2025-07-31@10:57:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7
«ziyarar ta aziyya ga»:

Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari
Shugabannin Hukumomin Watsa Labarai Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya ga Tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari Shugabannin manyan hukumomin watsa labarai na ƙasa Hukumar Rediyon Najeriya (FRCN), Gidan Talabijin na Ƙasa (NTA), da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) – sun kai ziyarar ta’aziyya ga tsohuwar Uwargidan Shugaban Ƙasa, Hajiya Aisha Buhari, bisa rasuwar mijinta, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Daraktan Kula da Yankin Arewa maso Yamma na Rediyon Najeriya, Mallam Buhari Auwalu, shi ne ya gabatar da tawagar, inda ya bayyana rasuwar tsohon shugaban ƙasar a matsayin babban rashi ga iyalinsa, Najeriya da ma duniya baki ɗaya. Yayin ziyarar, Daraktan Sashen Injiniya na Hedikwatar Rediyon Najeriya, Injiniya Sanda Askira, ya roƙi Allah Madaukakin Sarki da ya gafarta wa marigayin...
Shugaban Ƙasar Gambiya, Adama Barrow, tare da matarsa Fatoumata Barrow, sun ziyarci Jihar Katsina, inda suka yi ta’aziyyar rasuwar tsohon shugaban ƙasa, marigayi Muhammadu Buhari. Sun kai ziyarar ne a ranar Juma’a domin jajanta wa iyalan marigayin game da rashin da suka yi. Za a ɗauke wuta na tsawon kwanaki 25 a Legas — TCN Wani mutum ya buɗe Ofishin Jakadancin Indiya na bogi a ƙasar Sun sauka a filin jirgin sama na Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, inda Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina, Barista Abdullahi Faskari, ya tarbe su a madadin Gwamna Dikko Umar Radda. Bayan sojoji sun yi wa Shugaba Barrow faretin ban girma, sun wuce Daura kai-tsaye, inda suka yi wa iyalan marigayin da kuma Mai Martaba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Firaministan Pakistan Muhammad Shehbaz Sharif ya na ziyara a birnin Tehran domin inda yake ganawa da manyan jami’an kasar kan muhimman batutuwan da suka shafi kasashen biyu, shiyya-shiyya da kuma duniya baki daya. A yau litinin ne Sharif ya jagoranci tawaga a Tehran bisa gayyatar da shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya yi masa. Da yake magana a wata hira da IRNA gabanin ziyarar tasa, Sharif ya yaba da diflomasiyyar zaman lafiya ta Iran a matsayin abin a yaba, yana mai jaddada goyon bayan al’ummarsa ga Jamhuriyar Musulunci. Ya ce babban makasudin ziyarar tasa a Tehran ita ce nuna godiya ga Iran bisa goyon bayan da ta bayar, musamman yadda ta amince da diflomasiyyar Iran a yankin, a lokacin da...

Batun Zuba Hannun Jari A Amurka Ne Babbar Ajandar Ziyarar Shugaba Donald Trump Zuwa Kasashen Larabawan Yankin Tekun Pasha
A yau Talata ne shugaban kasar Amurka Donald Trump ya isa kasar Saudiyya domin fara ziyarar aiki a karon farko tun da ya zama shugaban kasa. Baya ga kasar Saudiyya shugaban kasar ta Amurka zai kuma kai Ziyara zuwa kasashen Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da zummar bunkasa alaka da larabawan yankin tekun Pasha kamar yadda majiyar bangarorin biyu take ambatawa. Bugu da kari, kafafen watsa labarun Amurka sun ce, a yayin wannan ziyarar tashi, shugaban kasar Amurkan, zai yi kokarin samarwa kasarsa hannun jari da kasashen larabawa masu arziki za su zuba. Tun a baya dai Donald Trump ya bukacin ganin Saudiyya kadai ta kara yawan hannun jarinta a cikin Amurka da zai kai dala tiriliyan 1. Kafar watsa...
Sheikh Isa Ali Pantami ya ziyarci Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir domin yi masa ta’aziyyar rasuwar Sheikh Sa’idu Hassan Jingir a garin Jos, fadar Jihar Filato.
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya karbi bakuncin tawaga daga kasar Saudiyya karkashin jagorancin Sheikh Nuhu Idris Fallata shugaban hukumar Saudiyya mai kula da ciyar da Alhazai. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta zo ne domin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da dansa ya rasa. Sheikh Fallata ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu. Tawagar ta kuma yabawa tare da karrama Gwamna Namadi bisa kulawa da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar Alhazai. A cewar tawagar, jihar Jigawa ta yi fice mai ban sha’awa a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024. Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jiha Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yabawa tawagar bisa karrama gwamnan jihar ta...