2025-08-10@23:21:36 GMT
إجمالي نتائج البحث: 7635

«na da matuƙar»:

    “Na taɓa zama abar kwatance, musamman a ɓangaren da shafi kuɗi, suna, girmamawa, amma kuskuren da na yi ya zama dalilin da yasa masana’antar ta juya min baya, sakamakon babu abin da na iya ko na sani face; harkar ta fim. Halin da ake ciki yanzu, babu wani tallafi, babu aikin yi, akwai lokacin da ina da ɗimbin masoya da suke son aurena da kuma nuna min soyayya, amma sai na kasa zaɓen wanda zan ci gaba da rayuwata da shi a wancan lokaci. Babban dalilin da ya jawo min koma-baya a harkar fim shi ne, hatsarin da na samu na mota, wanda Allah ya jarrabce ni da shi, na yi hatsarin mota da har sai da na samu karaya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rahotanni daga sojojin da ke mulki a Mali, sun ce sun kama wasu sojoji kusan 30 da ake zargin suna shirin kifar da gwamnati ƙasar. Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa cikin waɗanda aka kama akwai Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti da ke tsakiyar ƙasar. Ma’aikatan shari’a 97 sun samu ƙarin girma a Borno EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  Har yanzu gwamnatin ƙasar ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba game da lamarin. Ita ma gwamnatin da ke mulki yanzu ta karɓi mulki ne ta hanyar juyin mulki a shekarar 2021. Wannan zargi ya ƙara nuna cewa akwai rashin kwanciyar hankali a tsakanin gwamnatin sojin. Yanzu haka dai gwamnatin na fuskantar matsalar hare-haren masu...
    “Duk da cewa jama’a suna da ‘yancin nuna sha’awarsu kan siyasa, shirye-shiryen amincewa, yunƙurin tattarawa, da tallace-tallace irin na kamfen da nufin tallata ‘yan takara kafin lokacin yaƙin neman zaɓe na hukumance ba a amince da su ba. “INEC tunin ta nusar da wannan batun a lokacin ganawarta da jam’iyyun siyasa, ta kuma gargaɗin dukkanin ‘yan siyasa da su bi dokoki da ƙa’idojin zaɓe,” sanarwar ta shaida. Ya buƙaci ‘yan siyasa da magoya bayansu da su mutunta matakan zaɓe tare da jiran jadawalin yadda zaɓen zai gudana a hukumance kafin su fara harkokin yaƙin neman zaɓe. Wannan gargaɗin dai na zuwa ne yayin da ake ƙara samun yadda jama’a suke ayyana goyon bayan tazarcen Shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma...
    Wata kotu a kasar Chadi ta daure tsohun firai ministan kasar Succes Masra shekaru 20 a gidan kaso da taran caifa biliyon guda a jiya Asabar. Shafin yanar gizo na Labarai Afrika Newas ya kara da cewa kotun ta tabbatar da laifin kan dan siyasar, kuma dan adawa da gwamnatinn Debi, da laifin watsa wasu kalaman batanci da raba kan mutane, har ila yau da hannu cikin rigimar Mandakao ina ya kai ga rasa rayuka masu yawa. A cikin watan Mayun da ya gabata. Lawyan dan siysan ya bayyana rashin amincewa da hukuncin, ya kuma bayyana cewa an yi amfani da sharia don warware matsalar siyasa ne kawai. Akai wasu mutane 74 wadanda suka gurfana a gaban kotun dangane da...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran Abba Aragchi ya bayyana cewa kara karfin da dangantaka tsakanin Iran da Saudia yake yi, yana taimakawa zaman lafiya a yankin. Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar iran ya kara da cewa Aragchi ya bayyana haka ne a lokacinda ya gana da jakadan kasar Iran a Saudiya Ali Reza Enayati  a jiya Asabar a nan Tehran. Jakadan ya gabatarwa ministan rahoto kan inda dangantaka tsakanin Iran da saudiya yake. A na shi bangaren ministan ya bayyana kara karfin da dangantaka tsakanin kasashen musulmi biyu yana taimakawa da zaman lafiya mai dorewa a yankin. Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name*...
    Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae shawara, wato Ali Akbar Wilayati ya bayyana cewa Iran zata hana America samar da hanya a yankin Caucasus, ko da kasar rasha ta taimaka ko bata taimaka ba. A wata hira na musamman da kamfanin dillancin labaran Tasnim, Ali Akbara wailayati ya yi watsi da wani shiri wai shi zangezur wanda an tsara zai hana kasar Armenia da Nakhchivan. Da aka tambaye shi da maganar cewa Armenia zata bawa Amurka yankin haya na tsawon shekaru 99 masu zuwa, Wilayati ya bayyana cewa warin zai zama makabartan sojojin Donal trump, wannan ba hanya ce wanda Amurka ta mallaka ba. Ya ce gwamnatin kasar Iran ta sha bayyana cewa bata...
    Sojojin HKI sun shiga yankuna da dama a lardin Qunaitara na kasar Siriya a Jiya Asabar. Inda ta kafa shingaye a kan tituna a wasu garuruwa a lardin suka yi ta binciken ababen hawa, kafin su janye daga baya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa, HKI tana shirin mamayar wadan nan yankunan na kasar Siriya shi ya sa bata son ganin an sami zaman lafiya a kasar ta Syriya gaba daya, har zuwa lokacinda zata mamaye yankin. Gwamnatin kasar Siriya mai ci ta tabbatar da cewa samuwar sojojin HKI a duk lokacinda suka ga dama a wadannan yankuna alamace ta rashin zaman lafiya a kasar. Kowa ya san cewa HKI ba zata taba barin kasar Siriya...
    Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta bada sanarwan cewa alkalan wasan kwallon kafa ta mata kuma ta Salon guda biyu ne ta zama a kasar Iran don alkalanci a gasar FIFA ta kwallon Saloon ta masa na wannan shekara ta 2025, wanda za’a gudanar a kasar Philipine. Zaben Zari Fathi da kuma Gelareh Nazemi a matsayin alkalai a wannan gasar mai muhimmanci ya nuna irin matsayinda Iran take da shi a hukumar ta FIFA. A ranar 21 ga watan Nuwamba mai zuwa ne, zuwa 2 ga watan Decemban shekara ta 2025 ne za’a gudanar da gasar kwallon salon ta mata da kuma duniya a biranen Manila da Negros,na kasar Philipine. Inda kungiyoyin kwallon kafa ta mata 16 daga kasashen...
    Amma saboda yanzu yanayin rayuwa ya canza, ba ni da mota ko ɗaya; ya sa idan na yi waccan maganar sai wasu su riƙa nuna rashin amincewarsu, wannan kuma rashin sani ne kawai, domin kuwa da a ce sun san wane ne Mai Dawayya a shekarun da suka gabata, da ba su yi wannan magana ba, koda kuwa da wasa, in ji shi. Mai Dawayya ya buƙaci matasan mawaƙa masu tasowa a masana’antar ta Kannywood, da su tabbatar sun yi amfani da wannan lokaci da suke kan ganiyarsu, duniya kuma take yi da su; wajen gina gobensu, ba wai su dinga hawan motoci da sauran sharholiyar rayuwa ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Ƴan bindiga sun kashe mutane biyar, ciki har da wani Ɗansanda, a sabon harin da suka kai garin Babanla a ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar Kwara. Lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, kwanaki ƙalilan bayan kisan wasu matafiya uku da garkuwa da wasu biyu a yankin. Mai magana da yawun rundunar ƴansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi, ta ce maharan sun kai ɗaruruwa akan babura ne suka farmaki garin, kuma suka kai hari ofishin Ƴansanda na yankin, sannan suka yi ɓarna a kasuwar garin. An kashe Kofural Adejumo Wasiu tare da wasu fararen hula huɗu. NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas  Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu Ta bayyana...
    Hukumar Shari’a ta Jihar Borno ta ƙara wa ma’aikatanta 97 girma bayan wani taro na kwanaki huɗu da ta gudanar a Maiduguri. Muƙaddashin sakataren hukumar, Saleh Khala Jidda ne, ya bayyana hakan a wata sanarwa cewa ma’aikatan sun samu ƙarin girma ne saboda ƙwazonsu. EFCC ta kama ’yan damfara a ɗakin karatun Obasanjo  ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato Waɗanda abin ya shafa sun hada da Majistare 10 daga matakin Majistare mataki na ɗaya zuwa Babban Majistare mataki na biyu. Sai Majistare daga matakin farko zuwa Babban Majistare na biyu. Sauran sun haɗa manyan Magatakarda daga mataki na ɗaya zuwa na biyu. Sai dai a gefe guda, hukumar ta ɗauki mataki kan wani alƙalin Babban Kotun Majistare...
    Wakilan LEADERSHIP sun lura cewa yanzu ana amfani da wasu daga cikin waɗannan ofisoshin hulɗa da jama’a na Jihar Legas a matsayin matsugunin ‘yan kasuwa na da masu safarar barasa. Binciken da aka yi ya kuma nuna cewa jami’an tsaro da masu kula da waɗannan gidaje suna hayar wasu sassan gine-ginen da daddare don yin haramtattun ayyuka, inda suka mayar da su gidajen karuwai. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da kuma ‘yan kasuwa a yankunan da ke maƙwabtaka da su, inda suka ce ayyukan na da matuƙar haɗari ga tsaro, suna jawo masu aikata laifuka, da kuma zubar da mutuncin wakilan Jihar a Legas. Lamarin dai ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna yankin da...
    Jami’an tsaron kasar Iran sun murkushe ‘yan ta’adda da suka kai hari a ofishin ‘yan sanda a kudu maso gabashin kasar Wasu ‘yan ta’adda da ake kira “Rundunar Shari’a” sun yi yunkurin kai farmaki ofishin ‘yan sanda na Saravan da ke lardin Sistan da Baluchestan na kasar Iran a wani tsararren harin wuce gona da iri kan jami’an tsaron Iran, amma jami’an tsaron da aka tura domin kalubalantansu sun yi nasarar mayar da martani mai gauni kan ‘yan ta’addan. A cewar majiyoyin Iran, an kashe ‘yan ta’adda uku tare da kame biyu a wadannan gumurzun. Wani dan sanda mai suna Khodadad Baqiri Saravan ya yi shahada a wani artabu da gungun ‘yan ta’adda a birnin Saravan. Share 0 0 votes...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta dauka na mamaye zirin Gaza Ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da matakin baya-bayan nan da majalisar ministocin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta dauka na mamaye yankin zirin Gaza da korar al’ummarta, tare da la’akari da hakan a matsayin wani mataki na kammala shirin kisan gillar ga Falasdinawa da suke yi da kawar da asalin wanzuwar Falastinu. A cikin bayanin da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta fitar dangane da abubuwan da suke faruwa a zirin Gaza da yankunan Falastinu da aka mamaye, ma’aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayyana matukar damuwarta da takaicin yadda ake ci gaba da...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    A kokarin ta na ci gaba da kula da harkokin ilimi a yankin, Karamar Hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta kaddamar da aikin tantance malaman makaranta na B teach da kuma ma’aikatan lafiya na wato B health.   A jawabin sa wajen fara tantance malaman da ma’aikatan lafiyar, Shugaban karamar hukumar, Dr Muhammad Uba Builder, yace aikin tantancewar ya zama wajibi domin tabbatar da ma’aikata na gaskiya da kuma gano na bogi. Yana mai cewar akwai rahotannin daya nuna wasu suna aiki 2 wasu kuma suna amfani da takardun bogi.   A don haka, yace duk wanda aka samu da hakan zai rasa aikin sa gami da kama shi don fuskantar hukunci.   Builder Muhammad Uba, yace an...
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
    An sake shiga tashin hankali a Jihar Sakkwato bayan wani sabon mummunan hari da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyuka, lamarin da ke ƙara tsananta matsalar tsaro a faɗin jihar. Rahotanni sun nuna cewa duk shekara musamman a lokacin damina, ’yan bindiga sukan ƙara ƙaimi wajen kai hare-haren da ke tarwatsa jama’a a garuruwansu da hana manoma zuwa gona ko kuma ƙaƙaba musu harajin zuwa gonakin. An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr Aminiya ta ruwaito cewa, a bana ma, maharan sun ci gaba da addabar mazauna ƙananan hukumomi 20 daga cikin 23 na Jihar Sakkwato. Majiyoyi sun tabbatar cewa a harin baya-bayan nan, ’yan ta’addan sun hallaka...
    Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas. NDLEA Ta Cafke Masu Baburan Da Ke Kai Saƙon Muggan Ƙwayoyi A Abuja Dole Ne Afrika Ta Mayar Da Hankali Wajen Amfana Da Damarmakin Da Ke Tekunanta – Ɗantsoho Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi...
    dimokuradiyya ta hanyar ba da umarni ga manyan wadanda ya nada na arewa su halarci taron.   “Wannan aiki daya na sadaukarwar da shugaban kasa ya yi don tattaunawa da mutane   Yana ishara da cewa, ba wai isa ce kadai a kan iya siyasa ba har ma da isa matuka wajen mutunta ka’idojin dimokuradiyya.   Mahalarta taron sun hada da; Sakataren Gwamnati na Tarayya, Sanata George Akume, Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro Malam Nuhu Ribadu, Babban Hafsan Hafsoshin Tsaro Janar Christopher Musa, Hafsan Hafsan Sojin Sama Hassan Bala, Kwamanda Janar na NSCDC Dr. Ahmed Abubakar Audi, Shugaban Gwamnonin Arewa, Mai Girma Gwamna Inuwa Yahaya, Mai Girma Gwamnan Jihar Kwara Da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Hon. Abdulrazak...
    Wata kotu a N’Djamena, babban birnin Chadi, ta yanke wa tsohon firaminista kuma madugun adawa, Succes Masra, hukuncin ɗaurin shekaru 20 a gidan yari. Kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP ya ruwaito kotun ta samu tsohon firaministan da laifin kalaman ƙiyayya, nuna wariyar ƙabilanci da kuma tayar da tarzomar da ta rikiɗe zuwa kisan kiyashi. Dan wasan Barcelona Inigo Martinez ya koma Al-Nassr MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Kotun a ranar Asabar ta ce ta sami Mista Masra da laifi kan rawar da ya taka wajen tayar da rikicin ƙabilanci wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 42 a ranar 14 ga Mayu — waɗanda galibi mata da yara ne a yankin Mandakao da ke kudu maso...
    A ranar Asabar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da cewa dan wasan bayanta, Inigo Martinez zai bar kungiyar, kuma jaridun Sifaniya sun ruwaito cewa zai koma kungiyar Al-Nassr da ke gasar Saudi Pro League. Tafiyar Martinez za ta taimaka wajen rage nauyin biyan albashin ’yan wasa a Barcelona, kungiyar da a bayan nan ke fama matsalar rashin kudi. MDD za ta yi zaman gaggawa kan yunƙurin ƙwace Gaza Dubban mutane sun yi zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu a Isra’ila da Pakistan Martinez mai shekara 34 ya buga wasa a wasanni 71 a dukkan gasanni tun bayan komawarsa kungiyar daga Athletic Bilbao a shekarar 2023, inda ya taimaka wa Barcelona ta lashe kofin La Liga a kakar bara. Kafin haka,...
    Gwamnan ya kuma umurci jami’an tsaro da su rufe gidan rediyon tare da nemo bayanan mai gidan rediyon, inda ya zarge ta da haddasa tashin hankali.   Sai dai a kara mai lamba FHC/L/CS/1587/2025 da aka shigar a ranar Juma’ar da ta gabata a babban kotun tarayya da ke Legas da SERAP da kuma NGE suna neman sani “ko a sashe na 22 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) da sashe na 2(1) (t) na dokar NBC, NBC na da hakkin kare ‘yancin Badeggi FM da gwamnan Neja ya rufe.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Jami’in ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 Ali Baqiri Kani mamba a majalisar tsare-tsaren a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta cimma babban matsayi a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa da yahudawan sahayoniyya. Baqiri ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi ta gidan talabijin a yammacin jiya Asabar cewa: Tabbas Iran ta cimma matsayi sosai a yakin kwanaki 12 da aka kwashe ana gwabzawa, yana mai jaddada muhimmancin diflomasiyya wajen tunkarar hare-haren da ake kai wa kasar, yana mai jaddada cewa: “Dole ne Iran ta mayar da martanin wuce gona da iri...
    Ɗan wasan Liverpool Mohamed Salah ya soki hukumar kwallon kafa ta Turai, UEFA, kan wallafa sakon alhinin mutuwar ɗan wasan Falasɗinawa da ya rasu ba tare da ba da cikakken bayani kan abin da ya yi sanadin rasuwarsa ba. A ranar Alhamis aka kashe Suleiman al-Obeid, wanda aka fi sani da Pelen Falasɗinawa – a hare-haren Isra’ila lokacin da yake jiran karɓan kayan tallafi a kudancin Gaza. “Ko za ku faɗa mana ta yaya ya mutu sannan a ina,” kamar yadda Salah ya wallafa a shafinsa na X ranar Asabar. Obeid wanda ɗan wasan gaba ne, ya zura kwallaye sama da 100 a tsawon rayuwarsa ta tamaula.
    Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon saukar agajin da aka kai a zirin Gaza ya kai Falasdinawa 23 tare da jikkata wasu 124 Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon saukar da agaji ta hanyar jiragen sama tun bayan fara yakin kisan kare dangi da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan zirin Gaza ya karu zuwa 23, yayin da wasu 124 suka samu raunuka, kamar yadda ofishin yada labarai na gwamnati a zirin Gaza ya sanar. Ofishin ya tabbatar da cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya, Asabar, cewa: Akasarin wadannan kayan agajin da jiragen saman ke watsowa ta sama suna fadowa ne a yankunan da ‘yan mamaya suka mamaye, ko kuma a cikin unguwannin da...
    “Baya ga alaƙa da Ruwa, ƙasashen da ke Afirka ta Gabas da kuma waɗanda ke a Afrika ta Tsakiya, da suke yi musharaka da irin ƙalubalensu da kuma sauran damarmakinsu, dole ne mu zage mu amfana da tattalin arzikin da ake da shin a Tekuna, musamman ta hanyar haɗa kanmu da kuma yin haɗaka, wanda idan ba a yi hakan ba, tamkar muna kawai yaudarar kawunan mu ne,” Ɗantso ya ce. A cewar Shugaban na Hukumar NPA, alƙaluman da ake da su, sune za su bamu damar, ci gaba da ɗaukar matakan da suka kamata, na wajen ci gaba da bai wa Tashoshin Jiragen Ruwa na Afrika, kulawar da ta dace. Kazalika, Shugaban ya kuma jinkinawa shugaban ƙasa Bola Tinubu,...
    Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya kira taron gaggawa a wannan Lahadin domin tattauna ƙudirin Isra’ila na ƙwace iko da Zirin Gaza. Wannan shirin, wanda Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da shi a ranar Juma’a, ya jawo suka daga ƙasashen duniya. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres ya kwatanta shirin da abin da zai ƙara dagula lamura a fadan da aka kwashe watanni 22 ana yi. Kasashen Turai da ke cikin Kwamitin Sulhun da suka hada da Denmark da Faransa da Girka da Burtaniya da Slovenia ne suka kira wannan zaman gaggawan a birnin New York na Amurka. DW ya ruwaito cewa, dukkan...
    Gwamnatin jihar Kano ta amince da korar wasu manyan mataimaka na musamman (SSAs) ba tare da bata lokaci ba, sakamakon zarge-zargen da wasu kwamitocin bincike suka yi na gudanar da bincike kan wasu laifuka.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk Ibrahim ya fitar.   A wani gagarumin mataki da gwamnan ya dauka, ya amince da korar Abubakar Umar Sharada, babban mataimaki na musamman kan harkokin siyasa, bayan da kwamitin bincike na musamman ya tuhume shi a matsayin wanda ya shirya belin wani mai hatsarin gaske kuma dilan kwyaan maye, Sulaiman Aminu Danwawu, wanda ya tabbatar da laifin Abubakar Sharada a cikin takaddamar belin ta hanyar kwamitin da ya gabatar a gaban...
    Don haka, kwamishinan ya gode wa ƙungiyar bisa wannan ziyara tare da bayyana shirin Ma’aikatar na yin haɗin gwiwa da haɗin gwiwa ta fuskar horarwa, wayar da kan jama’a, da wayar da kan jama’a game da SGBƁ. Tun da farko, Misis Achimugu ta bayyana cewa ziyarar bayar da shawarwarin ita ce kashi na biyu na ci gaba da wayar da kan jama’a, da bayar da shawarwari, koyan fasaha, da kuma shirin tallafa wa jama’a, wanda wani ɓangare ne na dabarun yaƙi da cin zarafin mata (SGBƁ) a Jihar Kogi. Ta bayyana muhimmancin haɗa hannu da masu ruwa da tsaki, ma’aikatu, sassa, hukumomi (MDAs), ƙungiyoyi masu zaman kansu, da cibiyoyin gargajiya da na addini domin yaƙar matsalar SGBƁ, musamman a tsakanin...
    Gwamnatin jihar Kwara ta gargadi manoma da mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su dauki matakan kariya cikin gaggawa domin ceto jarin da suke zubawa.   A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar noma da raya karkara, Ashaolu Omotola ya fitar, ya ce. Hukumar Kula da Ruwa ta Najeriya NIHSA, ta yi hasashen yiwuwar ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar Kwara tsakanin ranakun 7 zuwa 21 ga watan Agustan bana.   A cewar hukumar ta gano al’ummomi da dama a jihar daga cikin wurare 832 a fadin kasar da ke fuskantar hadarin ambaliya a wannan lokaci.   Ta ce ambaliyar ruwan da ake sa ran za ta iya tarwatsa hanyoyin sufuri tare da yin barazana ga filayen noma,...
    Ya ƙara da cewa an kama aƙalla mutane uku da ake zargin suna da alaƙa da kayan a wani samame da aka kai musu. Babafemi ya ce, “Kashi na farko na kayan, wanda ya kunshi kwayoyin Tramadol 57,420 na tramadol 225mg da 57 na hodar ibilis mai nauyin kilogiram 1.60, an kama su ne a cikin wani kaya da zai je kasar Gabon a Air Cote d’Iɓoire a ranar Asabar, 19 ga watan Yuli, 2025. Wani shahararren dan kasuwan nan mai suna Benkwee Ihesi Osina, shi ne wakilin cargo, wanda aka kama. Shipment, an kama shi nan take, wani bincike ya kai ga kama wani wanda ake zargi, Uzochukwu Godspower Chukwurah, a ranar Lahadi, 20 ga watan Yuli. “An gano...
    Dubban mutane ne suka fito kan tituna a birnin Tel Aviv na Isra’ila ranar Asabar, domin yin kira da a kawo ƙarshen yaƙin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin Isra’ila ta lashi takobin faɗaɗa rikicin tare da ƙwace birnin Gaza. Masu zanga-zangar da ke riƙe da hotunan waɗanda har yanzu ake garkuwa da su a yankin Falasdinawa sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da sakin su ’yan uwansu. Al-Hilal ta ɗauki Nunez daga Liverpool ASUU na shirin sake tsunduma yajin aiki ’Yan jaridar AFP a wajen gangamin sun ƙiyasta adadin waɗanda suka halarci taron a matsayin dubbai, yayin da wata ƙungiya da ke wakiltar iyalan wadanda aka yi garkuwa da su ta ce mutane kusan 100,000 ne suka...
    Garima wanda har ila yau shi ne, and Jakadan Gwandu ya yi nuni da cewa, cibiyoyin na CNG da gwamnatin taraya ta samar a jihohin Kano da Kaduna, za su taimaka wajen samar da Iskar Gas ɗin a Arewa ta tsakiya da kuma Arewa ta Gabas. Kazalika ya ce, samar da cibiyar a jihar Sokoto wadda take kusa da Jamhuriyyar Nijar, hakan zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin jihar Garima ya sanar da cewa, Iskar Gas ɗin ta CNG tsafatattaciya ce kuma bata da wani tsada, inda kuma ta rage gurɓatar muhalli. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin...
    Wani lokacin, yanayin shekaru da Jinsin Jini ne ke fayyace irin girma ko ƙantantar Ƙwan da Kajin za su yi. 2- Wajen Kwana: Kajin na buƙatar a tabbatar da ana samar musu da wadataccen ruwan sha a ɗakunan kwanansu da kuma ba su kariya daga kamuwa da cutuka da rage musu wahala da cunkoso da kuma zafi, wanda hakan na iya shafar Ƙwan da za su yi kai tsaye. 3- Abinci Mai Gina Jiki: Ciyar da su abinci mai gina jiki, wanda ke ɗauke da sinadaran ‘protein, amino acids’, waɗanda za su sanya su yi nauyi tare kuma da buƙatar a riƙa yi musu allurar ƙara musu lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu...
    Jaridar Tehran Times, ta nakalto cewa, Iran da Amurka a shirye suke su fara wata sabuwar tattaunawa. Majiyoyin sun ce tattaunawar za ta kasance ba kai tsaye ba,  sanann kuma ana sa ran cewa kasar Norway ce za ta kasance mai shiga tsakanin bangarorin biyu. Jaridar ta kasar Iran ta yi nuni da cewa “Tehran ta dage kan cewa batun biyan diyya a kan barnar da aka yi mata a yakin baya-bayan nan ya zama wani muhimmin bangare na duk wata tattaunawa a  nan gaba.” A ranar  Alhamis kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya musanta duk wata Magana kan wani takamaiman lokaci ko wurin da za a yi shawarwari da Washington, yana mai jaddada cewa “dukkan jita-jita game da hakan...
    Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza. Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza, suna masu kira ga hukumomi da su ba da fifikon sakin su kan fadada ayyukan soji. An kuma bayyana cewa hatta a cikin manyan jami’an soji na Isra’ila, babban hafsan hafsan hafsoshin sojin Isra’ila  Eyal Zamir ya yi yunkurin shawo kan majalisar ministoci kan cewa mamaye Gaza ba shi ne zabin da ya dace ba, da kuma tattauna babbar illar da hakan...
    Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
    ‘Yan sandan Birtaniya a birnin Landan sun sanar da kame mutane 365 a wata zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wadda kungiyar Palestine Action da gwamnatin Birtaniya ta haramta a watan jiya ta shirya. A cikin jerin rubuce-rubucen da aka yi a Shafin  X, ‘yan sanda sun ce “sun dauki tsauraran matakai a kan wannan laari,  tare da yin barazanar kame duk wanda ya nuna goyon baya ga Action Palestine. Masu zanga-zangar dai na dauke da alamomin da aka rubuta “Ku kawo karshen kisan kare dangi, ku goyi bayan matakin Falasdinu,” tare da rera taken “Ku kun ji kunya”. Kungiyar kare hakkibil adama ta  “Lift the Ban”, ta bayar da rahoton cewa ‘yan sandan Biritaniya sun gaba da kame mutane kan...
    Hukumomin tsaro a kasar Venezuela sun kama wasu tarin bama-bamai a gabashin birnin Maturin na jihar Monagas, a wani abin da jami’ai suka bayyana a matsayin yunkurin da wasu bangarori masu tsatsauran ra’ayi suka yi na kai hare-haren ta’addanci da nufin kawo cikas ga gwamnatin shugaba Nicolas Maduro. Ministan harkokin cikin gida, Diosdado Cabello, ya sanar a jiya Asabar cewa, jami’an tsaro, bayan gudanar da ayyukan leken asiri, sun gano wasu kayyayakin fashewa da abubuwan harhada bama-bamai da aka boye a wasu shaguna biyu.Kayan sun dai sun  hada da akwatuna 1,137 da ke dauke da wasu nauyin bama-bamai da ba a taba ganin irinsu a kasar ba, da  rokoki 35, da igiyoyin tayar ta bama-bamai da ababen fashewa,  na’urorin kashe...
    Kyari ya ce, a yanzu ana noma Waken Soya da ya kai kimanin tan miliyan 1.35, wanda kuma buƙatar da ake da shi a ƙasar ya wuce tan miliyan 2.7. Ya sanar da cewa, wanan tsari zai kuma amfani tattalin arziƙin ƙasar da ƙara samar da ayyuakn yi da kuma ƙara haɓaka samar da wadataccen abinci a ƙasar. Shi kuwa a nasa jawabin a wajen ƙaddamarwar, Gwamnan Jihar Biniwai, Hyacinth Iormem Alia, ya jaddada muhimmancin da za a amfana da shi a tsarin. “Dabarun faɗaɗa noman Waken Soya na ƙasa, mataki ne da ya dace wajen yin haɗaka, domin samar da kuɗaɗen shiga ga ƙasar a duk shekara da suka kai kimanin Naira tiriliyan 3.9 da ƙara ƙirƙiro da ayyukan...
    Yayin ziyararsa a kasar Indiya kwanan nan, shugaban kasar Philippines ya bayyana cewa, idan Sin da Amurka suka yi taho-mu-gama kan batun yankin Taiwan, Philippines ba za ta iya killace kanta daga ciki ba. Irin wannan furucin nasa yana da ban mamaki, wanda ya saba da alkawarin da Philippines ta yi na tsayawa ga manufar kasancewar kasar Sin daya tak a duniya, kana, zai kara illata dangantakarta da kasar Sin, da zaman lafiya da tsaro a wannan shiyya. Rura wutar rikici kan yankin Taiwan, yunkuri ne da Philippines ta yi na dogaro kan Amurka tare da ba ta hadin-kai, don hana ci gaban kasar Sin. Amma batun da ya shafi yankin Taiwan, batu ne na cikin gidan kasar Sin, kuma...
    Mambobin haɗakar jam’iyar sun ƙunshi tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi da tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal da tsohon shugaban jam’iyyar APC, John Oyegun, da sauran manyan mutane da dama. A cikin wannan tsarin, haɗakar jam’iyyar ta naɗa tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark da tsohon ministan cikin gida, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaban da sakatare na riƙon ƙwarya. Tun daga wannan lokaci, jam’iyyar tana ta karɓar masu sauya sheƙa daga sauran jam’iyyun adawa da kuma gudanar da tarurruka domin ƙara masun mambobi a faɗin ƙasar nan kafin zaɓen 2027. El-Rufai, wanda ya kasance ɗaya daga cikin asalin mambobin APC, ya...
    Gwamnatin Jihar Jigawa  ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar.   Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.   A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon.   Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin...
    Jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai, ya gana a kwanan nan da ministar kula da harkokin masana’antu, da cinikayya, da zuba jari ta tarayyar Najeriya, madam Jumoke Oduwole. Jakada Yu ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a watan Satumban bara, zuwa yanzu, Sin da Najeriya na kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, tare da fadada hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi masana’antu, cinikayya da zuba jari, har ma kwalliya ta biya kudin sabulu. Ya ce kasar Sin tana fatan ita da Najeriya za su rattaba hannu kan yarjejeniyar raya dangantakar abokantaka a...
    Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno. A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann. Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi. Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196. Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya yabawa yan jarida musamman a khidimar da suka gabatar a yakin kwanaki 12. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana fadar haka a yau Asabar a lokacinda ya kai ziyarar ganin ido a cibiyar hukumar gidajen radiyo da talabijin na JMI a nan birnin Tehran. Labarin ya kara da cewa shugaban yay aba da ayyukan da yan jarida a kasar suka yi a lokacin yakin kwanaki 12, na samar da hadin kai tsakanin iraniyawa duk tare da banbanci-bambance da ke tsakaninsu da kuma fadin labaran gaskiyan abinda yake faruwa ga mutanen kasar da kuma duniya gaba daya dangane da yakin. Shugaban yay aba da yadda suka nuna zanga-zangar hadin kai...
    Yansanda a kasar Burtaniya ta kama mutane fiye da 200 wadanda suka fito zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a birnin London. Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai a birnin London na cewa mutane kimani 600-700 ne suka fito suka kuma tsaya a wani wuri kusa da majalisar dokokin kasar wanda ake kira ‘ in Westminster’s Parliament Square ‘ inda suke dauke da kwalaye da rubuton ina son mutuncin ma’aikatar sharia, bana son zalunci. Kafin haka dai gwamnatinn kasar ta haramta zanga-zangar da aka saba gudanarwa a birnin na Lodun a dukkan karshen mako, wato ranar asabar na goyon bayan Falasdinawa da kuma yin allawadai da kasashen yamma musamman gwamnatin kasar Burtaniya wacce daga daga cikin...
    Yawancin ‘yan Nijeriya sun nuna damuwa game da yadda majalisar dattawa ta 10 ke gudanar da harkokin majalisa, suna cewa ‘yan majalisar sun gaza bayar da muhimman ayyukan da aka ɗora musu na binciken ɓangaren zartarwa don kare ‘yan Nijeriya. Ana zargin majalisa dattawa ta 10 da ƙin tilasta wa gwamnatin tarayya wurin magance tarin ƙalubale da ke fuskantar ‘yan Nijeriya, ciki har da tsadar rayuwa, talauci, yunwa, yawan rashin aikin yi da rashin tsaro, da sauran su. Rahotanni su bayyana cewa akwai tsofaffin gwamnonin 13 da ke majalisar dattawa ta 10 a halin yanzu, wanda suka haɗa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio (Akwa Ibom), Aliyu Wammako (Sakkwato), Abdulaziz Yari (Zamfara), Aminu Waziri Tambuwal (Sakkwato) da Adams Oshiomhole (Edo)....
    Falasdinwa 11 suka rasa rayukansu a yau Asabar a Gaza saboda yunwa, wanda ya kawo adadin wadanda yunwa ta kasashe a Gaza tun lokacinda HKI ta hana shigowar abinci yankin zuwa 212. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto majiyar ma’aikatar kiwon lafiya na Gaza na fadar haka, sannan masana sun bayyana cewa mai yuwa wannan adadin ya wuce haka, saboda ita yunwa tana hana garkuwan jiki aiki, don haka karamin cuta tana iya kashe mutun saboda yunwa.  Sun kara da cewa akwai wasu Falasdinawa da dama a wasu wurare a cikin gaza wadanda basa da lafiya amma yunwa ta karasa su a gida ba tare da sun zo asbiti ba. Larabarin ya kara da cewa a cikin...
    Shugaban kasar Kwango democradiyya Félix Tshisekedi, a gabatar da sauye-sauye a gwamnatinsa a jiya jumma’a inda ya shigo da sabbin ministoci guda biyu daga bangaren yan adawa. Shafin yanar gizo na labarai ‘Afrika News’ ya bayyana cewa gwamnatinn kasar kwango ta fara wannan sauye –sauyen ne tun farkon wannan shekarar kuma har yanzun akwai wasu sauye –sauyen da zai gabatar a dai-dai lokacinda ake ci gaba da tattaunawa da jam’iyyun adawa da kuma yan tawayen M23. A wannan karon dai shugaban ya shigo da sanannun yan adawa guda biyu cikin gwamnatinsa, kuma sune, Adolphe Muzito, wanda ya taba zama firay ministan kasar, ya bashi matsayi na mataimakin firay minister, kuma shi ne zai kula da kasafin kudin kasar. Sai kuma...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kara da cewa, masana’antar abinci ta Afrika na amfani da dabarun masu samar da kayayyaki na Sin, wajen samar da kayayyaki masu inganci. (Fa’iza Mustapha)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, ta yi aure da masoyinta, Ibrahim Garba. An ɗaura auren a ranar Asabar a Masallacin da ke Unguwan Rimi, a Jihar Kaduna, bayan Ibrahim ya biya sadaki Naira 300,000. Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Rahama, ta sanar da ɗaurin auren a shafinta na Facebook, inda ta gode wa Allah tare da neman addu’a daga masoyanta. Ta bayyana farin ciki da godiyarta, tare da fatan wannan sabon babi na rayuwarta zai kasance mai albarka. Auren mata na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar mahaifinta, Ibrahim Sadau. ’Yan uwanta sun yaɗa hotuna da bidiyon bikin a kafafen sada zumunta, inda...
    Majalisar zartarwa ta karamar hukumar Sule Tankarkar dake Jihar Jigawa ta amince da gudanar da muhimman ayyuka a bangarorin kiwon lafiya da sauran aikace-aikacen ci gaban al’umma.   Taron majalissar bisa jagorancin shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Tasi’u Adamu, ya kuma amince da gina makarantun Tsangaya guda 3 na zamani da za’a sanyawa sunayen wasu fitattun yan siyasa na yankin da suka rasu.   Yayi bayanin cewar, za’a gina makarantun tsangayar ne a garuruwan Danzomo da Shabaru da kuma Rukutu wadanda za’a sanyawa sunan wadanda suka rasu da suka hada da marigayi Sanata Dalha Ahmad Dan Zomo da marigayi Musa Waziri Kamus da kuma marigayi Ali Ado.   Haka kuma majalisar ta amince da gyaran masallatan Juma’a na Hannun Giwa da...
    Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar duniyar wata da aka raba ma wasu hukumomin bincike 7 na kasashe 6. Kana bisa gudanar da bincike kan kasar da na’urorin binciken duniyar wata na kasar Sin, wato Chang’e-5, da Chang’e-6, suka dawo da ita, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na sauran kasashe, sun gabatar da sakamakon bincike fiye da 150. An ce, tsarin da ake bi wajen neman samun...
    Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.! Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima. An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin. Bayanai sun...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da suka rasu. Wannan biyan zai shafi tsoffin ma’aikatan jihar, ma’aikatan wucin-gadi, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da malaman firamare. Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Ana sa ran biyan kuɗin zai fara daga kan watan Disamba 2024 zuwa Maris ɗin 2025. Gwamna Idri, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar ma’aikata da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima. Ya ce biyan haƙƙoƙin ma’aikata ba wasa ba ne, kuma gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen...
    Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da biyan sama da biliyan ɗaya a matsayin kuɗin garatitu ga iyalan ma’aikatan gwamnati 445 da suka rasu. Wannan biyan zai shafi tsoffin ma’aikatan jihar, ma’aikatan wucin-gadi, ma’aikatan ƙananan hukumomi, da malaman firamare. Tinubu ya yi alhinin rasuwar tsohon shugaban PDP, Audu Ogbeh Kotu ta ɗaure wata mata shekara 3 a kan damfara  Ana sa ran biyan kuɗin zai fara daga kan watan Disamba 2024 zuwa Maris ɗin 2025. Gwamna Idri, ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kula da walwalar ma’aikata da iyalansu, musamman waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa jihar hidima. Ya ce biyan haƙƙoƙin ma’aikata ba wasa ba ne, kuma gwamnatinsa za ta yi tsayin daka wajen...
    Manchester United sun kammala sayen ɗan wasan gaba na RB Leipzig, Benjamin Sesko, a kan kuɗi kimanin fam £73.7 miliyan. Sesko, ɗan ƙasar Slovenia mai shekaru 22, ya rattaba hannu kan kwangilar shekaru biyar tare da ƙungiyar. An biyan £66.3m kai tsaye, yayin da sauran kuɗin zai kasance a matsayin ƙari (add-ons). Wannan shi ne sayen ɗan wasa na uku a ɓangaren gaba da United suka yi a wannan kakar, bayan sayen Matheus Cunha a kan fam £62.5m da Bryan Mbeumo a fam £65m, wanda £6m na ƙari ne. Dukansu an gabatar da su ga magoya bayan ƙungiyar kafin wasan wasannin shirin kakar a gida da Fiorentina ranar Asabar. Manchester United Da Everton Na Zawarcin Wilfred Ndidi Sin Ta Gabatar...
    Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku. Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019. Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Gwamnatin...
    Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara. Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024. Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno  Ana tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba. A...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana cewa: Shirin gwamnatin mamayar Isra’ila shi ne shirin share al’umma Falasdinu daga kan doron kasa Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana cewa: Shirye-shiryen da gwamnatin ‘yan sahayoniyya take yi na mamaye yankin Zirin Gaza da kuma tilastawa al’ummar yankin gudun hijira wani karin shaida ne na musamman da wannan gwamnatin take da niyyar aikata kisan kiyashi a Falastinu da ta mamaye. Ismail Baqa’i ya bayyana shirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya na mamaye garin Gaza da sojoji da kuma tilastawa mazauna yankin kauracewa gidajensu a matsayin wani shiri na kammala kisan gillar da  take yi wa al’ummar Falastinu, yana mai jaddada tofin Allah tsine da Allah wadai da wannan mummunan cin zarafi....
    Kwamandan Dakarun Qudus na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gudun da Amurka ta yi daga Yemen wani shan kaye na soji da ba a taba ganin irin sa ba Kwamandan Dakarun Quds na Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ismail Qaani, ya kaddamar da wani kakkausar suka kan Amurka, yana mai bayyana sanarwar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na janyewa daga fagen daga a Yemen a matsayin “Halayen soja mafi wulakanci da kunya” a tarihin Amurka. A cewar wani faifan bidiyo da kafar yada labaran “Dakarun Qudus” suka wallafa a shafinsu na Telegram, Birgediya Qaani ya ce: Shugaban Amurka Donald Trump, da kansa ba wani ba—ba kawai kakakin...
    Mai ba da Shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci da tsohon fira ministan Iraki sun jadadda goyon bayansu ga kugiyoyin gwagwarmaya Mai ba da shawara kan harkokin kasa da kasa ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya tattauna kan ci gaban yankin Gabas ta Tsakiya a wata tattaunawa ta wayar tarho da tsohon fira ministan kasar Iraki Nuri al-Maliki, kuma dukkansu sun jaddada goyon bayansu ga kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa. A tattaunawar ta wayar tarho, Ali Akbar Welayati, mai ba da shawara ga Jagora kan harkokin kasa da kasa, ya yi tambaya game da lafiyar tsohon Fira ministan Iraki Nouri al-Maliki. A cikin kiran, Velayati ya yi fatan samun koshin lafiya ga al-Maliki da samun sauki cikin gaggawa, inda ya...
    “Kuma za a yi hakan ne saboda a matsayinmu na al’umma, muna ci gaba da ƙoƙarin canza abubuwan da ‘yan siyasa ba sa son canzawa,” in ji shi. Ya kuma bayyana cewa ba yau aka fara aikin gyaran kundin tsarin mulkin ƙasar kan batun cin gashin kan ƙananan hukumomi ba. Ejah ya ƙara da cewa ana sa ran kashi biyu cikin uku na ‘yan majalisar wakilai za su kaɗa ƙuri’ar amincewa ko kuma ƙin amincewa da gyaran. Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta bayar da umarnin ne kawai, biyo bayan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke, cewa a biya kason kuɗaɗen da majalisun za su samu kai tsaye a asusunsu. A cewarsa, wannan ba gyara ba ne, domin...
    Rinsola Babajide, Ajibola Abiodun.   ‘Yan Wasan Tsakiya Ibrahim Ayinde, Asisat Oshoala, Chinwendu Ihezuo, Christy Ucheibe, Onyi Echegini, ‘Yan Wasan Gaba Chioma Okafor, Toni Payne, Rasheedat Ajibade, Florence Ijamilusi, Esther Okoronkwo Ifeoma Onumonu, Hakazalika a wani taron liyafa da shugaba Tinubu ya karɓa, wanda mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya wakilta, ya bayar da lambar yabo ta ƙasa ga kowace ‘yar wasa ta tawagar ƙwallon kwando a tawagar, tare da ba su kyautar gida a Abuja, a lokacin da yake jawabi ga tawagar, Shettima ya ce nasarar da suka samu alama ce ta ƙarfin haɗin kai. “Wannan nasara ta nuna abin da ke faruwa iɗan muka yi aiki tare, matan Nijeriya ba su tama bamu kunya a ɓangaren wasanni ba,...
    Wani kurtun soja ya soka wani ɗan sanda mai mukamin Constable, Aaron John da wuƙa har lahira a garin Jalingo, hedikwatar Jihar Taraba. Kakakin ’yan sanda na jihar, James Lashen, ya ce wannan mummunan al’amari ya faru ne da misalin karfe 9 na dare a ranar Litinin, a unguwar Mayo-Goyi, da ke gefen birnin Jalingo. Lashen ya bayyana cewa marigayi John ya samu kiran gaggawa daga wasu mazauna yankin dangane da sabani da suka samu da sojan. A yayin da yake kokarin warware rikicin, sai sojan mai suna Dauda Dedan, ya soka masa wuƙa. Ya ce, “Mun samu rahoton lamarin daga hedikwatar Brigade ta 6 ta Rundunar Sojin Najeriya, da tabbacin cewa za a kamo sojan da ya tsere domin...
    Ganawar da shugaba Trump ya yi a baya-bayan nan da shugabannin wasu ƙasashe biyar dake nahiyar Afirka, ita ma ta janyo hankalin al’ummun duniya. Inda shugaba Trump ya yabawa shugaban ƙasar Laberiya Joseph Boakai kan yadda ya iya Turancin Ingilishi sosai, lamarin da ya bayyana rashin fahimtarsa kan alaƙar tarihi tsakanin ƙasar Laberiya da Amurka. Bugu da ƙari, Trump ya katse maganar shugaban Ƙasar Mauritaniya Mohammed Ghazouani, inda ya nemi ya yi magana da sauri. A hakika, rashin mutuntawa da shugaba Trump ya nuna a fili, ta bayyana ainihin dalilin da ya sa aka gayyaci shugabannin Afirka biyar zuwa wajen ganawar, ba domin neman ƙarfafa dangantaka ba ne, sai dai don tabbatar wa Amurka ɗin damar samun ma’adanan da take...
    A ranar Juma’a da yamma, wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun tare motar haya a mararrabar Ogbabo, kan titin Itobe-Anyigba a jihar Kogi, inda suka yi awon gaba da fasinjoji 9. Direban motar da wasu fasinjoji 6 kuwa sun tsere ba tare da an sace su ba. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:20 na yamma a yankin ƙaramar hukumar Ofu, lokacin da ƴan bindigar suka fito daga daji suka tare titin. Sun tilasta direban motar Toyota mai ɗauke da fasinjoji tsayawa, sannan suka yi harbi cikin iska domin tsoratar da mutane. Direban motar, Sunday Okechi, ya yi dabara ya tsere tare da wasu fasinjoji 6, yayin da sauran 9 suka faɗa hannun ƴan bindigar da suka tafi...
    A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana. Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada da shirye-shiryen sojojin Isra’ila na mallake birnin Gaza. Shirin ya tanadi wasu ka’idoji guda biyar na kawo karshen yakin, wanda ya fara da “kwace makaman Hamas,” sannan a dawo da dukkan fursunonin wadanda ke raye ko a mace. Hakan zai biyo bayan kwance damarar zirin Gaza gaba daya, da kafa wata sabuwar gwamnatin da ba ta karkashin ikon kungiyar Hamas ko kuma hukumar Falasdinawa. Za...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da takwaransa na Masar, Badr Abdel Ati, sun tattauna batutuwan da ke faruwa a zirin Gaza da Lebanon, inda suka jaddada bukatar daukar matakan gaggawa daga kasashen musulmi domin dakile kisan kiyashin da ake yi a Gaza da kuma hare-haren da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke ci gaba da kai wa kasar Labanon. A wata tattaunawa ta wayar tarho da bangarorin biyu suka yi, ministocin biyu sun tattauna kan tabarbarewar al’amuran jin kai a zirin Gaza sakamakon killace yankin da kuma shirin Isra’ila na mamaye yankin gaba daya. Sun kuma jaddada mahimmancin tabbatar cewa an shigar da agajin jin kai na kasa da kasa cikin gaggawa. Har ila yau, sun tattauna batutuwan da suka shafi...
    Shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya sanar a yau jumma’a cewa Jamus za ta dakatar da duk wani izinin fitar da kayan aikin soji da za a iya amfani da su a zirin Gaza, biyo bayan matakin Isra’ila na mamaye Gaza. Da yake magana bayan zaman majalisar ministoci ta Isra’ila da kuma amincewarta da shirin kwace birnin Gaza tare da mamaye shi, Shugaban gwamnatin Jamus Merz ya ce Berlin na ci gaba da ba da goyon baya ga ‘yancin “Isra’ila” na kwance damarar Hamas tare da ganin an sako fursunoni, amma kuma duk da haka basu goyon bayan duk wani mataki zai kai ga kara tabarbarewar lamurra na jin kai a Gaza. “Gwamnatin Jamus ta yi imanin cewa matakin soji...
    Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda al’ummar yankin ke fuskantar barazanar wanzuwa da kuma ‘yancinsu. A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na yau da kullun, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da na larabawa, a wani bangare na yunkurin sake fasalin yankin da kasar Lebanon. Babban abin da kungiyar tafi nuna takaicinta  akansa shi ne amincewar da gwamnatin Lebanon ta yi a baya-bayan nan da  shawarar da manzon Amurka Tom Barrack ya gabatar. Kungiyar...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na kasar Rasha, Vladimir Putin, ta wayar tarho a yau Jumma’a 8 ga wata. A tattaunawarsu, Putin ya bayyana ra’ayin kasar Rasha dangane da rikicin Ukraine a halin yanzu, da yadda Rasha ta tuntubi Amurka kwanan nan, inda ya ce, Rasha ta yaba sosai da muhimmiyar rawar da kasar Sin take takawa a fannin shawo kan rikici ta hanyar siyasa. A nasa bangaren kuma, Xi ya jaddada matsayin kasar Sin, tare da bayyana cewa babu wata dabara mai sauki da ke iya magance matsaloli masu sarkakiya. Ba tare da la’akari da duk wani sauyi da za a fuskanta ba, kasar Sin za ta tsaya ga neman sulhu da gudanar da shawarwari....
    Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya.   Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince ta bada sama da naira miliyan 156 domin sayen tikitin jirgi na mayar da daliban jihar masu karatun likita har su 184 da suka kammala hutun su a gida zuwa makaranta a kasar Cyprus. Shugaban Hukumar Bada Tallafin Karatu ta Jihar, Alhaji Saidu Magaji, ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, Babban Birnin Jihar. A cewar sa, tuni rukunin farko na dalibai mata su 31 suka tashi ta filin jirgin saman ikko zuwa Istanbul inda za’a dauke su zuwa kasar Cyprus don fara sabon zangon karatu. Alhaji Sa’idu Magaji wanda yake tare da daliban kafin tashin su, ya yaba da kulawar Gwamna Umar Namadi kan tallafawa daliban jihar domin ci gaba da karatun su....
    An shawarci sabbin mataimaka na musamman da su kasance masu adalci da gaskiya wajen aiwatar da ayyukansu a ƙaramar hukumar Auyo ta jihar Jigawa. Shugaban ƙaramar hukumar Auyo, Alhaji Binyaminu Ahmad Adamu Kafur ne ya bayar da wannan shawara yayin bikin rantsar da sabbin mataimaka na musamman 69 da aka gudanar a Auyo. Alhaji Binyaminu Kafur ya sake tabbatar da kudirin majalisar wajen yin aiki tare da masu ruwa da tsaki domin samar da kayayyaki more rayuwa, don tabbatar da ganin kowa ya  amfana da mulkin dimokuraɗiyya. Ya yi kira ga jama’a da kada su gaji wajen yin addu’a domin samun nasarar shugabanni wajen aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwarsu. Shi ma a...
    Shugaban tsangayar Kula da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu A Kwalejin Likitanci Ta Ƙasa (NPMCN), Farfesa Ayodeji Oluwole, ya bayyana hanyoyin da shirin ke bi wajen aiwatar da aikin: ” Wannan horo ya samar wa likitocinmu da fasaha ta zamani, kuma a cikin shekaru biyar, muna sa ran raguwar mutuwar mata masu juna biyu. “Babban abin da ake buƙata shi ne a rage yawan mace-macen mata masu ciki a Nijeriya da Afirka, mun horar da likitoci kusan 220 da masu ba da shawara 140 a duk yankuna shida na siyasa. “A yanzu haka, likitocin suna samun horo a babban asibitin ƙasa dake Abuja; hakan na da matuƙar muhimmanci wajen cimma manufofin gwamnatin tarayya na kula da lafiyar mata masu juna...
    Gwamnatin kasar Sin ta mika sabon kason tallafin abinci ga Zimbabwe, a wani mataki na bunkasa ikon kasar na samar da isasshen abinci ga al’ummarta, bayan matsanancin tasirin yanayin El-Nino da ya haifar da fari a shekarar bara. Yayin bikin mika kayan abincin a jiya Alhamis, wanda aka gudanar a birnin Harare fadar mulkin Zimbabwe, mataimakiyar ministan ma’aikatar kyautata rayuwa, kwadago da walwalar al’umma a kasar Mercy Dinha, ta jinjinawa tallafin na Sin, wanda ya kunshi kimanin tan 3,000 na shinkafa da alkama, kayan da ta ce za su taimakawa ‘yan kasar mafiya fama da kunci. A nasa bangare kuwa, jakadan Sin a Zimbabwe Zhou Ding, ya jaddada aniyar kasar Sin ta taimakawa Zimbabwe, wajen cimma nasarar wadatar da al’umma...
    Wannan irin jita-jitar tana kokain zana shi da kwatankwacin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani rikici da ya ɓarke ya yi sanadin mutuwar wani manomi mai suna Irmiya Yohanna, mai shekara 40, tare da hallaka shanu da tumaki 39, a ƙauyen Kaduna da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, a Jihar Bauchi. Haka kuma  ’yan sanda sun ceto shanu 249 da aka yi ƙoƙarin kashewa. Obi ya ziyarci Bauchi, ya ba da tallafin N15m don inganta ilimi PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Kakakin ’yan sandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya bayyana cewa, a ranar 7 ga watan Agusta 2025, Irmiya ya tafi gonarsa amma bai dawo gida ba. Bayan yin bincike, aka gano gawarsa a kwance a gonarsa. Bayan samun rahoto daga Sarkin ƙauyen, Emmanuel Bulus, ’yan sanda ƙarƙashin...
    Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a fannonin hidimar gida da masana’antu da kayan ajiya. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dabbobi 199 da aka sace (shanu 161 da tumaki 68) Motoci guda 3 da aka sace Babura 2 da ake zargi an sace su Miyagun ƙwayoyi da yawa ciki har da tabar wiwi Wayoyin wutar lantarki da aka lalata DSP Aliyu ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da al’ummar jihar saboda haɗin kai da suka bayar, yana mai cewa ba za a cimma nasarorin ba tare da taimakon jama’a ba. Ya buƙaci al’umma su ci gaba da bai wa ‘yansanda goyon baya, tare da kai rahoton duk wani abun zargi ta waɗannan layukan gaggawa: 0815697777722, 0902220969033, da 07072722539. “Rundunar ‘Yansandan Jihar Katsina za ta ci gaba da ƙoƙarinta don kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar,” in ji shi....
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce ma’aikatar harkokin wajen kasar, da ofishin jakadancin kasar a Philippines, sun gabatar da korafi da babbar murya dangane da kalaman da aka jiyo jagoran Philippines na yi game da batun yankin Taiwan na Sin. Kakakin wanda ya bayyana hakan a Juma’ar nan, ya ce, yayin ziyarar da ya gudanar a kasar India, shugaban na Philippine ya shaidawa ‘yan jarida cewa, idan har yaki ya barke tsakanin Sin da Amurka, tabbas kasarsa za ta shiga, saboda kasancewarta a kewayen yankin, da ma ‘yan Philippines da dama dake zaune a Taiwan, wadanda ya zama wajibi a aiwatar da matakan mayar da su gida. Jami’in Sin ya kara da cewa kasar Sin daya ce tak...
    Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci Jihar Bauchi tare da ba da tallafin Naira miliyan 15 don tallafa wa harkar ilimi. Obi, ya sauka a filin jirgin sama na Abubakar Tafawa Balewa da misalin ƙarfe 9:40 na safe. Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe Bayan saukarsa ya wuce Makarantar Kiwon Lafiya da Koyon Aikin Jinya da Ungozoma ta Malikiya da ke Bauchi. A yayin ziyarar, Obi ya gana da ɗaliban makarantar, inda ya roƙe su da su dage wajen karatu domin aikin jinya da kula da lafiya yana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban ƙasa. Ya ce: “A yau, nasarar...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33. Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu. Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da...
    A cewarsa, wannan gamayyar ta faro ne sama da wata 18 da suka wuce, wadda kuma an samar da ita ne saboda fargabar da ake da ita a ƙasar na kar a kasance ana da jam’iyya ɗaya tilo a Nijeriya. Lukman, wanda kuma shi ne tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma kafin ya sauya sheƙa zuwa ADC, ya koka kan yadda gwamnatin Kaduna ba ta kula da haƙƙoƙin ma’aikatan jihar da rashin biyan ‘yan fansho haƙƙoƙinsu da ƙalubalen rashin tsaro wanda hakan ke hana manoma zuwa gonakansu. Ya soki tsarin rabar da takin zamani na gwamnatin jihar ke gudanarwa ba tare da ta magance ƙalubalen rashin tsaro ba daga tushe. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna...
    Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya tattauna batutuwa da dama a wata zantawa ta wayar tarho da shugaban Rasha Vladimir Putin. Ofishin shugaban kasar Afirka ta Kudu ya ce, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, shugaban kasar ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan rikicin Ukraine da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Ofishin shugaban kasar Afirka ta kudu ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, “Tattaunawar ta biyo bayan bukatar shugaba Putin na yiwa shugaba Ramaphosa bayanin shirin zaman lafiya da Ukraine da kuma magance batutuwan da suka shafi moriyar juna.” Share 0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {}...
    Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF), ta kai hare-hare ta sama a yankin Rann, wani gari da ke Jihar Borno, wanda ake zargin ya zama mafakar ’yan ta’adda. Wannan aiki na cikin shirin Operation Haɗin Kai, kuma ya yi sanadin hallaka ’yan ta’adda da dama. ’Yan damfara 2 sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Wasu mazauna yankin sun bayyana cewa ’yan ta’addan sun fara guduws bayan yunƙurinsu na kai hari sansanin sojoji ya ci tura. Da suka hangi jiragen yaƙi na sojojin sama, sai suka fara tserewa daga maɓoyarsu, amma an kashe da yawa daga cikinsu ta hanyar ɓarin wuta. Wani mazaunin Rann ya ce da farko sun...
    A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu. Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da damfarar mutane a wajen cirar kuɗi a ATM. Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkareem, ya ce an kama Umar Abubakar mai shekara 24 da Abdulaziz Mohammad mai shekara 25 daga Ƙaramar Hukumar Kumbotso, a Jihar Kano. PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027 Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu An kama su lokacin da suke ƙoƙarin yaudarar wani mutum a wajen ATM na bankin Fidelity da ke Damaturu. Ana zargin matasan da amfani da wasu dabara wajen damfarar mutane ta hanyar nuna kamar suna taimaka musu, amma daga baya sai su sauya musu katin ATM. A wani...
    Jam’iyyar PDP ta ce za ta ɗauki mataki kan wasu mambobinta da ke aikata abubuwan da ke kawo wa jam’iyyar koma baya. Shugabancin jam’iyyar ya fi damuwa da mambobin da ke bayyana goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu don sake tsayawa takara a zaɓen 2027. Isra’ila za ta mamaye ilahirin Zirin Gaza ya koma karkashinta – Netanyahu Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano Mai magana da yawun jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce wasu fitattun mambobin jam’iyyar na yin magana a kafafen watsa labarai tare da ƙalubalantar jam’iyyar. A cewarsa wasu ma suna bayyana shirinsu na taimaka wa jam’iyyar APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Ya ce...
    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya ce kasarsa ta kammala shirin amfani da sojoji wajen mamaye ilahirin Zirin Gaza na Falasdinawa domin ya koma karkashin ikonta. A cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar da safiyar Juma’a, Netanyahu ya tabbatar da shirin inda ya ce, “Sojojin Isra’ila za su shirya karbe iko da Zirin Gaza baki daya sannan a samar wa fararen hula agaji a wajen yankunan da ake gwabza yaki.” Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 Kazalika, wasu majiyoyi biyu daga gwamnatin Isra’ila sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk hukuncin da majalisar tsaron kasar ta yanke zai bukaci...
    Ranar Cutar Daji Ta 2025: Akwai Matakan Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Kansa -Masana Uwargidan Gwamnan Zamfara Ta Zama Sakatariyar Kungiyar Yaƙi Da Cutar Daji “Ta hanyar gudanar da ɗimbin ayyukan noma a Gandun Dazukan wannan ƙasa, zai yi matuƙar ƙara yawan ayyukan masana’antun ƙasar da ke sarrafa amfanin gona domin fitarwa zuwa kasuwannin duniya, don sayarwa”, in ji Ibrahim. Kazalika, Ibrahim wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar manoma ta ƙasa (AFAN) ya jaddada cewa; idan aka samu goyon bayan ma’aikatar aikin noma da samar da wadataccen abinci da kuma goyon bayan sauran hukumomin, hakan zai bayar da damar gyara Gandun Dazukan da ake da su, musamman wajen kare su daga kwararowar hamada. Shugaban ya ƙara da cewa, akasarin noman...