PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027
Published: 8th, August 2025 GMT
Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya.
Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027.
Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano
Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar.
A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
Ya ce hakan babbar barazana ce ga jam’iyyar PDP.
A cewar kundin tsarin mulkin PDP, babu wani mamba da zai haɗa kai da wata jam’iyya ko ƙungiya don rage ƙarfan jam’iyyar ko gwamnatin PDP.
Ologunagba, ya ƙara da cewa irin waɗannan ayyukan suna haifar da rabuwar kai, rikici da ficewar mambobi daga jam’iyyar, wanda ka iya rage ƙarfinta a zaɓe mai zuwa.
Don haka, Kwamitin Gudanarwa na PDP (NWC) ya yi gargaɗi mai ƙarfi ga waɗanda ke aikata irin waɗannan abubuwa.
Ya kuma buƙaci da su daina, ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri bisa tsarin jam’iyyar.
Jam’iyyar ta kuma buƙaci dukkanin mambobinta su kasance masu biyayya tare da ci gaba da shiri don tunkarar babban taronta na ƙasa da zai gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, daga 15 zuwa 16 ga Nuwamban 2025.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargadi Goyon Baya Zaɓen 2027
এছাড়াও পড়ুন:
Yara biyu sun mutu bayan faɗawa rijiya a Kano
Ana fargabar cewa wasu yara biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan faɗawa rijiya a ƙananan hukumomin Dawakin Tofa da Dala da ke Jihar Kano.
Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Jirgin ƙasa ya murƙushe babur mai ƙafa uku a Jos Majalisar Dattawa ta dakatar da tantance sabon Ministan TinubuA cewarsa, tsautsayin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 8:53 na safiyar ranar Talata a ƙauyen Kashirmo da ke yankin Sarkakiya na Dawakin Tofa, inda wata yarinya mai shekara takwas mai suna Zara’u Muhammad ta faɗa wata rijiya da ke kusa da gidansu.
Duk da ƙoƙarin jama’a na ceto yarinyar kafin isowar jami’an hukumar kashe gobara ya ci tura, saboda zurfin rijiyar da kuma yawan ruwan da ke cikinta.
Sai dai daga bisani an tsamo gawarta, sannan aka miƙa ta ga dagacin yankin, Abdullahi Garba.
Sai kuma a Larabar ce makamancin wannan lamari ya auku, inda wani yaro mai shekara shida, Ahmad Abdurashid, ya faɗa rijiya a unguwar Dandishe Tsamiyar Goodluck da ke a ƙaramar hukumar Dala.
An dai samu nasarar ceto yaron a raye amma daga bisani ya ce ga garinku nan.
Daraktan hukumar, Alhaji Sani Anas, ya bayyana baƙin ciki kan faruwar irin waɗannan lamurra, yana mai roƙon jama’a da su riƙa rufe rijiyoyi da kyau da kuma kula da yara ƙanana domin guje wa irin wannan mummunan sakamako.