Gwamna Yusuf Ya Amince Da Korar Wasu Mataimaka Biyu Bisa Hannu Akan Belin Wani Dilan Miyagun Kwayoyi
Published: 10th, August 2025 GMT
Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar.
A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin wani mai hatsarin gaske kuma dilan kwyaan maye, Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar kwamitin da ya gabatar a gaban kwamitin.
A cewar wata wasika da ya fitar a ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta 2025, ta hannun sakataren gwamnatin jihar (SSG), Sharada an umurce shi da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa ga babban sakatare, bincike, ranar Litinin, 11 ga Agusta 2025.
An kuma gargade shi da kada ya nuna kansa a matsayin jami’in gwamnati a wannan gwamnati mai ci.
Hakazalika, gwamnan ya sauke Tasiu Adamu Al’amin Roba, babban mataimaki na musamman, daga mukaminsa bayan kama shi da laifin sama da fadi da wasu buhunan hatsi a wani dakin ajiyar kaya da ke Sharada a shekarar 2024.
Tuni dai Roba ya gurfana a gaban kotu inda ake tuhumarsa da laifin sata da hada baki a kan zargin karkatar da kadarorin jama’a.
Haka kuma an umurci Tasiu Adamu Al’amin Roba da ya mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannun sa da suka hada da katin shaida a ranar Litinin ko kuma kafin ranar Litinin 11 ga watan Agusta 2025. Ya kuma yi gargadin kada ya bayyana kansa a matsayin ma’aikacin gwamnati a wannan gwamnati mai ci.
A wani labarin kuma, gwamnatin jihar ta wanke Hon. Musa Ado Tsamiya, mai ba shi shawara na musamman kan magudanun ruwa, wanda kwamitin bincike ya wanke shi daga dukkan zarge-zargen, inda ya tabbatar da cewa ba shi da laifi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na tabbatar da adalci da kuma rashin hakuri da cin hanci da rashawa, yana mai gargadin dukkanin jami’an gwamnati da su kasance masu bin ka’ida mai inganci a ayyukansu da kuma rayuwarsu ta sirri.
A cikin wannan sanarwa, ana shawartar jama’a da kada su yi wata hulda da wadannan ‘yan siyasa biyu da aka kora a kan duk wani batu da ya shafi gwamnatin jihar Kano, duk wanda ya yi haka, ya yi ne a kan kansa.
Saki/Abdullahi jalaluddeen/Kano
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: siyasa gwamnatin jihar
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ekiti, Joseph Eribo, ya tabbatar da ƙwato jaririn da aka sace a wani asibiti da ke Ado-Ekiti ranar Litinin.
An miƙa jaririn ga iyayensa, Mustapha Aliyu mai shekara 29 da kuma Salmatu Lawal mai shekara 22, bayan da jami’an ’yan sanda suka tsananta binciken lamarin.
An kashe matafiya biyu da yin garkuwa da uku a Kwara ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a BornoA cewar Eribo, an samu nasarar ne bayan samun wani sahihin daga wani da ya ba da rahoto ya tuntuɓi wani babban jami’in ‘yan sanda, inda ya nuna shakku kan wata mata da ta yi imanin cewa tana da alaƙa da sace jaririyar da ta ji a cikin labarai.
Binciken da aka yi ya sa jami’an ’yan sanda suka kai gano wata jaka da aka bari a asibiti. Jakar na ƙunshe da ƙullin auduga da kuma takardar shaida daga wani babban kanti.
Hotunan na’urar CCTV daga babban kanti ya nuna wata mata da wasu gungun maza, inda suka taimaka wa ’yan sanda wajen ganowa tare da kama wacce ake zargin.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa, wanda ake zargin ta yi ƙaryar tana da juna biyu kuma ta yi kamar tana jiran haihuwa a asibiti. Ta yi amfani da damar da ta samu ta sace jaririn a lokacin da mahaifiyar jaririn ta ɗan tashi daga wajen.
Da take magana da manema labarai, wanda ake zargin Miss Deborah Ayeni, ta amsa laifin da ake zargin ta aikata. Ta ce, ta yi ɓarin cikinta ne a watan Maris kuma tana tsoron mijin nata da ke zaune a Birtaniya zai iya barinta, lamarin da ya sa ta sace jaririn. Ta yarda ta kwana a asibiti tare da ƙulla alaƙa da jaririn kafin ta sace shi.
Mahaifin jaririn, Mustapha Aliyu ya bayyana godiyarsa ga Allah da aka mayar masa da jaririn nasa lafiya, ya kuma yaba wa ’yan sanda bisa gaggawar ɗaukar matakin da suka ɗauka da kuma ƙwazon aiki.