Cibiyar binciken duniyar wata, karkashin hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin, ta sanar da cewa, zuwa karo na 9, kasar Sin ta samar da kasar duniyar wata da jimilar nauyinta ya kai gram 125.42, ga kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha na kasashe daban daban, ciki har da kason kasar duniyar wata da aka raba ma wasu hukumomin bincike 7 na kasashe 6.

Kana bisa gudanar da bincike kan kasar da na’urorin binciken duniyar wata na kasar Sin, wato Chang’e-5, da Chang’e-6, suka dawo da ita, masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin da na sauran kasashe, sun gabatar da sakamakon bincike fiye da 150.

An ce, tsarin da ake bi wajen neman samun kasar duniyar wata, shi ne a mika bukatar samun kasar ta wani shafin yanar gizo mai alaka da ayyukan binciken duniyar wata da sararin samaniya na kasar Sin. Daga baya wasu kwararru na kasar Sin za su tantance bukatar da aka mika, gami da yanke shawara kan ko za a ba da kasar ko a’a.

Ban da haka, bayanan da hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta kasar Sin ta samar, sun nuna yadda masu nazarin kimiyya da fasaha na kasar Sin ke karkata hankalinsu daga binciken labarin kasa na duniyar wata, zuwa na fasahar amfani da albarkatun duniyar wata, da samar da tubali don share fagen aikin gini a duniyar. A cewar wani jami’in hukumar kula da zirga-zirgar kumbuna a sararin samaniya ta Sin, an yi hakan ne don shirya fasahohin da ake bukata wajen gudanar da ayyukan kai mutane duniyar wata, da gina tashar bincike kan duniyar wata, a nan gaba. (Bello Wang)

 

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: a sararin samaniya kasar duniyar wata duniyar wata da na kasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

An shafe wata 8 ana mulki babu mataimakin gwamna a Taraba

Mataimakin Gwamnan Jihar Taraba, Alhaji Aminu Alkali, ya yi ɓatan dabo inda ya shafe tsawon watanni takwas ba tare da an gan shi ba.

Alkali, na fama da rashin lafiya tun a bara wanda hakan ya sa bai sake bayyana a bainar jama’a ba.

Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki

An fara kula da lafiyarsa a Asibitin Ƙasa da ke Abuja, daga baya aka kai shi ƙasar Masar domin ci gaba da jinya.

Gwamna Agbu Kefas, ya naɗa Emmanuel Lawson, ɗaya daga cikin mataimakansa, domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan ofishin mataimakin gwamnan.

A wata wasiƙa da Sakataren Gwamnatin Jiha ya sanya wa hannu, an ce naɗin zai taimaka wajen tabbatar da ingantaccen shugabanci.

Sai dai wasu na ganin Lawson bai cancanci riƙe wannan ofishi ba saboda ba zaɓar shi aka yi ba.

Gwamnati ta ce yana murmurewa

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa Alhaji Aminu Alkali na murmurewa daga ciwon shanyewar ɓarin jiki da ya shafi lafiyarsa da yanayin maganarsa.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Bordiya Buma, ya kai masa ziyara a watan Maris kuma ya ce yana samun sauƙi.

“Muna farin ciki da samun sauƙi da yake yi kuma muna fatan zai dawo nan ba da jimawa ba.”

Sai dai har yanzu bai dawo bakin aiki ba.

Wasu rahotanni na cewa yana Abuja yana ci gaba da jinya, wasu kuma na cewa yana zaune a wani gida a unguwar Wuse.

A gefe guda kuma, ma’aikatansa sun ce ba sa ganinsa ba.

’Yan adawa na neman ba’asi

Wasu ‘yan siyasa da jama’a suna buƙatar gwamnati ta bayyana gaskiyar halin da mataimakin gwamnan jihar ke ciki.

“Mutanen Taraba suna da ‘yancin sanin inda mataimakin gwamna yake da halin da lafiyarsa ke ciki,” in ji Alhaji Hassan Jika Ardo, tsohon shugaban jam’iyyar APC a jihar.

Ya ce gwamnati ta daina wasa da hankalin jama’a a kan batun da dokar ƙasa ta bayyana a fili.

Dalilin da ya sa ba a sauke shi ba

Sashe na 189 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya bayyana cewa za a iya tsige mataimakin gwamna ne kawai idan kwamitin likitoci ya tabbatar cewa ba shi da ƙoshin lafiyar da zai iya kataɓus.

Wannan na buƙatar ƙuri’a daga kashi biyu bisa uku na majalisar zartarwa ta jihar.

Har yanzu ba a ɗauki wannan matakin ba.

Siyasa ta hana a ɗauki mataki

Wasu majiyoyi sun ce ana matsa wa gwamnan jihar lamba kan ya sauke mataimakin nasa, amma yana tsoron kada hakan ya rushe tsarin rabon madafun iko tsakanin yankunan jihar.

Sauya mataimakin gwamnan na iya janyo rikicin siyasa a jihar.

An taɓa fuskantar irin wannan rikici a Taraba

A shekarar 2012, Gwamna Danbaba Suntai, ya yi hatsarin jirgin sama kuma bai samu sauƙi ba na tsawon watanni.

Rikici ya ɓarke saboda ba a bayyana halin da yake ciki ba, kuma bai miƙa wa majalisa wasiƙar cewa ba zai iya ci gaba da aiki ba.

Wannan ya janyo rikici da rarrabuwar kawuna tsakanin masu goyon bayan gwamnan da na mataimakinsa.

Ra’ayoyin lauyoyi sun bambanta

Wasu lauyoyi sun ce lokaci ya yi da gwamnati za ta aiwatar da dokar ƙasa.

“Rashin lafiyar mataimakin gwamna ta shafi ci gaban jihar. Idan ba zai iya aiki ba, ya kamata ya sauka,” in ji lauya mai kare haƙƙin bil’adama, Malachy Ugwumadu.

Amma wani babban lauya, Richard Ahonaruogho (SAN), ya ce jihar ba ta cikin matsala dangane da rashin lafiyarsa.

“Muddin gwamna bai koka cewa ba zai iya aiki ba, babu buƙatar ɗaukar mataki,” in ji shi.

Jama’a sun fara gajiya

Yayin da aka shafe tsawon lokaci babu mataimakin gwamnan, mutane da dama a jihar suna fara nuna damuwa.

Wasu na ganin rashin bayyana gaskiya yana nuna rashin girmama masu kaɗa ƙuri’a.

Yanzu dai idanun mutane sun karkata ne kan gwamnan da majalisar dokokin jihar domin su bayyana gaskiya ko su ɗauki matakin doka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe
  • Gwamnatin Kaduna Ta Amince Da Hutun Wata 6 Ga Mata Masu Shayarwa
  • Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
  • Hizbullah Da Amal Na Kasar Lebanon sun Yi Tir Da gwamnatin Kasar Saboda Bukatar Kwance Damarar Hizbullah
  • Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji
  • Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama
  • Mutanen Kasar Lebanon Suna Tsoron HKI Zata Shiga Kasar Daga Kasar Siriya
  • An shafe wata 8 ana mulki babu mataimakin gwamna a Taraba
  • Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan