Ku Yaƙi Cin Hanci Ba Ƴan Adawa Ba – ADC GA EFCC
Published: 11th, August 2025 GMT
Jam’iyyar ADC ta zargi hukumar EFCC na yin son zuciya tare da yin aiki a matsayin kayan aikin siyasa ga jam’iyyar mai mulki APC. Jam’iyyar ta gargaɗin cewa irin wannan mataki yana rage ingancin yaƙin da ake da cin hanci da kuma rage amincewar jama’a.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar na ƙasa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya fitar, ADC ta bayyana cewa ayyukan EFCC na baya-bayan nan, ciki har da buɗe tsofaffin shari’o’i da kuma maida hankali kan ƴan adawa, sun nuna halayyar kamar ta “mai aiwatar da umarnin siyasa” maimakon hukuma mai aiki da gaskiya.
ADC ta jaddada cewa an kafa EFCC ne domin tabbatar da adalci ta hanyar aiwatar da doka a kan kowane ɗan Nijeriya ba tare da wariya ba, amma yanzu wannan hangen nesan da aka yi ya lalace. Ta zargi hukumar da barin shari’o’in da suka shafi abokan APC su shuɗe ba tare da kulawa ba, yayin da take tsananta bincike kan ƴan adawa, lamarin da ke ƙara tabbatar da ra’ayin cewa alaƙa da jam’iyya mai mulki ne ke tantance wanda za a bincika.
Jam’iyyar ta yi kira ga ƴan Nijeriya, da ƙungiyoyin farar hula da kafafen yaɗa labarai da su ƙi amincewa da duk wata alama ta mulkin kama-karya, ta kuma tunatar da EFCC cewa hukuma ce ta ƙasa wadda ake ɗaukar nauyinta daga harajin jama’a, ba sashi a jam’iyya mai mulki ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wakiliyar CMG Ta Zanta Da Farfesa Jeffrey Sachs Na Jami’ar Columbia
Farfesa Jeffrey Sachs na jami’ar Columbia, ya yaba wa nasarorin da Sin ta samu, inda ya ce, “shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wani shiri ne mai ban mamaki kuma na musamman.”
Farfesa Sachs ya fadi hakan ne a kwanan nan, yayin da wakiliyar rukunin gidan rediyo da talibijin kasar Sin wato CMG ta zanta da shi. Ya kuma bayyana cewa, kamar yadda shugaban kasar Xi Jinping ya fada a karon farko, yayin gabatar da wannan shawara, tushen ta ya samo asali ne daga hanyar kasuwanci ta hanyar siliki, hanyar dake da tarihin fiye da shekaru dubu biyu tsakanin yankin gabas da yamma. Ya ce, “Idan kina nazarin tattalin arziki kamar yadda nake yi, za ki yi imanin cewa, ainihin ciniki shi ne samun moriyar juna, da habaka al’adu, da samar da ingantattun kayayyaki, wanda ke amfanar mutane daga sassa daban-daban na duniya, to za ki amince cewa ciniki shi ne tsarin gaskiya na samun riba ga kowa. Ina goyon bayan wannan ra’ayi na hadin kai, kuma na yi imanin cewa yana da fa’ida mai yawa. Shirin Sin na tabbatar da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ cikin hadin gwiwa, ya yi kokari sosai a fannin inganta hadin kai da kara zurfafa mu’ammala.” (Amina Xu)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA