Runduunar ‘Yan Sandan Jihar kwara Ta Karfafa Tsaro A Banbila
Published: 11th, August 2025 GMT
Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta ce ta karfafa matakan tsaro a yankin Babanla biyo bayan harin da wasu da ake zargin mahara ne suka kai musu, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda, SP Adetoun Ejinre-Adeyemi ya fitar, ya ce ‘yan fashi da makami da yawansu ya kai daruruwa, a kan babura, sun mamaye al’ummar Babanla a karamar hukumar Ifelodun.
A cewarsa wadanda ake zargin sun kai hari ne a hedikwatar ‘yan sanda inda suka kai farmaki cikin kasuwar.
Ya bayyana cewa maharan sun yi ta harbe-harbe kai-tsaye, inda suka kashe mutane 5 ciki har da dan sanda Adejumo Wasiu.
Sanarwar ta ce jami’an ‘yan sanda, jami’an Sojin Najeriya, ‘yan banga, da mafarauta cikin gaggawa sun dakile harin, tare da dawo da zaman lafiya, tare da fara farautar wadanda suka kai harin.
Ya yi nuni da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kwara, Adekimi Ojo, tare da rakiyar daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), sun kai ziyarar tantancewa Babanla domin tantance yanayin tsaro.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, an samar da wani babban tsari domin tabbatar da zaman lafiya da karfafa hadin gwiwa tsakanin hukumomi da tsaro a cikin al’ummar da lamarin ya shafa.
Ta ce tawagar jami’an tsaron hadin gwiwa sun zagaya muhimman wurare a cikin al’umma – ciki har da kasuwa, da hedikwatar ‘yan sanda, da kewaye domin tabbatar da cewa an samu kwanciyar hankali.
REL/ALI MUHAMMAD RABIU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa
Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya.
“Manufar taron ita ce samar da matsaya ɗaya wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke damun yankin, tare da tsara hanyar magance su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, za a yanke muhimman shawarwari a taron domin tabbatar da tsaron yankin.
’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a KatsinaAhemba ya bayyana cewa, sakamakon ƙalubalen tsaro da wasu jihohin Arewa ke fuskanta, gwamnatin Nasarawa ta ɗauki matakan gaggawa ta hanyar shirya taron tsaro na musamman, inda za a yanke shawarar da za ta kare jihar daga duk wata barazanar tsaro.
“Ya zama wajibi ga ’yan ƙasa su taka rawa wajen magance barazanar tsaro a ƙasarmu da jihohinmu. Don haka, dole ne jama’a su riƙa ba wa hukumomin tsaro bayanai kan mutanen da ke da halin aikata laifi,” in ji shi.