bangare na shirin allurar riga-kafi da aka shirya yi a wata mai zuwa. Shugabar ofishin kula da kananan yara ta UNICEF, Rahama Farah, ce ta sanar da hakan a wani taron tattaunawa da wayar da kan masu ruwa da tsaki a shafukan sada zumunta da aka gudanar a Katsina a wani bangare na shirye-shiryen rigakafin da ke tafe. Ya bayyana cewa za a yi allurar rigakafin cutar kyanda ga yara ‘yan tsakanin watanni 9 zuwa 14 yayin da za a yi allurar rigakafin cutar shan inna ga yara ‘yan kasa da shekaru biyar. Mista Farah...
A lokacin hatsarin karfen sauya hanyar ya karye gaba daya, wanda ya haifar da hatsarin. Hukumar ta kuma gano cewa duk da cewa direbobin jirgin ƙwararru ne, ba a ba su sabon horo ba. An kuma gano cewa wasu muhimman kayan aiki kamar na’urar CCTV, na’urar sadarwa da agogo sun samu matsala. NSIB ta shawarci NRC da ta gyara dukkanin kayan da suka lalace, ta sanya sabbin karafan sauya hanya, sannan ta riƙa horar da ma’aikata akai-akai don gujewa irin wannan matsala. A lokacin hatsarin, mutane 21 ne suka ji rauni daga cikin fasinjoji 618 da ke cikin jirgin, amma babu wanda ya rasu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai...
Haka nan a nasa ta’alikin da ya gabatar Malam Abubakar Abba Dewu ya jawo hankalin Malaman Islamiyoyi, domin su kasanca masu shirya irin wadanan muhadirorin lokacin Bayan lokacin a Makarantun su, domin cusawa Mata da ƙananan yara jin Tsoron Allah tare da yin abin da ya dace da koyarwar addinini Musulunci a bisa sunnar Annabi Muhammad (saww). Haka nan a lokacin da take miƙa jawabi godiya a gun taron Shugaban Makaranta Malam Halima Musa ta ce, suna shirya irin wannan muhadaran ne lokaci bayan lokacin sabo da cusawa Mata da ƙananan yara tsoron Allah a zukata. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta kama mutum biyar da ake zargi da satar fakiti 7,871 na abincin yara, wanda aka fi sani da Tamuwa, wanda aka tanada don yara masu fama da cutar yunwa. Kakakin rundunar, ASP Nahum Kenneth Daso ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 19 ga Satumba, 2025 . Ya bayyana cewa an gano kayan ne a samame guda biyu da aka kai a Maiduguri. Shettima ya bar Abuja don halartar taron majalisar ɗinkin duniya a New York An sanya tukwicin N10m domin kama makasan limamin coci a Enugu Samamen farko ya auku ne a ranar 12 ga Afrilu, lokacin da aka tsayar da wata mota a Njimtilo, kusa da Maiduguri, inda...
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya ce duk wani shugaba da bai yi aiki yadda ya kamata ba, bai kamata a sake zaɓarsa ba. Ya yi gargaɗin cewa maguɗin zaɓe na ɗaya daga cikin manyan barazana ga dimokuraɗiyya a Afirka, kuma idan ba a gyara tsarin ba, ’yan kama-karya za su zama wajen zama. Yadda za ka dawo da kuɗinka da ka yi kuskuren turawa wa wani An tsinci gawar kwamandan hukumar NDLEA a otel a Kalaba Jonathan, ya yi wannan jawabi ne a taron shekara-shekara na Tattaunawar Gidauniyar Goodluck Jonathan da aka gudanar a Birnin Accra, na Ƙasar Ghana. Ya ce mutanen Afirka na son a yi amfani da ƙuri’unsu don su samu shugabanni da za su inganta ilimi,...
Daga nan ya wuce gidan tsohon shugaban ƙasa Marigayi Muhammadu Buhari domin yi wa matar sa Aisha da sauran ‘yan uwa ta’aziyya. Tinubu a gidan marigayi tsohon shugaban kasa, Buhari Ya bayyana Buhari a matsayin “shugaba mai kishin ƙasa da sadaukarwa, wanda gudunmawarsa ga haɗin kan Najeriya da ci gabanta ba za a manta da su ba,” inda ya tabbatar da ci gaba da goyon bayansa ga iyalan. Cikin manyan baki da suka halarci taron har da Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi; Gwamna Umar Bago na Jihar Neja; Gwamna Dikko Radda na Katsina; Gwamna AbdulRahman AbdulRazak na Kwara da Ministan Tsaro, Bello Matawalle. Sauran sun haɗa da tsoffin gwamnoni Sule Lamido na Jigawa; Aliyu Wamakko na Sakkwato;...
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauya sunan ma’aikatar harkokin mata, yara da nakasassu a hukumance zuwa “Ma’aikatar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman.” Wannan dabarar yanke shawara, ga kwamishiniyar harkokin mata Ambasada Hajiya Amina Sani Abdullahi, ta nuna irin kwakkwaran kudurin gwamnati na inganta mutunci, hada kai, da daidaito ga dukkan ‘yan kasa musamman masu bukata ta musamman. A cewarta, sake suna ya yi daidai da mafi kyawun ayyuka na duniya ta hanyar maye gurbin tsoffin kalmomin da za su iya ɓata lokaci da mutane-harshen farko wanda ke mutunta haƙƙin ɗan adam da kuma kiyaye ƙa’idodin adalci na zamantakewa. “Wannan canjin ya wuce alama yana nuna dabi’un mu a matsayin...
Gwamnatin Jihar Gombe, ta fara aikin gyara da sake duba hanyoyin kiwo 37 tare da filayen kiwo takwas a faɗin jihar. Wannan aiki na daga cikin matakan da ake ɗauka domin rage rikici da ake samu tsakanin manoma da makiyaya. HOTUNA: Yadda dubban magoya baya suka yi dafifi don tarbar Fubara Microsoft ya ƙwace shafukan wasu kamfanoni 340 a Najeriya An gudanar da aikin ne ƙarƙashin shirin ‘Livestock Productivity and Resilience Support (L-PRES)’ a matsayin wani ɓangare na gwamnatin jihar don samar da zaman lafiya. Shugaban shirin na jihar, Farfesa Usman Bello Abubakar, ya bayyana cewa ana fuskantar matsaloli ne saboda lalacewar hanyoyin kiwo da gonaki. A baya-bayan nan, tawagar shirin tare da jami’an tsaro, shugabannin gargajiya da jagororin makiyaya,...
Hukumar Kula da Inshorar Lafiya ta Kasa (NHIA) a ranar Laraba ta kaddamar da shirin bayar da kulawar lafiyar gaggawa kyauta ga yara a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Kano. Shirin, a cewar Darakta a hukumar, Dr. Salahudeen Sikiru, wani bangare ne na fadada shirin lafiyar iyaye da NHIA ke aiwatarwa zuwa ga yara masu rauni da masu bukata ta musamman. Tun Tinubu yana Gwamna ba abin da ya fi shahara da shi kamar tara haraji – Adebayo Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono Ya ce an fara shirin fiye da shekara ɗaya da ta gabata da nufin rage mace-macen jarirai ’yan kasa da shekaru biyar. “Mun fara wannan shiri fiye da shekara...
Ɗan takarar jam’iyyar Labour a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da kuma sabon Olubadan na Ibadan, Rashidi Ladoja, a wani zagayen ganawa da manyan ’yan siyasa gabanin zaɓen 2027. Obi, wanda ke ƙoƙarin ƙara yauƙaƙa zumunci da manyan shugabanni a fadin ƙasar, ya bayyana cewa ziyarar na da alaƙa da burinsa na ganin an samu shugabanci na gaskiya da riƙon amana a Najeriya. An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar KEDCO ya ƙaryata asibitin AKTH kan mutuwar majinyata saboda ɗauke wuta A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ziyararsa ta musamman zuwa Ibadan na da nufin girmama Rashidi Ladoja,...
A cikin shekaru uku da kafuwarta, gidauniyar Misilli, ta mayar da yara 150 makarantar boko a Jihar Gombe, ciki har da mata 88 da maza 62, tare da ɗaukar nauyin kuɗaɗen karatunsu. Wannan mataki ya taimaka wajen rage nauyin iyaye marasa hali, inda suka samu ’yancin zaɓar makarantun da ke kusa da su. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe An yi wa zakarun wasan motsa jiki ruwan kuɗi a Akwa Ibom Shirin AGILE ya tallafa wa gidauniyar da litattafai domin ƙarfafa wannan yunƙuri, lamarin da shugabar shirin a Gombe, Dokta Amina Haruna Abdul, ta yaba da shi tare da alƙawarin yin haɗin gwiwa. Ita ma, Dokta Hauwa Yahaya Umar daga SUBEB, ta ce irin wannan...
Rundunar ‘yansandan jihar Adamawa ta ce ta ceto wasu yara biyar da ake zargin sato su aka yi, daga Maiduguri jihar Borno zuwa Adamawa. Kwamandan yankin na Mubi, ACP Marcos Mancha, a ranar 13 ga Satumba, 2025, a yayin da ya samu wasu bayanan sirri, ya jagoranci tawagarsa inda ya samu wasu yara biyar akan titin garin Mubi a ɗimauce. Anan ne, jami’an ‘yansandan suka ceto yaran da suka hada da Adamu Musa, Suleiman Idris, Suleiman Mohammed, Dauda Yahaya da Mohammed Alhassan, dukkansu mazauna garin Gwange, Maiduguri, jihar Borno. Binciken da ‘yansanda suka gudanar ya zuwa yanzu ya nuna cewa wani mai suna Aliga Suleiman na Sabon Layi, Gwange, Maiduguri ne ya ɗauko yaran daga Maiduguri ba bisa ƙa’ida ba....
Aƙalla mutum 12; ciki har da yara huɗu ne suka rasu a wani hatsarin mota da ya auku a kan babban titin Owerri zuwa Onitsha da ke Jihar Imo. Hatsarin ya auku ne lokacin da wata tankar gas mai lamba T 16716 LA, mai ɗauke da rubutun NUPENG, ta ƙwace daga kan hannunta ta afka wa wata motar fasinja. Likitoci sun bai wa gwamnati sa’o’i 24 kafin tsunduma yajin aiki Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci Motar na ɗauke da mambobin Ikklisin Jehovah’s Witness daga Jihar Anambra zuwa ƙauyen Agwa da ke Jihar Imo. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da mutuwar manyan mutane takwas da wasu yara huɗu, yayin da wasu...
Dukkanin kamfanonin sun roƙi abokan hulɗarsu da su yi haƙuri, inda suka ce injiniyoyi na aiki don gyara wutar. Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ƙoƙarin gyara wutar lantarkin yanzu haka. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ƙoƙarinta na daƙile matsalar cin zarafin yara, rundunar ’yan sandan Jihar Kebbi ta ce ta samu nasarar kama wasu mutum biyu da ake zargi da yi wa ƙananan yara fyaɗe a makon jiya. Wakilinmu ya ruwaito cewa, wata yarinya ’yar kimanin shekaru 10 da ke Unguwar Bedi a ƙaramar hukumar Zuru, ta faɗa mummunan tarkon ne a lokacin da mahaifiyarta ta aike ta karɓo saƙo. ’Yan bindiga da masu ɗaukar musu bayanai ba su da bambanci — Gwamnan Sakkwato TUC ta yi barazanar shiga yajin aiki kan ƙara harajin man fetur Bayanai sun ce wani mai suna Amos Jondo Maliki, wanda ke maƙwabtaka da su, ya kai ta ɗakinsa inda ya samu damar saduwa da ita. Haka zalika, wata...
Dakarun sojin Najeriya sun kashe wani kasurgumin dan ta’adda wanda aka fi sani da suna Kachalla Bala da yaransa biyar a Jihar Kogi. Sojojin Birget ta 12 da ke Lakwaja, hedikwatar jihar sun kuma yi nasarar ceto wasu mutanen da gungun ’yan bindigar suka yi garkuwa da su. Mukaddashin kakakin rundunar, Laftanar Hassan Abdullahi ya ce samamen da sojojin ke kaiwa a sassan jihar domin kakkabe ayyukan ’yan binidga yana samun nasara a yankunan Tunga da Aleke da Ungwan Soni da Ungwan Nyaba da kuma Ankomi. Yankin gadar Agbede–Adankoo (Mosalanci Boka) da ke yankunan Lokoja, Kabba-Bunu, da kuma Karamar Hukumar Yagba sun yi iyaka da jihohin Kwara da Neja, wanda hakan ya sa suka zama mafaka ga ayyukan ’yan bindiga....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Iyaye na ci gaba da kokawa kan yadda ilimi ke ƙara tsada yayin komawan ’ya’yansu makaranta a sabuwar shekarar karatu. Makarantu na ƙara ɓullo da sabbin hanyoyin karɓar kuɗi daga hannun yara da sunan koyarwa. NAJERIYA A YAU: Yadda ake gudanar da bukukuwar Sallar Gani yayin Mauludi DAGA LARABA: Yadda Matan Da Ke Auren Gwaji Suke Yamutsa Hazo Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da ke sa ilimi ƙara tsada yayin da yara ke komawa makaranta. Domin sauke shirin, latsa nan
Kasashe takwas, ciki har da Pakistan, Morocco, Syriya, Libya, Jordan, Lebanon da kuma Masar, sun himmatu wajen bayar da fifikon kula da cutar kansa ta yara, ta hanyar kula da ka’idojin kasa, ta hanyar yin gwajin cutar da a kan lokaci, samar da ingantattun magunguna da kuma samar da kudade don bai wa iyali kariya. Kwanan nan, Maroko ta karbi bakuncin taron bita na farko, kan kula da lafiyar yara, yayin da Lebenon kuma ta kafa kwamitin kula da cutar kansar yara, wanda ya shafi wadanda suka tsira da rayukansu, ma’aikatan jinya, sauran ma’aikata da kuma wakilan Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Kun tuna jita-jitar ake yaɗawa game wai arzikin sa ya kai Naira Tiriliyan 9? Kuma Mutane da yawa sun gaskata. A matsayin sa na gwamnan jihar Zamfara, ina da abubuwa da yawa da zan iya cewa game da Dauda Lawal, musamman da yake ina cikin makusantan sa, mai yin aiki kafaɗa da kafaɗa da shi a matsayin kakakin sa sama da shekaru biyu. A shekarun baya na yi rubuce-rubuce da dama a kan Dauda Lawal, ma’aikacin banki kuma mai taimakon al’umma. Amma, yayin da ya cika shekara 60 a yau, zan so in fitar da wasu ’yan muhimman abubuwa da Dauda Lawal ya yi a matsayin gwamna, wanda ke mayar da Jihar Zamfara daga kufai da...
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
Farashin Man Fetur Ya Fadi Kadan Sabuda Fatan Kyarar Bututun DRUZHBAC Na Kasar Rasha Farashin man fetur ya tashi a kasuwannin duniya bayan da ana saran za’a kammala gyaran bututun kwararar man fetur na kasar Rasha watu DRUZHBA wanda yake kai man fetur zuwa kasashen turai ta kasashen Slovakia da kuma Hungary. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa farashin man ya tashi a jiya laraba, amma kuma tare da wannan fatan ya sake tashi. A cikin makonnin da suka gabata ne sojojin kasar Ukraine suka kai hare-hare kan bututun man tare da amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa. Labarin ya kara da cewa tuni kamfanonin man fetur a kasashen Slovakia da kuma Hungary sun bayyana cewa...
Gwamnatin Jihar Gombe tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary International sun ƙaddamar da shirin aikin jinya domin rage mace-macen mata da yara a faɗin jihar. Shirin da aka gudanar a Ƙananan hukumomi uku da suka haɗa: Gombe da Kaltungo da Yamaltu-Deba, inda aka yi wa jama’a gwaje-gwaje, jinya da wayar da kai a unguwannin Yelenguruza da Kagarawal. An kama Ɗan sanda kan harbe soja a Bauchi Gwamnati ta kara kudin yin fasfo zuwa N100,000 da kuma N200,000 Shugaban Rotary Reproductive, Maternal and Child Health a Nijeriya, Farfesa Emmanuel Adedolapo Lufadeju, ya bayyana cewa fiye da mutum 120 aka duba a unguwar Kagarawal kaɗai, inda aka samu kashi 70 cikin 100 sun kamu da zazzaɓin cizon sauro. Ya ce, tun daga...
Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ta ceto wasu yara guda uku da aka sace tare da kama mutum uku da ake zargi da sace su. A ranar Talata, 26 ga watan Agusta, 2025, wani mutum ya kai rahoton cewa an sace ’ya’yansa uku. An kashe mutum 3 a faɗan ƙungiyoyin asiri a Legas ’Yan bindigar da suka sace ma’aurata a Katsina na neman N600m Yaran sun haɗa da Aslam Umar Lukman mai shekaru 14, Suleiman Umar Tanko mai shekaru 12 da Aliyu Umar Tanko mai shekaru 10. Waɗanda suka sace yaran sun nemi a ba su Naira miliyan 50 a matsayin kuɗin fansa. ’Yan sanda sun yi amfani da dabaru inda suka cafke shugaban ƙungiyar, Richard Philip. Yayin bincike, ya...
Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta kara hada kai da hukumomin tsaro domin dawo da zaman lafiya, tare da samar da kayayyakin agaji da tallafi ga wadanda abin ya shafa. Majiyoyin yankin sun ce al’ummar yankin sun sha fama da hare-hare akai-akai a ‘yan makonnin da suka gabata, lamarin da ya tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu. Ku tuna cewa, Gwamna Radda a ranar 18 ga Agusta, 2025 ya bar kasar don hutun makonni uku domin duba lafiyarsa a kasar waje. Gwamnan ya samu rakiyar manyan jami’an gwamnati da shugabannin hukumomin tsaro na jihar da kuma kungiyoyin bayar da agajin gaggawa ga al’umma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun...

Gwamnati Ta Fara Aikin Gyara Na’urar Watsa Shirye-shirye Mai Gajeren Zango Ta Gidan Rediyon Muryar Nijeriya
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya. A cewar sa: “Yayin da muke ɗaukar wannan babban mataki na ƙaddamar kwangilar gyara tiransimitar ‘shortwave’ ta Muryar Nijeriya mai ƙarfin kilowat 250, ya dace mu nuna ɗimbin godiyar mu ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, bisa hangen nesa da jajircewar sa wajen farfaɗo da kuma zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai na Muryar Nijeriya.” Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa wannan aikin zai sauya yanayin yadda ake yaɗa labarai a ƙasar nan. Ya ce: “Da zarar an kammala wannan aiki, na’urorin tiransimita na VON da aka...
Matasa da dama a garin Kafanchan, da ke Ƙaramar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, sun yi aikin gayya domin gyara hanyar garin. Sun yi amfani da gatari, fatanya, diga da sauran kayan aiki wajen yi wa hanyar gyara. Ɗaliba ta haɗu da ajalinta a hatsarin mota a Yobe Japan za ta bai wa Najeriya rancen $190m don inganta wutar lantarki Aikin ya haɗa da haƙa da faɗaɗa magudanan ruwa don kaucewa ambaliya da kuma hana hanyar ƙara lalacewa. Shugaban ƙungiyar Kafanchan Youth Forum, Injiniya Sa’adu Bako, ya ce sun yi aikin ne domin rage wahalar da jama’a ke sha, musamman wajen zuwa jana’iza, musamman a lokacin damina. Ya kuma yi kira ga gwamnati ta gyara hanyar, kasancewar ba maƙabarta kaɗai...
Yara 2 sun mutu wasu 6 sun jikkata bayan tashin bom a yankin Ƙofa Biyu da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno. Shaidu a garin sun shaida wa wakilinmu cewa bom ɗin ya tashi ne bayan yaran sun kawo shi gida bisa rashin sani. Sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun kawo bam ɗin cikin gari ba tare da sanin hatsarinsa ba, suna ɗauka ƙarfe ne da za a sayar. Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ce lamarin ya faru da misalin ƙarfe 5 na yamma a ranar Lahadi. ’Yan bindiga sun yi hatsari bayan karbar kudin fansa An rage kuɗin wankin koda da kashi 76% a asibitocin tarayya NAJERIYA A...
Shugaban Iran Masoud Pezeshkian na Shirin wata kai wata muhimmiyar ziyara a kasashen Armeniya da Belarus. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Asabar, mai baiwa shugaban kasar shawara Mahdi Sanaei, ya ce Pezeshkian zai bar Tehran zuwa Yerevan a ranar Litinin din nan, sannan ya wuce Minsk. Ya kara da cewa, a ziyarar ta kwanaki biyu da shugaban zai kai, yana shirin tattaunawa da manyan hukumomin Armeniya da Belarus, kan hanyoyin da za a bi wajen fadada dangantakarsu, musamman a fannin kasuwanci, da kuma sanya hannu a kan takardun yarjeniyoyi a tsakaninsu. Sanaei ya kara da cewa an shirya kai ziyara a kasashen Armenia da Belarus a karshen watan Yuni, amma aka dage. Ya...
Daga cikin wadannan alkaluman na yara miliyan 1.65 sun kasance suna a jihohin Zamfara, Bauchi, Sokoto, Borno, Kebbi, Kano, da kuma wadanda kuma suke a jihohin da Kungiyar ta MSF ke gudanar da ayyukanta kuma jihohin da ke ci gaba da fuskantar kalubalen rashin tsaro. Bugu da kari, akasarin kungiyoyi, sun yi ittifakin cewa, batun kula da lafiya, abu ne, da ya kamata matan Gwamatin uku na kasar, su bayyana dokar ta baci a kai. Wannan rashin ayyana dokar ta bacin a fannin, mussaman a Arewacun Nijeriya, za a iya cewa, babbar gazawar rashin iya gudanar da shugabanci na gari ne, inda a Katsina irin wannan sakacin, mussaman na gazar samar wa yaran abinci mai gina jiki, ya bayyana karar...
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) a ɗakin taro na Majalisar da ke Fadar Shugaban Ƙasa, Abuja. Kafin a fara taron, Shugaban Ƙasa ya rantsar da Farfesa Dakas James Dakas da Dakta Uchenna Eugene a matsayin Shugaban Hukumar Gyaran Dokoki ta Ƙasa da Kwamishina. Majalisar ta kuma dakatar da taron na minti ɗaya domin girmama marigayi Cif Audu Ogbe, wanda ya kasance memba a majalisar a lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Shehu Shagari, haka kuma a ƙarƙashin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Cif Ogbe ya rasu a ranar Asabar, 9 ga watan Agusta, yana da shekaru 78. Daga Bello Wakili
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shawarci matasan da ake ribatarsu a matsayin ’yan daban siyasa da suka tuba da su guji tashin hankali, yana tabbatar musu da shirye-shiryen gwamnatinsa na gyara tarbiyarsu tare da mayar da su cikin al’umma. Gwamnan ya yi wannan alkawari ne a taron wuni ɗaya da aka gudanar tare da shugabannin rukunan ’yan daban da suka tuba a ƙarƙashin Shirin Safe Corridor. Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya An kama mutumin da ake zargi da kashe jami’in sibil difens a Jigawa Gwamnan, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya, ya wakilta, ya ce: “Ba za a sake ɗaukar makami da sunan fadan siyasa ko wasu munanan...
Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma. Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun yan siyasa na yankin da suka rasu. Yayi bayanin cewar, za’a gina makarantun tsangayar ne a garuruwan Danzomo da Shabaru da kuma Rukutu wadanda za’a sanyawa sunan wadanda suka rasu da suka hada da marigayi Sanata Dalha Ahmad Dan Zomo da marigayi Musa Waziri Kamus da kuma marigayi Ali Ado. Haka kuma majalisar ta amince da gyaran masallatan Juma’a na Hannun Giwa da...
Fashewar gurneti ya salwantar da rayukan yara mata uku a garin Pulka da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno. A wani rahoto da ma’aikacin Sibiliyan JTF Buba Yaga ya fitar, ya ce ɗaya daga cikin ƙananna yaran suna wasa da gurnetin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, suka yi watsi da su a lokacin da gurnetin ya tashi da misalin ƙarfe 2:20 na ranar Alhamis. An garzaya da yaran zuwa Babban Asibitin Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu. Daga nan ne aka miqa gawarsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada. Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a zirin Gaza sakamakon harin bama-baman Isra’ila da kuma yunwar da ta jefa a l’ummar yankin a ciki. Kungiyar ta yi bayanin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, yaran Gaza na fuskantar kisa “sakamakon tashin bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki, yunwa, da kuma rashin muhimman kayan agaji da ayyukan kiwon lafiya. UNICEF ta jaddada cewa yara a Gaza na bukatar abinci, ruwa, magunguna, da kuma kariya. Mafi mahimmanci kuma shi ne, suna bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa.” A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, sama da mutane...
Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati. Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina dakin kwanan dalibai mai hawa daya a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, da za a kasha naira miliyan dari hudu da tamanin da bakwai. Alhaji Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta kuma amince da gyaran sashen da aka kona na gidan talabijin ta Najeriya NTA Sokoto wanda kudinsa ya kai naira miliyan dari biyu da casa’in....
Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa. Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara. Hajiya Larai Musa Lawal, ta mika sakon ta’aziyyar uwargidan shugaban kasar ga iyalan gidan sarautar tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama. Ta kuma mika sakon taya murna ga sabon sarkin, tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya mai cike da hikima da zaman lafiya da hadin kai. A nasa jawabi, sabon Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim...
Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi. An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano. Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
Amincewar Gwamnatin Tarayya da kashe Naira biliyan 712 biliyan don gyaran Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed da ke Legas ya haifar da ce-ce-ku-ce a faɗin Najeriya. Wannan gagarumin kashe kuɗi, da Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da shi a ranar Alhamis da ta gabata, ya sanya masana harkar jiragen sama, ’yan adawa, da kuma jama’ar ƙasa yin tambayoyi game da buƙatarsa, tsadarsa, da kuma inda za a samo kuɗin. Masu suka suna nuna yadda kuɗin ya yi yawa, har ya ninka kuɗin da aka ware wa Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama a kasafin kuɗin 2025 har sau goma. Hasali ma aikin ba ya cikin kasafin 2025. Wannan ya sa wasu ke kiran aikin a matsayin “almubazaranci,” musamman ganin halin...
ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa. Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan aiki na “rashin hankali”, inda ta bukaci a dakatar da shi nan take, sannan a karkatar da kudaden zuwa ayyukan da al’umma suka fi bukata, wadanda su ya kamata kowacce gwamnati ta fi ba su muhimmanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
Ma’aikatan agajin gaggawa a lardin Hebei na arewacin kasar Sin da ambaliya ta aukawa, sun karfafa kokarin gyara tituna da gadojin da suka lalace, domin tabbatar da isar da kayayyakin agaji da na aikin ceto ba tare da tangarda ba. Ruwan sama dake ci gaba da sauka a kwanakin baya-bayan nan ya haifar da ambaliya da zaftarewar kasa a fadin lardin, lamarin da ya rutsa da gundumomi da dama. Zuwa safiyar jiya Asabar, an dawo da zirga-zirga a sassan tituna 961 dake fadin lardin Hebei. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
Asusun kula da Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, ya ce Najeriya ce ƙasa ta biyu da aka fi samun ɓullar cutar kwalara a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka. Darektan Hukumar UNICEF mai kula da yammacin Afirka da Afirka ta tsakiya, Gilles Fagninou ne ya bayyana hakan tare da cewar annobar kwalara ta zama tamfar alaƙaƙai a Najeriya. Haɗarin tirela ya yi sanadin asarar awaki sama da 100 a Zariya Martani: Har yanzu muna ci gaba da yajin aiki — Ma’aikatan jinya “A cewarsa cutar Kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Najeriya, inda ƙasar ke fama da ɓarkewar cutar a ‘yan shekarun nan.” “Ya zuwa ƙarshen watan Yuni, Najeriya ta samu adadin mutane 3,109 da ake zargin...
A wani yunkuri na yaki da rashin abinci mai gina jiki da kuma karfafa tattalin arzikin mata a jihar Jigawa, Gwamna Umar Namadi ya jagoranci bikin yaye mata 600 da suka samu horo kan yadda ake sarrafa abincin yara mai gina jiki daga kayayyakin da ake samarwa a gida, wanda aka fi sani da “Tom Brown”. Malam Umar Namadi ya bayyana wannan shiri a matsayin wata dabara ta cikin gida da aka kirkira domin shawo kan matsalolin rashin abinci mai gina jiki a tsakanin yara, da kuma karfafa tattalin arzikin mata. “Muna matukar godewa Allah da ya ba mu hikima da basira don kirkirar wannan tsari wanda zai taimaka mana mu cimma manufofi da dama a lokaci guda.” In ji...
A wani gagarumin ci gaba na inganta walwala da ci gaban yara da matasa wadanda suka isa makaranta, Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Farko ta Jihar Nasarawa NSUBEB, Dokta Kasim Mohammed Kasim ya karbi tawagar Kids & Teens Resource Center K&TRC a wani taron bayar da shawarwari da aka mayar da hankali kan shirin Ilimi don Lafiya da walwala, wanda UNESCO ke tallafawa. An gudanar da babban taron ne a hedkwatar Hukumar NSUBEB, inda ya samu halartar kwamishinonin hukumar su uku, da Daraktoci da dama, da kuma tawagar K&TRC karkashin jagorancin wanda ya kafa kuma Shugaba, Mista Martin-Mary Falana. Tattaunawar a yayin zaman ta tabo batutuwan da suka shafi rayuwar yara da matasa a jihar, wadanda suka hada...
Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala gyaran makarantu fiye da 1,200 a kananan hukumomi 44 na jihar a wani yunkuri na farfado da harkar ilimi. Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Ali Haruna Makoda, ne ya bayyana hakan yayin taron bitar yini guda kan kara kaimi a tsarin duba ingancin karatu, da aka gudanar a dakin taro na Cibiyar Kula da Ilimin Al’umma (CERC). Ya ce banda gyaran manyan makarantu, gwamnatin ta ware Naira miliyan 484 domin gudanar da karin ayyukan gyare-gyare a gundumomi 484, inda kansilolin mazabu ke kula da gudanarwar ayyukan. “A karo na farko a tarihin Kano ake aiwatar da manyan ayyukan ilimi a wannan mataki. Mun riga mun gyara makarantu sama da 1,200 kuma an...
Wani rahoto daga ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa wato Medecins Sans Frontiere na nuni da cewa sama da yara 650 ne suka mutu bayan fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki a Jihar Katsina. Medicins Sans Frontiere wadda ta fara aiki a Katsina tun shekarar 2021, ta ce ta samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki da aka isar da su zuwa cibiyoyin kula da marasa lafiya da ƙungiyar ke da su a yankin. Za mu ba da damar shigar da kayan agaji a Gaza — Isra’ila Super Falcons ta lashe gasar WAFCON karo na 10 bayan doke Maroko A cewarta, a tsakanin Janairu da Yuni 2025 ta yi jinyar kusan yara 70,000 da ke...
Amfani da man kwakwa da man Amla: Daga farko ki dora man kwakwa a wuta sannan sai ki zuba masa man Amla. Daga nan sai ki gauraya sosai, idan kin tabbata sun gaurayu, sai ki sauke daga wuta, har hadin ya huce. Sannan ki zuba man a kwalba kina shafa wannan hadin a fatar kanki da gashinki kamar sau uku a sati. Amfani da Lemon Tsami: Ki samu ruwan Lemun Tsami, sai ki hada shi da kwai da kuma man Amla. Sai ki shafa hadin a fatar kai da kuma gashi. Ki bar hadin a kanki har tsawon minti talatin, sannan ki wanke da ruwan Dumi. Za ki iya yin wannan hadin sau biyu a wata. Amfani da Alo Bera:...
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibril, ya kaddamar da zaman jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya a Kano. Yayin gabatar da jawabinsa na bude taron, Sanata Barau ya yi maraba da manyan baki da suka halarci zaman, yana mai cewa: “Ina alfahari da zuwanku wannan zama na jin ra’ayoyin jama’a na yankin Arewa maso Yamma, wanda ya shafi kudurori da sabbin batutuwa dangane da gyaran kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya.” Sanata Barau ya tunatar da cewa Majalisar Ƙasa ta riga ta amince da gyaran kundin tsarin mulki sau biyar, da aka fi sani da alteration acts na farko zuwa na biyar. Ya jaddada cewa akwai muhimman batutuwa da ke buƙatar ƙarin...
Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce sake gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 dole ne, ya taimaka wajen haɗa kan ƙasa, kyautata mulki, da bunƙasa tattalin arziƙi. Ya buƙaci a gudanar da wannan aiki cikin adalci, gaskiya da kuma bisa ra’ayoyin jama’a gaba ɗaya. HOTUNA: Shugaban Gambiya ya kai wa iyalan Buhari ziyarar ta’aziyya a Daura Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Gwamna Abba, ya bayyana haka ne ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Sulaiman Wali. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake gabatar da saƙon maraba da baƙi a wajen Taron Sauraron Ra’ayoyin Jama’a na Yankin Arewa maso Yamma kan sake gyaran kundin tsarin mulki, da aka gudanar a Kano ranar Asabar....
Wasu yankuna a Jihar Legas, na iya fuskantar rashin wuta na tsawon kwanaki 25, yayin da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), zai fara gyaran layin lantarkin Omotosho zuwa Ikeja ta Yamma mai ƙarfin 330kV. A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, 25 ga watan Yuli, aikin zai gudana kowace rana daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma, kuma za a kammala aikin a ranar Alhamis, 21 ga watan Agustan 2025. Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar Ta’addanci: Alƙawuran sojoji 8 na kamo Bello Turji Kamfanin, ya bayyana cewa gyaran zai shafi raba wutar lantarki a wasu wurare, kuma hakan na iya janyo ɗaukewar wuta. Sanarwar ta ce: “Abokan...
A daidai lokacin da aka cika kwanaki 659 daga fara kisan kiyashin Gaza, sojojin Sahayoniya suna ci gaba da killace yankin da hana shigar da abinci da magani. Ma’aiktar kiwon lafiya ta Gaza ta sanar da cewa ya zuwa wannan lokacin jumillar wadanda yunwa ta kashe sun kai 122 daga cikinsu da akwai kananan yara 83. Da jijjifin safiyar yau Asabar, majiyar asibitin “Nasr’ ta sanar da cewa wata jaririya ta yi shahada saboda rashin abinci mai gina jiki. Haka nan kuma ta ce, jaririyar ‘yar watanni 6 da haihuwa ta yi shahada ne saboda rashin abinci mai gina jiki da kuma magani saboda takunkumin da HKI ta kakabawa yankin na Gaza. Babban jami’iin gudanarwa na ma’aikatar kiwon lafiya a...
Aƙalla mutum 14; ciki har da mata da ƙananan yara ƙanana ne, suka rasu a wani sabon hari da aka kai a Jihar Filato. Harin ya faru ne da yammacin ranar Alhamis a Gundumar Mangor da ke Ƙaramar Hukumar Bokkos. Sarkin Katsinan Gusau ya rasu Yadda aka mayar da yaran da aka sace a Kano masu wanke-wanke a Kudu Waɗanda aka kashe suna kan hanyarsu ta dawowa daga kasuwar mako-mako da ke garin Bokkos, lokacin da wasu ’yan bindiga suka buɗe musu wuta. Wannan hari na zuwa ne wata guda bayan wani hari da aka kai wa wasu ‘yan ɗaurin aure daga Zariya a Jihar Filato, inda aka kashe su. Ƙungiyar Bokkos Cultural Development Forum (BCDF), ta tabbatar da faruwar...

Hukumar Ba Da Agajin Jin Kai Ta ‘Yan Gudun Hijirar Falasdinawa Ta “UNRWA” Ta Sanar Da Kashe Ma’aikatan 330 A Gaza
Hukumar ba da agaji da kula da ‘yan gudun hijirar Falasdinawa ta “UNRWA” tana karkashin wuta sakamakon ma’aikatan 330 da suka yi shahada kuma aka lalata cibiyoyinta 300 a Gaza! Inas Hamdan, mai magana da yawun hukumar ta UNRWA a birnin Alkahira, ta tabbatar da cewa; Yunwar da ke faruwa a zirin Gaza, wani bala’i ne da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya shafi mutane sama da miliyan biyu, ciki har da akalla yara miliyan daya. Wannan ya saba wa duk dokokin jin kai da ka’idoji, kuma abin takaici, lamarin yana da kara muni. Hamdan ta yi nuni da cewa, a lokacin da suke magana kan matsalar agajin jin kai ko shigar da kayan abinci zuwa zirin Gaza,...
Aisha Muhammad Abdullahi ’yar shekaru 7 ba ta da masaniyar irin hadarin da ke gaba yayin da mahaifiyarta ta aike ta ta sayo sinadarin hada lemon zoborodo amma ta manta ba ta sayo kankara ba wanda hakan ya sa ta juya. A daidai wannan lokacin ne wata mace wacce ke bin ta a baya ta kirayi Aisha ta kuma ba ta alewa sannan ta bukaci ta bi ta. Abin da Aisha za ta iya tunawa kawai shi ne ta farka daga barci ta ganta a garin Onitsha na Jihar Anambra a hannun wata mace mai suna Ebere. Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso An rantsar da Nentawe sabon shugaban APC na ƙasa Aisha na...
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Bauchi ta ce ta kama wata budurwa ‘yar shekara 19 mai suna Esther Gambo bisa zargin sace yara da yin garkuwa da su sannan ta kashe su. Rundunar ta ce wadannan kananan yara biyu mata ne ‘yan shekara bakwai, lamarin da ya jawo tarzoma da kona coci. Kakakin Rundunar, CSP Mohammed Ahmed Wakil ya shaida wa manema labarai haka a Bauchi ranar Alhamis. NAJERIYA A YAU: Yadda masu yi wa kasa hidima za su ci arzikin yankunan da suke aiki Tinubu ya fi mayar da hankali wajen gina Kudancin Nijeriya — Kwankwaso Wakil Ya bayyana cewa an samu rahoton faruwar lamarin ne a ranar 22 ga watan Yulin 2025, da misalin karfe 3:00 na rana. Ya...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya nuna damuwa kan halin da yara ke ciki a jihar Kano, yana mai kira ga gwamnatin jihar da ta ƙara zuba jari a fannin lafiya, ilimi, da abinci mai gina jiki ta hanyar kasafin kuɗi da ya danganci makomar yara. Shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Muhammad Farah, ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da ‘yan jarida kan kasafin kuɗi mai la’akari da bukatun yara, inda ya gabatar da wasu alkalumma masu tayar da hankali dangane da rayuwar yara a jihar. Farah ya ce jihar Kano na da yara fiye da miliyan 6 da rabi da ke ƙasa da shekaru 18, wadanda da dama daga cikinsu na...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A duk lokacin da aka ce an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abubuwa na daban da kuma ba su damar shakuwa da ’yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata a ce ana ware wa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. NAJERIYA A YAU: Yadda tsadar taki ke hana noman masara da shinkafa DAGA LARABA: Makomar Siyasar Najeriya Bayan Rasuwar Shugaba Buhari Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin...
Gwamna Bala Muhammad ya ƙaddamar da aikin gyare-gyare da sabunta ginin Majalisar Dokokin Bauchi kan kuɗin da ya haura Naira biliyan bakwai, wanda ya haɗa da inganta kayan aiki, ofisoshi, da kuma gina sabon ofishin hukumar kula da harkokin majalisa. A yayin ƙaddamarwar da aka gudanar ranar Talata, Gwamna Bala ya bayyana cewa wannan gyara na cikin shirin gwamnatinsa na sauya fasalin birane da samar da muhalli mai kyau ga ma’aikata domin sauƙaƙa aikinsu. Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu karɓo rancen $21bn a ƙetare UNICEF na zargin Gwamnatin Nijeriya da cin zarafin ƙananan yara Ya ƙara da cewa tuni aka riga aka biya rabin kuɗin aikin domin tabbatar da cewa aikin ya kammala a kan lokaci. Kwamishinan gidaje da...
Asusun kula da ƙananan yana na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF, ya ce ya wani sabon bincike da ya gudanar ya banƙado yadda cin zarafin ƙananan yara da kuma kulle su ba bisa ƙa’ida ba ke ci gaba da bazuwa a Nijeriya. A cikin rahoton da ya fitar ranar Litinin, UNICEF ya ce har yanzu akwai dubban ƙananan yara da gwamnati ta rufe su ba kuma tare da cikakken bayani ga iyalansu ba, wasu ma a yanzu babu cikakken bayani kan inda suke ko kuma halin da suke ciki. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 151 a Nijeriya bana — NCDC Jami’an tsaro sun dakile yunkurin Sanata Natasha na shiga harabar Majalisa Asusun ya ce a Nijeriya rufe ƙananan yara tare da...
Gwamnatin Jihar Kano ta kara zage damtse wajen farfado da mata masu shaye-shayen miyagun kwayoyi ta hanyar mayar da Cibiyar Gyaran Matan Gaya, wadda a da ya kasance gidan marayu, zuwa wurin gyaran tarbiya. Kwamishiniyar harkokin mata, yara da masu bukata ta musamman, Hajiya Amina Abdullahi Sani, ta jagoranci wata babbar tawaga zuwa cibiyar da ke Gaya domin tantance bukatun gyare-gyare da kuma hada kai da ma’aikatu domin gudanar da aikin. Tawagar ta hada da kwamishinan ayyuka Engr. Marwan Ahmad Badawi, tawagarsa ta fasaha, daraktoci, da mataimaka daga ma’aikatar harkokin mata. A yayin ziyarar, kwamishinar ta bayyana wa takwararta na ma’aikatar ayyuka irin ayyukan da ake bukata domin inganta cibiyar, da suka hada da gyare-gyare da fadada...
Hukumar bayar da agajin gaggawa a Gaza ta ce aƙalla mutum 10, ciki har da ƙananan yara guda shida ne suka rasu a sanadiyar harin da Isra’ila ta kai ta sama a Gaza a safiyar Lahadi. An kai gawarwakin waɗanda suka rasu zuwa asibitin Nuseirat’s al-Awda, inda wani likita ya ƙara da cewa sun yi jinyar wasu mutum 16, ciki har da ƙananan yara guda bakwai. Wani ganau ya ce jirgi mara matuƙi ne ya harba makami mai linzami a kan dandazon mutanen da suka yi layi riƙe da jarkunansu domin ɗibar ruwa daga wata tankar ruwa a sansanin ƴangudun hijira na al-Nuseirat. Har zuwa haɗa wannan rahoton, rundunar tsaron Isra’ila ba ta ce komai ba kan batun. Wani faifan...
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya gabatar da matsayar Jihar Kaduna a zaman jin ra’ayin jama’a dangane da gyaran kundin tsarin mulkin shekarar 1999. An gudanar da taron ne a gidan Gwamnati na General Hassan Katsina da ke Kawo, a garin Kaduna, a matsayin wani bangare na ci gaba da shirin gyaran kundin tsarin mulki da Majalisar Wakilai ta kasa ke jagoranta. Wannan zaman jin ra’ayi da aka ware a matsayin Cibiyar ta daya, ya hada da jihohin Kaduna, Kano, Katsina da Jigawa. Taron ya tara shugabanni daga fannoni daban-daban ciki har da ’yan siyasa, da sarakuna da kuma wakilan kungiyoyin fararen hula, domin tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen kundin tsarin mulki. ...
Yadda ake hadawa: Da farko za ki gyara shinkafarki ki wanke ta ki tsane ta sai ki bar ta ta dan bushe, sannan a barzo miki ita a inji sai ki ajiye a gefe. Sai ki wanke namanki ki dora a wuta ki sa maggi, da gishiri da tafarnuwa da citta da albasa. Sannan sai ki zo ki tankade wannan shinkafar da kika barzo ta saboda da tsakin ake amfani. Sai ki sa ruwa ki wanke tsakin ki tsane shi, sai ki zuba shi a madambaci ki dora a wuta. Sai kuma ki gyara zogalenki, ki wanke, ki hada da tsakin sai ki rufe. Ki tsame namanki, ki yanka kayan miyanki ko ki jajjaga duk daya ne ki ajiye a...
Gwamnatin ta ce ba za ta lamunci cin zarafi da amfani da iko ba da gangan wajen cutar da waɗanda ke cikin irin wannan cibiya ba. Domin rage wa matashin raɗaɗi ta tallafa masa, gwamnatin jihar ta ba shi Naira dubu dari tara da saba’in (₦970,000) don yin magani, da kuma Naira miliyan 3.5 (₦3,500,000) domin sayen hannun roba da zai taimaka masa wajen yin rayuwa. Gwamnan ya kuma amince da shirin sake fasalin cibiyar ta Babbar Ruga domin inganta ta da kuma hana irin wannan abu faruwa a nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
Kakakin Brigade ya bayyana cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen magance duk wani yunkuri na sojojin Nijeriya wajen aikata aikin da bai dace ba, tare da tabbatar da da’a, da bin doka da oda. Ya yi nuni da cewa ba za a iya jure duk wani nau’i na rashin da’a a tsakanin ma’aikatanta ba. Ya kuma ba jama’a tabbacin cewa sakamakon binciken zai fito fili domin tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma adalci. Rundunar ta kuma bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, su guji yada jita-jita, ko kuma shiga ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, tare da yin alkawarin tabbatar da martabarta da kuma bautar kasa. A halin...
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), ya ce ya fara tunanin yiwuwar sayar da matatun man ƙasar nan. Shugaban kamfanin, Bayo Ojulari ne, ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da Bloomberg. Dalilin da ya sa muka gayyaci Sheikh Lawal Triumph – ’Yan sanda Ya kamata mulkin Najeriya ya ci gaba da zama a hannun ’yan Kudu — Hannatu Musawa Ya ce yanzu haka kamfanin yana sake duba yadda ake gudanar da matatun, kuma ana sa ran kammala wannan nazari kafin ƙarshen shekara. Da yake magana a taron OPEC karo na tara da aka yi a Birnin Vienna, na ƙasar Austria, Ojulari ya ce gyaran tsofaffin matatun gwamnati ya wuce yadda ake tsammani. Najeriya na da matatu huɗu;...
Rundunar ’yan sandan Jihar Filato a ranar Alhamis ta gurfanar da wasu mutane 22 da ake zargi da kashe matafiya bikin aure da a unguwar Mangun da ke Ƙaramar hukumar Mangu ta Jihar Filato. An kashe mutum 13 daga cikin matafiyan, yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa unguwar Qua da ke ƙaramar hukumar Qua’an Pan ta Jihar Filato. ’Yan sanda sun ƙaddamar da sabon samame, sun kama mutum 98 a Kano Jami’ar Tarayya ta Gashuwa za ta ba matar Tinubu digirin girmamawa Adadin waɗanda aka kashe mutum 32 da suka haɗa da maza da mata da ƙananan yara suna cikin...
Jakadan Amurka na musamman a yankin yammacin Asiya Steven Witkoff ya bayyana cewa yana fatan HKI da kuma kungiyar Hamas zasu cimma yarjeniyar tsagaita budewa juna wuta a karshen wannan makon. Jakadan ya kara da cewa idan har yarjeniyar ta tabbata, kungiyar Hamas zata mikawa HKI yahudawa masu rai 10 da kuma gawakinn wasu 09 . Steven Witkoff bai bayyana abinta ita Hamas da kuma sauran Falasdinawa zasu samu a wannan yarjeniyar na kwanaki 60 ba. Musamman bayan ta rasha falasdinawa kimani 57500 ya cikin watanni kimani 21 yahudawan suna fafatawa da ita ba. Har’ila yau falasdinawa 150,000 suka ji rauni mafi yawansu mara da yara. A cikin wadanda aka kashe akwai yara kimani 12, 000 Daga karshe Witkoff, yace...
Kananan yara uku sun rasu yayin da wasu da shidan ke kwance a asibiti sakamakon sake bullar cutar nan ta mashako a garin Zariya da ke Jihar Kaduna. Wani mazaunin unguwar Kwarbai a yankin na Zariya, Mallam Bashir Magaji wanda ya rasa ’yarsa sakamakon barkewar cutar wadda a turance ake kira Diphtheria, ya bayyana yadda take bazuwa cikin sauri a kwanakin nan. Kira ga Haƙuri: A Dakatar da Ƙirƙirar Sabbin Masarautu a Jihar Bauchi Amurka za ta ɗauki nauyin ’yan tawaye domin yaƙi da ta’addanci A cewarsa, ’yarsa da ta nuna alamun kamuwa da cutar na kumburin wuya da sarkewar numfashi, an gaggauta mika ta Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, amma daga bisani ta ce ga...
Hukumar Gyaran Hali ta Najeriya reshen jihar Kano, ta bayyana cewa Fursunoni 58 suna rubuta Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa NECO ta shekarar 2025. Wannan ci gaba ya samu ne bayan biyan kudin rajista da gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi. Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Kofar-Nasarawa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai a Kano. Ya ce wannan karamci na gwamnatin jihar Kano shaida ce ta jajircewarta wajen kula da walwalar fursunoni, gyaran dabi’unsu da kuma dawo da su cikin al’umma yadda ya kamata. “Biyan kudin rajistar jarrabawa da gwamnatin Kano ta yi alama ce ta jajircewarta wajen samar da dama ga fursunoni domin su...
Wani malamin addinin musulunci a jihar Zamfara, Sheikh Mohammed Tukur Sani Jangebe, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Zamfara da su gaggauta gudanar da kananan gyare-gyare daga mahadar Maru –Mayanchi – Maradun, da ke kan hanyar zuwa wani yanki na karamar hukumar Talata Mafara. Ya ce mummunan yanayin hanyar yana ci gaba da haifar da babban kalubale ga matafiya tare da fallasa su ga hare-haren ‘yan bindiga a kan hanyar. Sheikh Jangebe ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zantawa da wakilin gidan rediyon Najeriya a Gusau babban birnin jihar Zamfara. Ya bayyana cewa babbar hanyar Maru zuwa Talata Mafara ta samar da ramuka sama da dari, wadanda ke hana zirga-zirgar ababen...
Hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC) a jihar Kano ta ce ta samu rahoton laifuka 351 na take hakkin yara daga cikin jimillar kararraki 446 da ta samu daga watan Afrilu zuwa Yuni 2025. Kodinetan NHRC na jihar Kano Alhaji Shehu Abdullahi ne ya bayyana haka a Kano. Ya bayyana cewa daga cikin jimillar korafe-korafe 446 da aka samu a cikin watanni uku 351 na da alaka da take hakkin yara. Ko’odinetan jihar ya yi nuni da cewa, sauran shari’o’in sun hada da tashin hankalin gida 19, 18 da suka shafi ‘yancin tattalin arziki da zamantakewa, da kuma biyar da suka shafi ‘yancin rayuwa. “cikin zarge zargen har na Maita da sauran shari’o’in da...
Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu. A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Taron Ashura Ya Zama Lamari Mafi Girma Da Cinkoson Jama’a, Inda Masu Ziyara Daga Sassan Duniya Suka Isa Karbala
Gangamin Ashura ya zama lamarin mafi girma da cunkoson jama’a inda tattakiin Tuwairij yake gudana tare da faɗaɗa da ba a taɓa ganin irinsa ba Tattakin Tuwairij na bana zuwa birnin Karbala na fuskantar hallara da cunkoson jama’a da ba a taba ganin irinsa ba, inda dimbin masu ziyara daga sassan duniya ke tururuwa zuwa hubbaren Imam Husaini da kuma titunan da ke kewaye. Mai ba da shawara ga babban sakataren cibiyar Hubbaren Imam Husain {a.s} Fadel Oz a cikin wata sanarwa da ya aikewa kafafen watsa labarai ya bayyana cewa: “A shirye-shiryen wannan juyayi, babban Sakatariyar Haramin Imam Husain (a.s) da haramin Abbas sun samar da dukkan sharuddan da suka dace don kula da masu ziyara da kuma tabbatar...
Hukumomi a Jihar Texas ta Amurka sun ce gomman mutane sun riga mu gidan gaskiya ciki har da kananan yara sakamakon wata mummunar ambaliyar ruwa a ranar Asabar. Sai dai ya zuwa yau Lahadi, adadin wadanda suka mutu sun kai 50 ciki har da kananan yara 15 yayin da ake ci gaba da aikin ceto wadanda lamarin ya rutsa da su kamar yadda wani babban jami’in dan sanda na yankin, Larry Leitha ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP. An kama ɗan Najeriya yana taimaka wa Rasha a yaƙinta da Ukraine Sojoji sun kashe ’yan ta’adda 41 a Nijar Tuni dai Shugaba Donald Trump ya sanar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa wajen kai dauki yankin na...
Idan ko tana wannan kazar-kazar din to dukkanin jikinta budewa yake yi. Don haka idan budurwa ta yi aure kuma ta kasance mai irin wannan dabi’a shi ne sai ki ga an sami matsala da miji yana zarginta da ko tana yawon banza tun da bai same ta a matsayin wacce ba ta taba aure ba. Nan kuwa ba haka bane, yawan tsalle-tsalle ne ya jawo a yayin al’ada. Idan kuma matar aure ce to sai ka ga jikinta ya sake budewa, idan ta gama al’ada ta koma turaka sai ki samu maigida bai damu da ya rika waiwayarta ba saboda a madadin jikinta ya matse a a sai ma ya kara budewa da yayi. Don haka idan har kina...
“A kowane mako, muna karbar yara fiye da 100 da ke fama da cutar maleriya. Sannan kuma, mafi yawancin lokaci; ba a kawo su asibiti, sai cutar ta tsananta”, in ji likitan. – Ciwon ciki da amai da gudawa (kwalera): Lokacin damina na kawo yawan samun gurbataccen ruwa, wanda ke haddasa cututtuka kamar ciwon ciki, amai da gudawa da kuma zazzabin taifod. Wannan na yawan shafar yara, musamman ‘yan kasa da shekara biyar. Dakta Ahmad ya kara da cewa, “Yara na da rauni a garkuwar jikinsu, sannan kuma idan suka kamu da gudawa, jikin nasu na rasa ruwa cikin sauri, har ta kai ga samun mace-mace.” -Kaikayi da kurajen fata: Likitan ya ce, lokacin damina na matukar kawo danshi,...
Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Jihar Gombe (SEMA) ta bayyana cewa, ambaliya da iska mai ƙarfi sun rushe da lalata gidaje 171 a yankunan jihar cikin watanni biyu da suka gabata, lamarin da ya haddasa asara da kuma mutuwar yara huɗu. Sakataren zartarwa na Hukumar SEMA, Malam Abdullahi Haruna Abdullahi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gombe, inda ya ce iftila’in ya shafi ƙananan hukumomin Dukku da Kwami da Gombe da Akko. Harin Filato: Remi Tinubu ta ba da gudummawar Naira biliya 1 Buhari ba ya cikin mawuyacin hali — Bashir Ahmad “Mun samu rahoton rushewar gidaje 87 a Dukku, 27 a Kwami, 30 a Gombe da kuma 27 a Akko, ciki...
Bisa ga sanarwar, wannan wani sashe ne na sabon yunkuri na ba da cikakken ‘yanci ga majalisar kananan hukumomi 774 na kasar nan. Haka kuma a kan gyaran kananan hukumomi, wata kudirin doka da ke neman kirkiro wata hukumar zabe mai zaman kanta ta kananan hukumomi (NALGEC), wanda za ta dunga shiryawa, gudanar da kuma kula da zaben kananan hukumomin, za a kuma gabatar da ita ga ‘yan Nijeriya don yin nazari a taron sauraron jin ra’ayoyin. Wadansu batutuwa da aka fitar a cikin sanarwar da suka hada da kudirin dokoki guda biyu kan tsaro da manufar samar da ‘yansandan jihohi da majalisar tsaro na jihohi don tsara manufofin tsaro na cikin gida a matakin yankuna. “A bangaren gyaran manufifin...