Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza
Published: 9th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon.
A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa.
Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi kasar Labanon, tare da jaddada muhimmancin kiyaye yanayin amincewa da daidaito tsakanin bangarori daban-daban na siyasa, da kuma kaucewa duk wani mataki da zai iya haifar da rikici a cikin gida.
Bangarorin biyu sun jaddada bukatar janyewar haramtacciyar kasar Isra’ila gaba daya daga yankunan da take ci gaba da mamayewa a kudancin kasar Lebanon da kuma dakatar da kai hare-hare a kan mutanen kasar.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza August 9, 2025 Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon August 9, 2025 Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka Ta Kwace Dalar Amurka $584 Na Jami’ar California A Los Angeles Saboda Gaza
Gwamnatin amurka ta kwace kudaden Jami’ar Calfoniya da ke birnin Losangelis saboda abinda ta kira samuwar masu goyon bayan Falasdinawa a cikin dalibai da kuma malaman jami’ar.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, wannan babban kalu bale ne ga Jami’ar saboda rashin wadan nan kudade. Gwamnatin amurka ta zargi hukumomin Jami’ar da gudanar da tarurruka da kuma gangami da zanga zanga na goyon bayan Gaza a jami’ar.
Labarin ya nakalto Dr Julio Frenk shugaban Jami’ar Calfonia a birnin Losangeles na 7th ya bayyana a jiya Laraba kan cewa rike wadannan kudin ba karami matsalace ga Jami’ar UCLA ba, ga kuma kasar Amurka kanta.
Gwamnatin nTrump dai ta bayyana cewa Jami’ar LosAngeles a Califonia, da, Columbia University a New Yrork da Stanford University, da wasu da dama a Amurka suna barin a gudanar da ayyukan na kin yahudawa a cikinsu. Wadanda suka hada da taron gangamin yin All..wadai da HKI da kuma gwamnatin Amurka wacce take goyon bayanta a kissan kiyashin da take yi a Gaza.
Wannan matsalar ta bullowa wadannan jami’o’I ne tun lokacin fara yakin Tufanul Aksa a shekara ta 2023.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya August 7, 2025 Amurka ta Fara Janye Wasu Sojojinta Daga Wurare 3 A Kasashen Iraki Da Siriya August 7, 2025 Kasar Masar Tana Ta Zama Mai Shiga Tsakanin Iran Da IAEA Da Kuma Amurka August 7, 2025 Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba August 7, 2025 Ghana: Ministocin tsaro da muhalli sun rasa rayukansu a hatsarin jirgi mai saukar ungulu August 7, 2025 Jamus: Shahararrun mutane da ‘yan jarida sun bukaci a daina baiwa Israila makamai August 7, 2025 Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya August 7, 2025 Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza August 6, 2025 Araqchi Ya Taya Larijani Murnar Zama Sakataren Majalisar Kolin Tsaron Kasar Iran August 6, 2025 Japan: An Fara Juyayin Cikar Shekaru 80 Da Harin Amurka Na Makamin Nukiliya A Hiroshima August 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci