NDLEA Ta Kama Fasto Bisa Laifin Safarar Miyagun Kwayoyi A Legas
Published: 10th, August 2025 GMT
Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ta kama wanda ya kafa kuma yake kula da cocin ‘The Turn of Mercy’, Adefolusho Olasele, wanda aka fi sani da Abbas Ajakaiye, bisa zarginsa da hannu wajen safarar miyagun kwayoyi da dama daga Ghana zuwa Nijeriya. Fasto Olasele, wanda ya shafe watanni ba a san inda yake ba, an kama shi ne a ranar Lahadi, 3 ga watan Agusta, 2025, a cocinsa da ke Okun Ajah, yankin Lekki, a Legas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Wata mata ta kashe ’yar shekara 7 a Ribas
Ana fargabar cewa wata mata mai suna Success ta kashe wata yarinya mai shekaru bakwai, Alicia Olajumoke, a unguwar Rumueme da ke birnin Fatakwal na Jihar Ribas.
Mazauna yankin sun shaida wa Aminiya cewa matar da ake zargin tana da kusanci da dangin mahaifiyar yarinyar, wacce ita kaɗai ce a wurin iyayenta.
El-Rufai ya koma jami’yyar haɗaka ta ADC An janye ’yan sanda 11,566 daga gadin manyan mutane a faɗin NijeriyaBayanai sun ce ita ma matar ta caka wa kanta wuƙa a wuya bayan kashe yarinyar, kuma bayan an garzaya da duk su biyun asibiti, likitoci suka tabbatar da cewa sun riga mu gidan gaskiya.
Lamarin wanda ya faru a ranar Talata ya ɗimauta mazauna yankin, la’akari da zargin cewa matar ta kashe yarinyar ce a gidanta bayan ta je har makarantarsu ta ɗauko ta ba tare da izinin mahaifiyarta ba.
Jami’ar hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ta fitar ranar Alhamis, inda ta ce an kai gawar yarinyar ɗakin ajiye gawa domin bai wa likitoci damar kammala bincikensu na kimiyya gabanin soma nasu binciken.
“Mun ziyarci wurin da abin ya faru, mun ɗauki hotuna, kuma an garzaya da su asibiti inda aka tabbatar da mutuwarsu.”