Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza
Published: 11th, August 2025 GMT
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce dole ne dukkan kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen laifukan da Isra’ila ke aikatawa a zirin Gaza da kuma kawo karshen killacewa da take yi wa yankin.
Pezeshkian ya bayyana hakan ne a ranar Lahadin da ta gabata yayin da yake karbar takardar shaidar sabbin jakadun kasashen Habasha, Estonia, Djibouti, Laos, Cambodia, Burundi, Latvia, Myanmar, da Nepal.
Ya ce gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da kara zafafa laifukan da take aikatawa a kan al’ummar Palastinu marasa kariya da ake zalunta a zirin Gaza.
Shugaban na Iran ya jaddada cewa: Dole ne dukkan kasashen duniya musamman kasashen musulmi su kara himma da hadin gwiwa wajen dakile wadannan laifuka a Gaza, da kuma isar da taimako mai yawa ga mutanen Gaza.
Ya yi gargadin cewa wani “mummunan bala’i” yana faruwa a Gaza, inda Isra’ila ke kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, tare da toshe hanyoyin samun abinci, ruwa, da magunguna da sunan kare kai.
“Babban abin bakin ciki shi ne ana aikata wadannan laifuka a kan idanun wadanda ke da’awar kare hakkin bil’adama, dimokuradiyya, da ‘yancin dan adam a duniya,” in ji Pezeshkian.
Yakin Isra’ila, wanda ya fara a watan Oktoban 2023, ya yi sanadin shahadar Falasdinawa akalla 61,430 tare da jikkata sama da 153,213.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Wani Hari Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza August 11, 2025 Iran: Babu wani abu da aka yanke game da tattaunawa da Washington August 11, 2025 Kwamitin Tsaro ya yi zaman gaggawa kan Shirin Isra’ila na mamaye Gaza August 11, 2025 Iraki: An bankado wani yunkurin kai wa masu ziyarar Arbaeen hari August 11, 2025 Chadi: An Daure Wani Dan Adawa Shekaru 20 A Gidan Kaso Da tara August 10, 2025 Dangantaka Tsakanin Iran da Saudiya Yana Taimakawa Zaman Lafiya A yankin August 10, 2025 Iran Zata Hana Amurka Samar da Hanya A yankin Caucasus Ko Rasha Bata taimaka ba August 10, 2025 HKI Ta Kai Hare-Hare A Kan Garuruwa Da Dama A Yankin Quneitra Na Kasar Siriya August 10, 2025 An Zabi Alkalan Wasa Biyu Daga Kasar Iran Don Alkalanci A gasar Kwallon Kafa ta Mata August 10, 2025 Kasar Iran Ta Yi Allah Wadai Da Bukatar ‘Yan Sahayoniyya Ta Son Kwace Zirin Gaza August 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
EU da AU na taro kan diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi
Taron koli karo na 7 na tarrayar Turai da tarayyar Afrika, wanda aka bude a Luanda, na maida hankali kan batun diyya ga laifukan mulkin mallaka da cinikin bayi a karon farko.
A cewar ajandar taron, daya daga cikin manyan jigogi zai mayar da hankali kan diyya ta kudi da siyasa da ta shafi zaluncin mulkin mallaka da cinikin bayi, gami da lalacewar tattalin arziki, da al’adu da aka tara tsawon shekaru da dama.
Wannan lokaci ne da ba a taba ganin irinsa ba a wannan matakin siyasa: ba a taba sanya irin wannan batu a cikin ajandar taron da ya hada shugabannin kasashen Turai da Afirka ba.
Kungiyar Tarayyar Afirka ta ware shekarar 2025 a matsayin shekarar “Adalci ga ‘Yan Afirka da kuma Mutanen da suka fito daga zuriyar Afirka ta hanyar diyya.
A cewar AllAfrica, kawai shigar da batun a cikin ajandar ya zama babban ci gaba, domin manyan biranen Turai sun dade suna guje wa batun.
Baya ga batun diyya, taron kolin ya yi magana kan batutuwa daban-daban: ci gaba mai dorewa, zuba jari, gyare-gyare ga tsarin kuɗi na duniya, rage raunin bashi, kirkire-kirkire, tsaro, da yanayi.
Kusan shugabanni 80 ne ke halartar taron, wanda João Lourenço, Shugaban Angola kuma Shugaban Tarayyar Afirka na yanzu, da António Costa, Shugaban Majalisar Turai, tare da Ursula von der Leyen suke jagoranta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Hizbullah: Isra’ila na kure idan ta na tunanin kashe-kashe zai kawo karshen kungiyarmu November 25, 2025 Tashar Talabijin ta Press TV ta kaddamar da sashen harshen Hebrew November 25, 2025 Bincike : Isra’ila Ta Kashe Falasdinawa Akalla 100,000 a Gaza November 25, 2025 Kasar Gambia Ta Bai Wa Jagoran ‘Yan Hamayyar Siyasar Kasar Kamaru Mafaka Ta Wucin Gadi November 25, 2025 China Ta Yi Tir Da Yadda Kasar Japan Ta Girke Makamai Masu Linzami A Kusa Da Yankin Taiwan November 25, 2025 Velayati: Alakar Iran da Iraki tana da karfi November 25, 2025 Arakci Ya Yi Gargadi Akan Abin Zai Biyo Bayan Keta Dokokin Duniya Da “Isra’ila” Take Yi A Cikin Wannan Yankin November 25, 2025 An Gudanar Da Jana’izar Shahidai 300 A Dai-Dai Ranar Shahadar Zahra (s) A Jiya Litinin November 25, 2025 Amurka Da HKI Sun Kawo Karshen Hukumar GHF Mai Raba Abinci A Gaza November 25, 2025 Babban Kwamandan Sojojin Sudan Ya Yi Watsi Da Shirin Trump Na Zaman Lafiya November 25, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci