Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu
Published: 8th, August 2025 GMT
Shugaban Sin Ya Aike Da Sakon Ta’aziyya Ga Takwaransa Na Rasha Sakamakon Hadarin Jirgin Saman Fasinja Da Ya Auku A Kasar An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara
A cewar Goɓspend, an kashe maƙudan kuɗaɗe a ƙarƙashin mulkin Shugaba Tinubu a tsakanin Afrilu da Agusta 2024 wajen kula da jiragen saman shugaban ƙasa.
Farkon kashe kuɗaɗen a ranar 14 ga Yulin 2023, lokacin da aka biya naira miliyan 846.03 a matsayin kuɗaɗen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa na wucin gadi. Kwanaki biyu daga bisani, an sake kashe naira miliyan 674.82. A wannan watan kaɗai, jirgin ya laƙume sama da naira biliyan 1.5.
A watan Agusta, kashe kuɗaɗen sun ƙaru. An kashe naira biliyan 2 a ranar 16 ga Agusta, kuma an rubuta ƙarin kuɗaɗe na naira miliyan 387.6 da naira miliyan 713.22 a wannan watan. A cikin zangon ƙarshe na shekara ta 2023, an kashe naira biliyan 1.26 a watan Nuwamba.
Shekarar 2024 ma ta fara ne da ƙarin kashe kuɗaɗe masu yawa. A watan Maris kaɗai, an kashe kuɗaɗe har sau biyu na naira biliyan 1.27 kowanne a ranar 7 da 9 na wannan watan. Wannan ya biyo bayan nai-ra biliyan 5.08 a ranar 23 ga Afrilu, wanda shi ne mafi girma a cikin kashe kuɗaɗe a watanni 18 da aka gudanar da binciken.
A ranar 8 ga Mayu da 11 ga Mayu, an kashe naira biliyan 2.43 da naira biliyan 1.27 a jere, tare da wani ƙarin naira biliyan 1.27 da aka aike a ranar 25 ga Mayu. A ranar 5 ga Agusta, gwamnatin ta baya naira biliyan 1.25 da naira biliyan 2.21, sannan a ranar 6 ga Agusta, naira miliyan 902.9 da naira biliyan 1.24 aka kashe. Jimlar dukkanin abin da aka kashe a watan Agusta ya kai sama da naira biliyan 5.6.
Biyan kuɗin ya ci gaba har zuwa ƙarshen kwata na hudu na 2024, duk da haka a cikin ƙarancin adadi. Waɗanda sunka haɗa da naira miliyan 160.4, a ranar 8 ga Agusta, naira miliyan 35, a ranar 11 ga Sa-tumba, naira milian 133, a ranar 29 ga Satumba, da jerin biyan kuɗaɗe masu ƙaranci a Disamba, ciki har da na naira miliyan 290 da naira miliyan 102.95 da naira miliyan 25.25 da naira miliyan 8.7.
Jirgin saman shugaban ƙasa, wanda rundunar sojin saman Nijeriya ke kula da shi, ana amfani da shi ne wajen yin sufuri na sama na shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa da manyan jami’an gwamna-ti. Duk da cewa yana da matuƙar muhimmanci, amma kuɗaɗen da ake kashewa wajen kulawa da jirgin ya kasance batun da ake tattaunawa da sukan lamarin, musamman ma a cikin yanayin matsalolin kuɗi da Nijeriya kef ama da shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: da naira miliyan da naira biliyan naira biliyan 1 kashe kuɗaɗe kashe naira
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Kula Da Wutar Lantarki Ta Kasa
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Injiniya Abdullahi Garba Ramat a matsayin sabon Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa (CEO) na Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC). Haka kuma, ya naɗa Abubakar Yusuf a matsayin Kwamishinan Harkokin Abokan Hulɗa, da Dr. Fouad Olayinka Animashun a matsayin Kwamishinan Kudi da Harkokin Gudanarwa.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara ta Musamman kan Harkokin Watsa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya sanya wa hannu, shugaban ƙasar ya bukaci waɗanda aka naɗa su yi amfani da ƙwarewarsu wajen tabbatar da burin gwamnatinsa a fannin wutar lantarki.
Onanuga ya bayyana cewa waɗannan nade-naden suna jiran tantancewar Majalisar Dattawa. Sai dai, domin kauce wa gibin shugabanci a hukumar, Shugaba Tinubu ya umarci Injiniya Ramat da ya fara aiki a matsayin mukaddashin shugaba kafin tantancewarsa, bisa tanadin doka.
Injiniya Ramat, mai shekaru 39, kwararre ne a fannin injiniyan lantarki, yana kuma da ƙwarewa a harkokin gudanarwa, yana da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanarwa ta Dabaru (Strategic Management).
Daga Bello Wakili