2025-08-05@11:22:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 6127

«kwallon kwando»:

    Tosin Demehin ta nuna godiya da jin daɗinta, tana mai cewa wannan girmamawa daga jiharta na ƙarfafa mata gwuiwa da sauran ’yan mata masu burin taka leda a matakin duniya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ta kafa kwamitin tsaron kasa, wanda zai kula da sabbin matsalolin tsaron kasa, da kuma da kuma karfin sojojin kasar . Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa an kafa kwamitin ne tare da dogaro da duka da 176 da kundin tsarin mulkin kasar. Labarin ya kara da cewa , kafa kwamitin wani mataki ne, na kyautata harkokin tsaron kasar, da kuma samar da mafita ga wasu sabbin matsalolin tsaro wadanda kasar take fuskanta. Da kuma tabbatar da cewa jami’an tsaron kasar a shirye suke su fuskanci duk wata barazanar tsaron da zasu bullowa kasar nan gaba. Banda haka kwamitin shine zai shirye dabarbarin kare kasar tsakanin bangarori daban0daban na sojojin...
    Gwamnatin kasar Burtaniya ta bayyana cewa zata fara amfani da wata yarjeniya da ta cimma da kasar Faransa kan maida dukkan yan gudun hijira ko bakin hauren da suke shigo kasar ta kwale-kwale zuwa kasar kasar ta Faransa. Daga yau Talata. Shafin labarai na yanar gizo Arab News ya nakalto cewa gwamnatocin biyu sun amince kan cewa Burtaniya zata maida dukkan wadanda suka iso Burtaniya ta amfani da kananan kwale kwale ta maida su Faransa, a inda ita kuma faransa zata mikawa kasar Burtaniya masu nrman mafaka wadanda suke da iyali a kasar Burtaniya dai dai adadin da ta mayar daga Burtaniya. Firai ministan kasar Burtanita Keir Starmer da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel macron sun amince haka a cikin...
    Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi. Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.” Mallam Yunusa ya ce, “Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a  da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata. Ya bayyana cewa makwabta da zuwan jami’an sun taimaka an aka fitar da motar da ke  garejin zuwa waje, amma an tafka asara. Sa’in yace “Muna addu’ar Allah Ya Maida...
    Tsohon jami’in harkokin wajen Tarayyar Turai Joesp Borrell, ya yi gargadi game da ci gaba da rashin taka rawar gani daga bangaren kasashen Turai dangane da ayyukan cin zarafin da Isra’ila ke ci gaba da yi, yana mai cewa irin wannan rashin hankali ya sa kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta zama abokiyar tarayya a cikin laifukan da Isra’ila ke aikatawa. Joesp Borrell ya bayyana hakan ne a cikin wani fashin baki wanda aka buga a cikin jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya. “Wadanda ba su yi aiki ba don dakatar da wannan kisan kiyashi da kuma keta dokokin kasa da kasa, duk da cewa suna da ikon yin wani abu kan hakan, to tabbas suna da hannu a cikin wadannan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wata tawagar jami’an tsaron Isra’ila da suka yi ritaya su 600 ciki har da tsaffin shugabannin hukumomin leƙen asiri sun aika wa Shugaban Amurka, Donald Trump wasiƙa domin neman ya matsa wa Isra’ila da ta gaggauta kawo ƙarshen yaƙin da ake a Gaza. Jami’an sun ce “tunaninmu ne cewa Hamas ta daina zama wata barazana ga Isra’ila”. “Amincin da kake da shi a wajen Isra’ilawa zai ƙara ba ka damar sanya Firaiminista [Benjamin] Netanyahu da gwamnatinsa a kan hanya daidaitacciya: A kawo ƙarshen yaƙin, a dawo da mutanen da ke tsare a kuma daina gallaza wa Falasɗinawa,” kamar yadda suka rubuta. Roƙon nasu na zuwa ne daidai lokacin da rahotanni ke cewa Netanyahu na ƙoƙarin faɗaɗa ayyukan soji a Gaza...
    Gwamnatin tarayya ta ce tace a shirin ta sauya wuraren dake bushe a sassan arewacin Nijeriyaza a raba naira miliyan  miliyan 3.4 kuma akasarin wadanda zasu amfana da wannan za su kasance mata ta hanyar Shirin ACReSAL.   Da yake jawabi a wajen bude taron kwanaki 10 na masu ruwa da tsaki kan tsarin kula da tsare-tsare (SCMP) na sabbin magudanan ruwa guda 11 a fadin Jihohi bakwai na tarayya a Ilorin, kodinetan ayyukan ACRESAL na kasa, Mista Abdulhamid Umar, ya ce za a gudanar da aikin ne ta hanyar shirin kawo sauyi na dogon lokaci.   Jami’in kula da ayyukan na kasa na ACRESAL Adamu Shettima wanda ya samu wakilcin kwararre a bangaren kula da ayyukan ruwa na gwamnatin...
    Kwalejin Horasda Hafsoshin Soja ta Kasa dake Kaduna -NDA ta karyata jerin sunayen wadanda suka yi nasara shiga kwalejin dake yawo a halin yanzu.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na makarantar, Manjo Mohammed Maidawa ya fitar ya ce jerin sunayen ba su fito daga Kwalejin NDA ba.   Don haka ya shawarci jama’a da su yi watsi da jerin sunayen da aka zayyana, domin za a buga sahihan jerin sunayen a cikin fitattun jaridu na kasa da kuma a yanar gizon NDA a kan https://NDA.edu.ng/, a lokacin da ya dace.   PR/Usman Sani.
    Kungiyar masu fafutukar tabbatar da zaman lafiya da kishin kasa reshen jihar Nasarawa ta kalubalanci kungiyar tabbatar da gaskiya da rikon amana da shugabanci na gari (NS-TA&G), da su tabbatar da zargin nuna son kai wajen sauke nauyin da babban Akanta Janar na jihar, Ahmed Musa Mohammed ke yi.   Ko’odinetan kungiyar na jiha Abimiku Dangana Solomon ne ya bayyana hakan a lokacin da yake mayar da martani ga wani jawabi da Mista Lazarus Salaki, ko’odinetan kungiyar NS-TA&G2 na jihar ya yi a wani taron manema labarai da aka gudanar a garin Lafia babban birnin jihar.   Mista Abimiku Dangana ya ce, hukuncin da kotun koli ta yanke na baya-bayan nan bai hana masu rike da mukaman gwamnati da ma’aikatan...
    Gwamnatin Tarayya ta gabatar da karramawar kasa da kuma tukuicin kudade ga kungiyar kwallon Kwando ta mata ta Najeriya, D’Tigress, bayan nasarar da suka samu a gasar cin kofin kwallon kwando na mata ta FIBA karo na biyar a jere.   A wata liyafar karrama su da aka yi a fadar shugaban kasa, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, mai wakiltar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa kowane dan wasa zai karbi dala 100,000, yayin da koci da kungiyar kwararru za su samu dala 50,000 kowanne, tare da karramawar kasa ga daukacin kungiyar. Ya kuma yi alkawarin karin tukuicin da zai zo.   Shettima ya ce ba wai don murnar nasarar da kungiyar ta samu a cikin shekaru 78-64...
    Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya raba wa sabbin ma’aikatan aikin gona 1,038 da aka dauka aiki takardun su na kama aiki.   Bikin, ya gudana ne a gidan gwamnatin Kano.   Da yake jawabi yayin bikin gwamnan ya gargade su da su guji cin hanci da rashawa, ya kuma bukace su da su yi wa jihar hidima cikin himma da gaskiya.     Ya ce matakin ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin da jihar ke yi na inganta samar da abinci da kuma habaka arzikin iyali.     Gwamna Yusuf ya bayyana daukar ma’aikata a matsayin cika alkawuran da ya dauka a lokacin yakin neman zabe da kuma wani muhimmin mataki na cimma wadannan manufofin.  ...
    Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle. Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu. Jami’in Sadarwar Zamani na Gwamnatin Jihar Yobe, Yusuf Ali, ya bayyana cewa Rukayya ta samu kafa wannan tarihi ne a dalilin zurfin tunani da kuma kaifin basirarta da kuma fahimtar al’amuran duniya, duk kuwa da ƙarancin shekarunta. Ɗalibar daga Kwalejin Nigerian Tulip International (NTIC), Rukayya, ta ɗauki hankalin alƙalan gasar da sauran jama’a saboda ƙarfin hujjojinta da ta gabatar da kuma iya bayani mai ganawarsa...
    Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fada a ranar Litinin cewa kimanin yara 28 ne ake kashewa a kullum a zirin Gaza sakamakon harin bama-baman Isra’ila da kuma yunwar da ta jefa a l’ummar yankin a ciki. Kungiyar ta yi bayanin a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa, yaran Gaza na fuskantar kisa “sakamakon tashin bama-bamai, rashin abinci mai gina jiki, yunwa, da kuma rashin muhimman kayan agaji da ayyukan kiwon lafiya. UNICEF ta jaddada cewa yara a Gaza na bukatar abinci, ruwa, magunguna, da kuma kariya. Mafi mahimmanci kuma shi ne, suna bukatar tsagaita bude wuta cikin gaggawa.” A wani labarin kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahoton cewa, sama da mutane...
    Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ba wa ɗalibar nan ’yar shekara 17 daga Jihar Yobe da ta lashe Gasar Turanci ta Duniya, Nafisa Abdullah Aminu, kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa ta OON. Ya buƙaci a gayyato Nafisa da malamanta na harshen Turanci musamman zuwa Fadar Shugaban Ƙasa a karrama su saboda yadda suka ɗaga sunan Najeriya a idon duniya a fannin ilimi. “Ina kira da babbar murya cewa a a ba wa Nafisa kyautar tsabar kuɗi Dala 100,000 da gida da kuma lambar girmamawa daga Gwamnatin Tarayya.” A cikin saƙon da ya wallafa a safiyar Talata, Pantami ya ƙara da cewa malaman Nafisa sun cancanci irin kyautar...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yaba da ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasar Masoud Pezeshkian ya kai a Pakistan, wanda a sakamakon an bude wani sabon shafi na karfafa alaka mai karfin gaske tsakanin Iran da Pakistan da suke makwabtaka da juna. “Ziyarar shugaban kasar Pakistan na da matukar muhimmanci,” in ji Esmaeil Baghaei yayin wani taron manema labarai na mako-mako a ranar Litinin a birnin Tehran, yayin da yake magana kan ziyarar Pezeshkian. Baghaei ya ba da misali da matsayar  da kasashen suka dauka na yin ciniki cikin ‘yanci bisa yarjejeniyar da ta dace a matsayin wani muhimmin batu na ziyarar, yana mai cewa wannan lamari mai matukar muhimmanci ga bangarorin biyu. Ya kara da cewa, yayin ziyarar, an...
    Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida da kashi 30% na bangaren da harajin Amurka ya shafa a wannan makon, tare da kebe wasu ka’idojin samun wannan tallafin kudi. Kasar mafi karfin tattalin arziki a Afirka ta kwashe watanni tana kokarin tattaunawa da Washington, inda ta yi tayin sayen iskar gas na Amurka da kuma zuba jarin dala biliyan 3.3 a masana’antun Amurka a wata yarjejeniya da tawagar shugaban Amurka Donald Trump ta gabatar. Wannan yunƙurin ya ci tura. Jami’an Afirka ta Kudu sun ce, a cewar kamfanin dillancin labaran  Reuters, harajin Amurka zai iya janyo asarar dubunnan ayyuka, musamman a fannin noma da kera motoci. A wani taron manema labarai, ministocin ciniki da...
    Wata yarinya ’yar shekara 17, Nafisa Abdullah, daga Jihar Yobe, ta lashe Babbar Gasar Harshen Turanci ta Duniya ta ‘TeenEagle’ ta shekarar 2025 da aka gudanar a birnin Landan, fadar gwamnatin  ƙasar Birtaniya. Nafisa ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 ce baya da ta fafata ne da sama da mahalarta gasar 20,000 daga ƙasashe kusan 69 na duniya, inda ta zama ta ɗaya a Gasar ‘UK Global Finals’, sakamakon fintinkau da ta yi wa takwarorinta na ƙasashe daban-daban da ke jin harshen Ingilishi a duniya. Wannan nasara ta lashe wannan babbar gasa da Nafisa ta samu ya haifar da alfahari a faɗin Najeriya, musamman a mahaifarta, Jihar Yobe. Nafisa ta wakilci Najeriya ne daga Kwalejin Tulip International College (NTIC), Jihar Yobe....
    Kungiyar Hamas, ta musanta kalaman da wakilin Amurka Steve Witkoff, inda ya yi ikirarin cewa kungiyar ta bayyana aniyar ta na yin watsi da makamanta. Kungiyar ta tabbatar da cewa, tsayin daka da makamanta hakki ne na kasa kuma na shari’a matukar dai an ci gaba da mamaye Falastinu, kuma dukkanin dokoki na kasa da kasa sun amince da hakan a ka’idojin MDD. Kungiyar ta jaddada cewa, “wadannan makamai ba za a yi watsi da su ba sai ta hanyar dawo mana da cikakken ‘yancinmu na kasa, wato kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci, mai cin gashin kanta tare da Kudus a matsayin babban birninta.” A baya can, Hamas ta zargi Witkoff da gudanar da wani shiri a ziyarar da...
    Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar ya ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobi da kuma takin zamani kyauta ga al’ummar mazaɓarsa. Da yake ƙaddamar da allurar rigakafin dabbobin garin Goɗɗiya da ke Ƙaramar Hukumar Bogoro, Sanata Buba ya ce, “A bana, za mu yi allurar rigakafin dabbobi 85,000 a wannan yankin na Majalisar Dattawa.” Ya ce a baya an yi wa dabbobi kimanin 40,000 allurar rigakafin a fadin yankin. “Na yi imanin cewa wannan abu ɗaya ne daga ayyukan wakilci wa mutanenmu manoma da makiyaya. ’Yan Najeriya ne kamar mu duka, suna zaɓe mu, kuma suna ba da gudummawa sosai ga tattalin arzikin ƙasar nan. “Wannan ba wani abu ba ne na musamman amma na yi imanin cewa wani abu...
    Gwamnan Kaduna, Malam Uba Sani, ya gargadi ’yan siyasa da masu amfani da kafafen sada zumunta da su daina zagin malaman addini da a yanzu ya zama ruwan dare a ƙasar nan. Gwamnan ya bayyana cewa irin wannan mummunar ɗabi’a ta cin zarafi malaman addini na iya lalata zamantakewa da tubalin zaman lafiya a tsakanin al’umma. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin tattaunawarsa da malaman addini da na gargajiya a birnin Kaduna, inda ya jaddada muhimmancin rawar da shugabannin addini ke takawa wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai. Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata kyautar Dala dubu 100 da gidaje Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu “Ina...
    Hukumar Yaki da Hamada da Sauyin Yanayi ta Kasa ta kammala shirye-shiryen dasa itatuwan dabino miliyan hamsin (50,000,000) a jihohi goma sha ɗaya 11 da ke fama da fari a Najeriya. Daraktan Hukumar, Alhaji Salihu Abubakar ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin dasa itatuwan dabinon da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar Jigawa. Ya ce za a dasa itatuwan dabino guda dubu dari biyar (500,000), tare da wasu nau’o’in itatuwa na gida a faɗin jihar Jigawa. Alhaji Salihu Abubakar ya yi kira ga jama’a da su rungumi al’adar dasawa da kula da itatuwa domin magance matsalolin hamada, zaizauar ƙasa da sauyin yanayi. A cewarsa, Hukumar tana aiki tukuru a jihohin da ke  fama da fari a...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaba Bola Tinubu ya bai wa ’yan wasan ƙwallon kwandon mata D’Tigress kyautar Dala dubu 100 da gidaje da lambar girmamawa ta OON, a matsayin karramawa bayan lashe kofin gasar ta bana. Shugaban ya kuma ba masu horar da ’yan wasan dala 50,000 kowannensu. Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton binciken Kwamishinan da ya yi belin Danwawu WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025 Wannan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan shugaban ya ’yan wasan ƙwallon ƙafa mata wata Super Falcons makamanciyar wannan kyautar ta dala 100,000 da lambar girma. A wannan Litinin din ce tawagar ’yan wasan ƙwallon kwando ta mata ta Nijeriya ta koma ƙasar bayan lashe gasar ƙwallon kwando ta mata ta Afirka, wato Afrobasket. Tawagar ta D’Tigress ta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da ta kafa domin gano haƙiƙanin gaskiya kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na jihar, Ibrahim Ali Namadi da shiga sha’anin belin wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi. Shugaban kwamitin, Barista Aminu Hussain, ne ya miƙa rahoton ga Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa sun gudanar da cikakken bincike na adalci, tare da tuntubar dukkan masu ruwa da tsaki. WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025 Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano Babu dai cikakken bayanin abin da rahoton ya ƙunsa, to sai dai matakin da gwamnati za ta ɗauka ne zai...
    Jaridar Le Monde ta bayyana cewa: Tallafin kayan da jiragen sama suke saukarwa a Gaza tamkar digon ruwa ne idan aka kwatanta girman bukatun al’ummar yankin Jaridar Le Monde ta ruwaito cewa, ko da yake hukumomin mamayar Isra’ila, a karkashin matsin lamba na kasa da kasa, sun ba da izinin saukar da kayan agajin abinci ta hanyar jiragen sama, amma adadin tallafin takaitacce ne da ba zai magance wata matsala ba. Le Monde ta kara da cewa: Sakamakon ya bayyana takaitacce ne a daidai lokacin da dubban manyan motoci makare da kayan agaji ke makale a wajen zirin Gaza. Jaridar ta yi bayanin cewa kasashe da dama da suka hada da Jordan, Hadaddiyar Daular Larabawa, Faransa, da Birtaniya, sun fara...
    Rundunar sojin kasar Sin (PLA) ta yi sintiri a yankin tekun kudancin Sin daga ranar 3 zuwa 4 ga wata. Kakakin rundunar PLA ta kudancin kasar Tian Junli ya bayyana a yau Litinin cewa, kasar Sin ta dauki matakin ne biyo bayan matakan Philippines na sanya kasashen dake wajen yankin cikin abun da ta kira da sintirin hadin gwiwa, wanda ke neman lalata zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin. A cewarsa, dakarun rundunar ta kudancin kasar za su ci gaba da kasancewa cikin shirin ko-ta-kwana da kare ikon kasar kan yankunanta da muradunta na teku ba tare da yin kasa a gwiwa ba, yana mai cewa za a dakile duk wani matakin soja dake nemen tada hankali da rikici a...
    Bayanin da Hukumar Haraji ta Kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a rabin farko na wannan shekara, kudaden cinikin da kamfanoni a duk fadin kasar suke samu ya ci gaba da karuwa cikin kwanciyar hankali. Masana’antu sun sami ingantaccen ci gaba yayin da manufofin “sabunta manyan kayan aiki na kasa” da “Maye gurbin kayan amfani da suka tsufa da sababbi” suka yi tasiri sosai. Kudin da aka samu a bangaren sana’ar kere-kere ya karu da sauri fiye da matsakaicin karuwar dukkan kamfanoni da kashi 1.5%. Wannan ya tabbatar da cewa masana’antu su ne tushen karfafa tattalin arzikin kasar. Kazalika, masana’antun kirkire-kirkire sun kara habaka, inda kudaden da aka samu a bangaren sayar da kayayyaki na masana’antun kimiyya mai inganci ya...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An nemi wata jaririya sa’o’i kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin. Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da...
    An nemi wata jaririya saoi kaɗan bayan haihuwarta an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririyar ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarta da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririyar da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin. Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririyar da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar da ke shirya jarabawa kammala karatun sakandire a Afrika ta Yamma (WAEC), ta saki sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2025. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 4 ga Agustan 2025, tana mai cewa dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar yanzu za su iya duba sakamakon nasu a shafinta na intanet. Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti “WAEC na farin cikin sanar da ɗalibai da suka rubuta jarabawar WASSCE a shekarar 2025 cewa an saki sakamakon a hukumance yau Litinin, 4 ga watan Agusta,” in ji sanarwar. WAEC ta buƙaci ɗalibai da su shiga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Kano ta bayyana shirin mayar da tsohon gidan yarin nan na Kurmawa, wanda aka gina fiye da shekara 100 da suka gabata, zuwa gidan adana abubuwan tarihi. Gidan yarin Kurmawa mai ɗaukar fursunoni 690 kacal, wanda aka gina a shekarar 1910 tun a zamanin Turawan mulkin mallaka a kusa da fadar mai martaba Sarkin Kano, yana da tarihin shekaru 115. An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ibrahim Adam, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi. Hadimin gwamnan ya ce an yanke shawarar sauya ma’anar wurin,...
    Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu. Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki, Barrister Aminu Hussain, ne ya mika rahoton ga Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim. Barrister Hussain ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci, da kuma bin hujjoji, ba tare da son rai ba. Ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinan Sufuri domin karin bayani, inda ya kuma gabatar da rubutaccen jawabi ga kwamitin. Sauran da aka tattauna da su...
    An nemi wani jariri sabuwar haihuwa an rasa a Cibiyar Lafiya ta Okeyinmi da ke Ado-Ekiti, babban birnin Jihar Ekiti, a ranar Litinin. Wani ganau ya ce an gano ɓatan jaririn ne lokacin da ma’aikatan jinyar da ke bakin aiki suka je su duba lafiyarsa da safiyar wannan Litinin ɗin. Za a samu ruwan sama kamar da bakin ƙwarya na kwanaki uku a faɗin Nijeriya — NiMet Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Lamarin na ba-zato-ba-tsammani ya haifar da fargaba musamman yadda ɗimauta uwar jaririn da kuma wasu daga cikin mutanen da ke cikin harabar asibitin. Tuni dai an garzaya da ma’aikatan da ke kula da ɗakin haihuwa da uwar jaririn da mai gadi...
    Sakamakon wannan mummunan ta’annuti, Mataimakin Gwamnan ya jagoranci wata ƙaƙƙarfar tawaga, wacce ta haɗa manyan ma’aikatan gwamnati da jami’an tsaro zuwa Banga da sauran wurare uku da waɗannan hare-hare ya shafa, don a jajanta masu, tare da ba su tallafi na abinci da kuɗaɗe.   Mataimakin Gwamnan ya kuma tabbatar wa da waɗannan al’ummu cewa gwamnatin na nan tana duk abin da za ta iya yi don kawo dawwamammen zaman lafiya a yankin.   Lokacin da ya ke mayar da jawabi, shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, Manir Haidara ya yaba da ƙoƙarin gwamnatin jihar na ganin ta samar da tsaro a duk faɗin jihar Zamfara. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
    Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya amince da ware Naira Biliyan 20 a karin kasafin kudin da aka yi domin ci gaba da gyaran gine-ginen makarantu a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimi na jihar, Dr. Lawal Olohungbebe, ya fitar, ya ce wannan sabon tsarin zai kara karfi wajen cigaban gyaran makarantun gwamnati. Sanarwar ta bayyana cewa tuni aka fara aikin, inda aka  zayyana yadda gine-ginen za su kasance, kuma sauran abubuwa za su biyo baya da zaran an amince da karin kasafin kudin. Sanarwar ta kara da cewa wannan ba wani aiki ne mai zaman kansa ba, illa wata sabuwar babbar gudummawa daga gwamnati don kara habaka aikin da take yi tun da farko. Ta kara...
    Hukumar Hasashen Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi gargaɗin cewa za a yi ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da tsawa na kwaki uku a faɗin ƙasar daga ranar Litinin. NiMet ta fitar da wannan hasashen ne ranar Lahadi a Abuja, lamarin da ke ƙara barazanar ambaliya a wasu jihohin ƙasar. Shirin kashe N712bn kan gyaran filin jirgin Legas ya tayar da ƙura Najeriya na hasashen samun N300bn a shekara daga noman dabino Hasashen na zuwa ne bayan ruwan sama ya lalata gidaje kimanin 50 da gonaki da wuraren ibada a Jihar Filato. Hukumar ta yi hasashen cewa za a yi tsawa da ruwan sama a jihohin arewacin ƙasar da suka haɗa da Adamawa da Taraba da Sakkwato da Kebbi...
    Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri. Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na da nufin inganta lafiyar mata da yara tare da rage mace-macen da za a iya kauce wa ta hanyar samar da dama ga ayyukan kiwon lafiya. Cibiyoyin lafiya a fadin karamar hukumar, ciki har da Asibitin Gwamnati na Gwarzo da Asibitin ‘Yar Kasuwa, sun bayar da rigakafi kyauta, shawarwari kan abinci mai gina jiki, kulawar haihuwa da sauran muhimman ayyuka na kiwon lafiya. Jami’in...
    Gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni ya tuhumi sabon Sarkin Gudi, Alhaji Ismaila Ahmed Gadaka da ya jagoranci zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban al’ummar masarautar sa, jiha da kasa baki daya. Gwamna Buni ya yi wannan kiran ne a ranar Litinin yayin gabatar da takardar nadin sarauta ga basaraken a hukumance a majalisar masarautar Gudi. Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule Wasu Kungiyoyi Sun Yi Kira Ga Dan Majalisa Aminu Sani Jaji Ya Fito Takarar Gwamnan Zamfara  Kwamishinan ilimi mai zurfi, kimiyya da fasaha na jihar, Farfesa Muhammad Bello Kawuwa ne ya mika takardar nadin ga sabon sarkin a madadin gwamnan. Da yake isar da sakon Gwamnan, Farfesa Kawuwa ya bayyana muhimmiyar...
    Gwamnan ya bukaci kamfanin da ke aikin da ya bi ka’idoji da tsarin tsaro, tare da roƙon al’ummomin da abin ya shafa da su ba da haɗin kai ga masu aikin da kuma kare rayuka da kayan aiki.   “Wannan aiki wani ɓangare ne na kudirin Gwamnatin Jihar wajen samar da ci gaban ababen more rayuwa domin bunkasa tattalin arziki da tabbatar da ganin cigaba ya kai kowane yanki,” in ji Gwamna.   Da yake kaddamar da aikin, Gwamna Sule ya sake jaddada kudirin Gwamnatinsa na kada a bar ko wata al’umma a baya wajen kawo ci gaba, domin samar da jihar Nasarawa da tabbatar da lafiya da haɗin kan ‘yan jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
    Akalla mutane 11 ne aka kashe a harin da wasu ‘yan bindiga suka kai a unguwannin Kagara da San-Isa da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara. Majiyoyi daga yankunan biyu sun shaida wa wakilinmu cewa an kai hare-haren ne a unguwannin Kagara da San-Isa tare da wasu kauyukan da ke kewaye. Waɗanne Ƙasashe Ne Suka Amince Da Kafa Ƙasar Falasɗinu? Sanata Shehu Buba Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Da Rigakafin Shanu A Bauchi Wata majiya daga dan garin Kagara wanda ya bayyana sunansa da Abubakar Sani ya shaidawa LEADERSHIP cewa ya rasa ‘yan uwansa guda biyu a harin wanda ya afku a ranar Asabar din da ta gabata. Ya ce, ‘yan fashin da suka yiwa kauyen su kawanya da...
    Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai kai jihar ga tudun mun tsira.   Lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Honorabul Aminu Sani Jaji, ya gode wa al’ummar Zamfara bisa nuna kauna da yarda da suka yi mishi, inda ya sha alwashin yi musu sakayya akan haka.   “Dukkanin abubuwan da muke yi muna yin su ne domin al’umma, kuma jama’ar nan ita taga dacewa...
    Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015. Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.
    Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja ya bayar da umarnin bude jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida Lapai domin fara gudanar da karatu na yau da kullun.   Umurnin sake bude jami’ar ya biyo bayan nazari sosai kan matakan tsaro da inganta ababen more rayuwa a jami’ar.   Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Neja Alhaji Abubakar Usman ya rabawa manema labarai ta hannun jami’in yada labaran sa Lawal Tanko a Minna.   Ya ce Gwamna Bago ya gamsu da ingantaccen gine-ginen tsaro da ci gaban ababen more rayuwa da aka yi don kare dalibai da ma’aikata da kuma al’ummar Jami’ar.   Sakataren Gwamnan Jihar Neja dai ya jaddada jajircewar Gwamnati wajen kare jin dadin...
    Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da kudurinta na yaki da zaizayar ƙasa, ambaliyar ruwa, da sauran matsalolin da suka shafi muhalli. Wannan bayani ya fito ne daga Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin kaddamar da babban shirin dashen itatuwa da za a shuka tsirrai miliyan biyar da rabi a faɗin jihar, wanda aka gudanar a ƙaramar hukumar Makoda. Ya bayyana cewa babban burin wannan shiri shi ne magance dimbin matsalolin muhalli da ke addabar al’ummar Kano. Gwamna Yusuf ya jaddada cewa waɗannan matsaloli sun jawo manyan kalubale ga al’umma. Ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta samar da dukkan kayayyakin da suka wajaba don kula da tsirran da za a dasa, domin su girma yadda ya kamata tare da cika...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq ya bukaci sabbin mambobin hukumar yi wa kasa hidima (NYSC) da aka rantsar da su kasance masu kishin kasa da kuma ci gaba da zama ’yan kasa nagari.   Gwamna AbdulRazaq ya bayyana haka ne a yayin bikin rantsar da rukunin ‘B’, a sansanin NYSC dake Yikpata a karamar hukumar Edu.   Ya kuma shawarce su da su yi taka tsantsan wajen gudanar da ayyuka daban-daban na kwas din.   Gwamna AbdulRazaq ya tabbatar wa ‘yan yiwa kasa hidimar cewa gwamnatin jihar za ta samar da yanayin da zai taimaka musu su ci gaba.   A nasa jawabin, kodinetan NYSC na jihar, Mista Onifade Joshua, ya yabawa gwamna AbdulRazaq bisa goyon bayan da yake baiwa...
    Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati.   Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina dakin kwanan dalibai mai hawa daya a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, da za a kasha naira miliyan dari hudu da tamanin da bakwai.   Alhaji Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta kuma amince da gyaran sashen da aka kona na gidan talabijin ta Najeriya NTA Sokoto wanda kudinsa ya kai naira miliyan dari biyu da casa’in....
    Tawagar Uwargidan Gwamnan Jihar Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ta kai ziyarar ta’aziyya ga sabon Sarkin Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a fadarsa.   Ziyarar ta biyo bayan rasuwar marigayi Sarkin Gusau, Dakta Ibrahim Bello, wanda aka yi ta murna da shi a bisa kyakkyawan jagoranci da kuma gudunmawar ci gaban masarautu da jihar Zamfara.   Hajiya Larai Musa Lawal, ta mika sakon ta’aziyyar uwargidan shugaban kasar ga iyalan gidan sarautar tare da addu’ar Allah ya jikansa da rahama.   Ta kuma mika sakon taya murna ga sabon sarkin, tare da yi masa fatan Allah ya kara masa lafiya mai cike da hikima da zaman lafiya da hadin kai.   A nasa jawabi, sabon Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim...
    Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.   Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.   A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
    Gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana jin dadinsa kan aikin titin Eiyenkorin zuwa Afon Ojoku zuwa Offa zuwa Odo zuwa Otin mai tsawon kilomita 49 da ake ginawa.   Titin siminti na daya daga cikin manyan tituna hudu da ake ba da tallafi a jihar Kwara a karkashin shirin gwamnatin tarayya na karbar haraji a misalin hadakar kamfanin BUA.   Gwamna AbdulRazaq ya godewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da aiwatar da ayyukan karbar haraji da kuma sauran dimbin tallafin da yake baiwa jihar.   “Muna duba ayyukan titunan gwamnatin tarayya da na Jihohi, wannan sabon titin Ilorin/Offa ne, kuma za ku ga yadda yake da inganci, dole ne mu gode wa Shugaba Bola Tinubu kan...
    Gwamnatin jihar Kano ta jaddada kudirinta na yaki da gurbacewar kasa, zaizayar kasa da sauran kalubalen muhalli.     Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin bikin kaddamar da wani katafaren shirin dashen itatuwa, inda za a dasa itatuwa miliyan 5 da rabi a fadin jihar, wanda aka gudanar a karamar hukumar Makoda.       Ya ce babban makasudin wannan shirin shi ne a magance dimbin kalubalen muhalli da ke addabar al’ummar jihar Kano.     Gwamna Yusuf ya jadadda cewa wadannan kalubalen na haifar da babbar matsala ga al’umma.     Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar ta bayar da duk wani tallafin da ya dace don shayar da ‘ya’yan itatuwan, ta yadda za...
    Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi.   An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano.   Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    Sabon ginin na Janguza mai dauke da fursunoni 3,000, gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ce ta gina shi.   An gina gidan yarin na Kurmawa ne a shekarar 1910 a karkashin gwamnatin mulkin mallaka. Daga nan ya zama daya daga cikin fitattun alamomin tarihin mulkin mallaka da ke Kano.   Kano tana da gidan yari guda goma. Biyu a cikin birni—Kurmawa da Goron Dutse, yayin da sauran kuma suke a kananan hukumomin Wudil, Kiru, Rano, Sumaila, Bichi, Tudun-Wada, Gwarzo, da Dawakin-Tofa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe ...
    ADC ta ce, duk da cewa an tsara filin jirgin ne don karbar fasinjoji miliyan 14 a cikin shekara guda, amma rahotannin da ake da su sun nuna cewa, filin jirgin ya karbi fasinjoji miliyan 6.5 ne kawai a shekarar 2024, kasa da rabin karfinsa.   Don haka, ADC ta yi kira ga daukacin ‘yan Nijeriya da su yi watsi da wannan aiki na “rashin hankali”, inda ta bukaci a dakatar da shi nan take, sannan a karkatar da kudaden zuwa ayyukan da al’umma suka fi bukata, wadanda su ya kamata kowacce gwamnati ta fi ba su muhimmanci. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin...
    A ranar Lahadin da ta gabata ne dubban masu zanga-zangar suka yi zanga-zangar nuna goyon baya ga Falasdinawa da kuma yin Allah wadai da kisan kiyashin da “Isra’ila ke yi” a Gaza. Taron wanda masu shirya taron suka yi wa lakabi da “March for Humanity”, ya ga mahalarta taron suna daga tutocin Falasdinawa da harba tukwane da kwanonin tukwane, abin da ke nuni da yanayin yunwa da yunwa da ke yaduwa a Gaza. Daga cikin wadanda suka halarci taron har da wanda ya kafa WikiLeaks Julian Assange da ‘yan majalisar Labour biyar, wadanda bayyanarsu ta ja hankali a cikin yanayi mai cike da rudani. Assange, wanda ya koma Ostiraliya a bara bayan an sake shi daga wani gidan yari na...
    Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wani kakkausar gargadi kan matsalar ruwan sha da ke kara kamari a zirin Gaza, inda ta bayyana cewa yunwa na ci gaba da rataya a kan al’ummar da ke kara hana samun tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli. A cikin wani sabon rahoto, MDD ta ce kashi 96% na iyalai a Gaza na fuskantar matsalar rashin ruwa, yayin da kashi 90% na al’ummar kasar ba su da tsaftataccen ruwan sha. Ya kara da cewa kashi 75 cikin 100 na mazauna garin suna kokawa wajen shiga bandaki, lamarin da ke kara tabarbarewar bala’in jin kai a cikin ci gaba da kawanya da kuma ta’addancin Isra’ila na tsawon watanni Tun da farko, ofishin kare hakkin bil...
    Ma’aikatar tsaron kasar Sin ta sanar a jiya Lahadi cewa, Sin da Rasha sun fara atisayen soja na hadin gwiwa mai taken “Tekun hadin gwiwa na shekarar 2025” a tekun Japan, a wani bangare na kokarin zurfafa hadin gwiwarsu ta fuskar “mutumin Amurka.” Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta bayyana cewa, sojojin biyu za su gudanar da ayyukan ceto a cikin ruwa, da yaki na hadin gwiwa na yaki da jiragen ruwa, da na yaki da jiragen ruwa, da na jiragen ruwa a kusa da tashar jiragen ruwa na Vladivostok na Rasha. Sanarwar ta ce, jiragen ruwa na kasar Sin 4 ne ke halartar atisayen tare da na Rasha, ciki har da makami mai linzami Shaoxing da Urumqi. Rasha da...
    Sojoji sun kama wani gungun dillalan miyagun ƙwayoyi 28 a cikin Babban Barikin Sojoji na Jaji da ke Jihar Kaduna. Dilolin ƙwayar da aka kama sun haɗa da mata 11 da maza 18, lamarin da ya haifar da fargaba gane da yaɗuwar ɗabi’ar ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a tsakanin iyalan sojoji da fararen hula da ke makwabtaka da su. Kakakin Cibiyar Horas da Mayaƙan Ƙasa da aka barikin, Kyaftin Olusegun Abioye, ya bayyana cewa sojoji sun gano cibiyar dilolin ƙwayar ne a unguwanni Railway da Unguwar Lauya da ke cikin harabar barikin na Jaji. Ya ƙara da cewa an kama shugabannin masu fataucin miyagun ƙwayoyi guda aƙalla guda 15 a waɗannan unguwanni biyu, kuma an miƙa duk waɗanda aka kama...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Ga alama kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu a fafutukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono zalla a wata shida na farko. Rahotanni sun ce duk da daɗewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da yara nono uwa zalla ba su haura kashi 29 cikin ɗari ba. NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suke hana mata shayar da ’ya’yansu nono zalla na watanni shida. Domin sauke...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada kudirin ta na kare al’umma daga ambaliyar ruwa kamar yadda hukumar hasashen yanayi ta kasa ta yi hasashen samu a wasu kananan hukumomin jihar a daminar bana. Mataimakin Shugaban kwamitin fasaha kan magance ambaliya, kuma mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara kan ambaliya da kuma sauyin yanayi, Alhaji Hamza Muhammad Hadejia ya bayyana haka yayin da yake duba aikin jingar ruwan kogi da ya ratsa garuruwan Auyo da Tsidir da Agin da Matsa da Sorakin da Jiyan da Tage da Turabu da kuma Tandanu. Alhaji Hamza Hadejia ya ce daga zuwan Gwamna Umar Namadi kan karagar mulkin Jihar, ya dauki kwararan matakai don kaucewa ambaliyar ruwa, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma. Ya...
    Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: Masu shirin halaka Gaza suna neman hadiye duniyar Musulunci  ne Dakarun kare juyin juya halin Musulunci nanIran sun yi gargadin cewa; Bangarorin da ke shirya kisan kiyashi a Gaza ba wai kawai halakar al’ummar Falastinu ba ne kawai, a’a suna neman mamaye yankuna masu arziki da muhimmanci na duniyar Musulunci ne a wani bangare na ci gaba da fadada ayyukan da suka shafi tsaro da albarkatun kasa. Dakarun kare juyin juya halin na Musuluncin sun bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Tsayin daka da gwagwarmayar da al’ummar Falastinu suke yi a yau a zirin Gaza wajen fuskantar kisan kare dangi da laifukan yahudawan sahayoniyya, wata shaida ce da ke...
    Babban kwamandan sojojin Iran ya jaddada cewa; Ƙarfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa ciki suna nan kuma a shirye suke don aiki Babban kwamandan sojojin kasar Iran, Manjo Janar Amir Hatami ya bayyana cewa: Karfin makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki na sojojin gwamnatin Jamhuriyar Musulunci ta Iran na ci gaba da aiki gadan-gadan, kuma a shirye suke su gudanar da ayyuka,  yana mai cewa: A lokacin yaki na baya-bayan nan suna  ci gaba da kai hare-hare har zuwa lokacin da aka gabata da shirin tsagaita bude wuta kan makiya. A wata ganawa da ya yi da kwamandoji da jami’an rundunar sojojin kasa, Manjo Janar Hatami ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya makiya ce...
    Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu sarautar Tafarkin Gombe. Dakta Daudu, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Sakatare na Tarayya da Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe. Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5 Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Daga baya ya zama Shugaban Ma’aikata a Gwamnatin Jihar Gombe, sannan ya riƙe wasu manyan muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa. Yanzu haka, shi ne Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikata na Ƙasa, inda yake wakiltar Jihohin Adamawa, Gombe da Taraba. Dakta Daudu ya fito ne daga gidan sarauta a Gombe, kuma kakansa shi ne Hakimin Gombe na farko bayan masarautar...
    Rahotonni sun bayyana cewa: Har yanzu gwamnatin mamayar Isra’ila ta ki bari an gano kashi 88% na irin laifukan da ta aikata a yakin Gaza ba Jaridar The Guardian ta Birtaniya ta bayyana cewa: Hukumomin mamayar Isra’ila sun boye kusan kashi 88% na binciken laifukan yaki ko cin zarafin da sojojin mamayar Isra’ila suka aikata a kan Falasdinawa a zirin Gaza ba, ba tare da gabatar da tuhumce-tuhumce ko cimma matsaya mai kyau ba tun farkon fara kai hare-haren wuce gona da iri kan Zirin Gaza a watan Oktoban shekara ta 2023. Rahoton ya nakalto Action on Armed Violence yana cewa: gwamnatin mamayar Isra’ila na neman dauke hankalin duniya kan rashin hukunta ta ta hanyar gujewa daukar alhakin manyan laifukan...
    Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dakta Abubakar Shehu Abubakar III, ya naɗa Dakta Ibrahim Jalo Daudu sarautar Tafarkin Gombe. Dakta Daudu, wanda ya taɓa riƙe muƙamin Babban Sakatare na Tarayya da Kwamishinan Lafiya na farko a Jihar Gombe. Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiya miliyan 5 Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Daga baya ya zama Shugaban Ma’aikata a Gwamnatin Jihar Gombe, sannan ya riƙe wasu manyan muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa. Yanzu haka, shi ne Kwamishina a Hukumar Kula da Ayyukan Ma’aikata na Ƙasa, inda yake wakiltar Jihohin Adamawa, Gombe da Taraba. Dakta Daudu ya fito ne daga gidan sarauta a Gombe, kuma kakansa shi ne Hakimin Gombe na farko bayan masarautar...
    A cewar sanarwar, AIHS za ta taimaka wajen haɓaka tambarin dangote da haɓaka dabarun haɗin gwiwa tare da masu ruwa da tsaki. Kodinetan shirin Barista Festus Adebayo ya shaida wa manema labarai cewa, za a iya cike giɓin gidaje a ƙasar ta hanyar haɗin gwiwar Haɗin kan Jama’a masu zaman kansu (PPP). Ya ce: “Kwarewa da haɗin gwiwa su ne manyan abubuwan da muka a gaba, idan aka yi la’akari da saurin ci gaban fasaha a cikin gine-ginen gidaje, samar da kudaɗe da kuma inganta tsarin.” Ya ce taken taron na wannan shekara, Maimaita Gidaje Ta Hanyar Sabuntawa, wanda daidai yake da ainihin darajar kamfanin. Barista Adebayo ya ce yana da ƙwarin gwiwar cewa haɗin gwiwa da kamfanin Simintin dangote...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da babban shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar a shekarar 2025. An fara dashen ne yankin Yanbawa da ke Ƙaramar Hukumar Makoda. Sake zaɓen Tinubu zai lalata makomar Najeriya — El-Rufai  Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Gwamnan ya ce wannan shiri na nufin yaƙi da sauyin yanayi, farfaɗo da ƙasar da ta lalace, da kuma kare muhalli. Ya ce an fara dashen bishiyoyin a wannan fili tun shekarar 1972, amma aka bari ya lalace. Yanzu gwamnatinsa ta gyara shi don ya taimaka wajen shawo kan matsalolin fari da sauyin yanayi. Ya ƙara da cewa wannan shiri yana daga cikin ayyukan muhalli da gwamnatinsa ta aiwatar cikin shekara guda....
    Ma’aikatan agajin gaggawa a lardin Hebei na arewacin kasar Sin da ambaliya ta aukawa, sun karfafa kokarin gyara tituna da gadojin da suka lalace, domin tabbatar da isar da kayayyakin agaji da na aikin ceto ba tare da tangarda ba. Ruwan sama dake ci gaba da sauka a kwanakin baya-bayan nan ya haifar da ambaliya da zaftarewar kasa a fadin lardin, lamarin da ya rutsa da gundumomi da dama. Zuwa safiyar jiya Asabar, an dawo da zirga-zirga a sassan tituna 961 dake fadin lardin Hebei. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Kocin Tottenham Frank, wanda ya koma Spurs daga Brentford a watan Yuni, ya yi godiya ga kyaftin din na Koriya ta Kudu, “shi gwarzo ne na gaskiya ga Spurs a kowane fanni, daya daga cikin manyan yan wasan da suka taba taka leda a gasar Premier inji kocin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ce idan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC suka sake lashe zaɓe a 2027, hakan zai lalata makomar ’yan Najeriya. El-Rufai, ya faɗi haka ne a Jihar Sakkwato yayin wani gangamin wayar da kan jama’a da jam’iyyar adawa ta ADC, ta shirya. Gwamnan Yobe ya naɗa Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ya ce yana goyon bayan wannan haɗaka, kuma zai taimaka wajen ganin ’yan Najeriya sun sauke APC daga kan mulki. “Idan muka bar wannan gwamnati ta ci gaba da mulki zuwa karo na biyu, ragowar abin da ya rage na haɗin kai da amincewa tsakanin ‘yan Najeriya zai lalace. “Ƙasar...
    A kokarin da Gwamnatin Jihar Jigawa ke yi na kara habbaka harkokin noma, shirin ACRESAL yace sami amincewar gwamnatin na siyo injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 3,000 domin tallafawa manoma. Shugaban Shirin na Jihar, Malam Yahaya Kafin Gana ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse. Yana mai cewar, samar da injinan ban ruwa masu amfani da hasken rana ga manoman na da nasaba da bunkasa aikin gona a jihar Jigawa. A cewar sa, shirin ACRESAL na jihar ya sami sahalewar gyaran karin wasu cibiyoyin renon itatuwa guda 3 a sassan jihar. Malam Yahaya Uba Kafin Gana ya kara da cewar, cibiyoyin renon itatuwan da za’a gyara sune na garuruwan Birnin Kudu da Kafin Hausa da...
    A zagayen duba farashin kayayyakin da aka gudanar a kasuwannin ƙasar nan, ya nuna cewa, farashin 50-kilogramme na buhun shinkafa ƴar gida ana sayar da shi ne a kan naira dubu 65,000 zuwa naira 68,000, inda kuma ake sayar da masara kan naira dubu 35,000 zuwa 37,000 a kan kowani buhu, yayin da na ƙasashen waje ke kaiwa naira 83,000 kan buhu guda.  Wannan gagarumin ragin da aka samu ya sanya manoman cikin gida na nuna hakan a matsayin ƙalubale ga ci gaba da noman a Nijeriya. Sai dai kuma babban matsalar da ake fuskanta a harkar noma a Nijeriya shi ne tsadar takin zamani da sauran kayan aikin gona a Nijeriya, lamarin da ke sanya abun da manoman cikin...
    Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe kiyama. Ya nuna gamsuwa da nasarorin da Gundumar ta samu wajen tattara zakka a masarautar sa. Daga bisani ya karrama Hakimin Yayari, Alhaji Garba Muhammad da Dagaci da kuma Mai Unguwar cikin garin Yayari. A jawabin sa, Sa’in Dutse, Mallam Mahmud Yunusa yace gundumar Yayari ce ta zo na 1 a tattara zakkar kudi yayin da Gundumomin Gantsa da Fagam suka zo na...
    Gargaɗin ya yi daidai da irin wannan sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka a Jamaica da Uganda suka fitar kwanan nan, a wani ɓangare na yaƙi da dabi’ar karya ƙa’ida shige da fice.  A cikin watan Janairun 2025, hukumomin Amurka sun sake jaddada aniyarsu na ƙarfafa ikon kula da iyakoki kan yin amfani da damar zama dan ƙasa ta haihuwa. A farkon wannan shekara, shugaban ƙasar ɗonald Trump ya sake nanata matsayinsa na cewa yaran da aka haifa a Amurka ga baƙin haure ba su da takardun zama ƴan ƙasa kai tsaye. A bisa dokar da aka yi wa kwaskwarima na Amurka kan shaidar zama dan ƙasa, ta fayyace cewa duk wani jaririn da aka haifa sai an duba matakin damar...
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya amince da naɗa Hon. Ismaila Ahmed Gadaka a matsayin sabon Sarkin Gudi, bayan rasuwar Alhaji Isa Bunuwa Madugu Ibn Kaji. Sabon Sarkin na Gudi, Ismaila Ahmed Gadaka, ya shahara da ƙwarewa a fannoni da dama. Sojoji sun ceto malamin Jami’a da aka sace a Taraba Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Ya taɓa zama ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Fika/Fune daga 2011 zuwa 2019, kuma kafin nan ya yi aiki a matsayin Kwamishina a Jihar Yobe daga 2007 zuwa 2010. Gadaka, ƙwararren ma’aikacin banki ne, inda ya yi aiki da bankuna irin su UBA da Standard Trust Bank, inda ya kai matsayin Manajan Kasuwanci. Kafin naɗa shi Sarki, ya...
    A cewar shugaban kwamitin, Katsina na kuma goyon bayan batun sauke wasu ikon gwamnati daga matakin tarayya zuwa jihohi, saka sarakunan gargajiya a cikin kundin tsarin mulki da kuma sake fasalin harkokin kuɗi. Sanata Ibrahim ya shaida wa kwamitin cewa an tattara dukkan ra’ayoyi da buƙatun jama’ar Katsina, tare da gabatar da su a cikin takardar matsayar. Tun da farko, yayin da yake ƙaddamar da taron jin ra’ayoyin jama’a, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan gyaran kudin tsarin mulki ya buƙaci a riƙa yin irin wannan taron lokaci zuwa lokaci domin ya dace da halin da ake ciki. Sanata Barau Jibrin, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar dattawa, ya tabbatar da cewa dukkan abubuwan da aka tattara daga gwamnati, ƙungiyoyi da...
    Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji Al’ummomin da aka kudiri niyyar sake tsugunar da su sun hada da Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram da Darajamal. Zulum ya ce ana kafa matsugunan tanti na wucin gadi guda 1,000 a kowace al’umma, inda tuni aka kammala wacce ke Darajamal. “Mun himmatu wajen mayar...
    Auwalu Labarina, wanda ke cikin matasa jarumai da tauraruwarsu ke haskawa a Masana’antar Kannywood, ya fito a manyan fina-finai da dama da suka hada da darasi, Kwana Casa’in, Gidan Sarauta da kuma shirin nan na Labarina, ya kuma samu kyautuka da dama da suka danganci wannan sana’a tasa ta fim a lokuta daban-daban. Kazalika, ya yi nuni da cewa; yanzu mafi akasarin mutane, ba sa son abin da zai taimaka musu; kawai dai sun fi mayar da hankali wajen sharholiya iri-iri. da yake amsa tambaya a kan me yasa ya fi mayar da hankali wajen ɗora bidiyo, musamman na jarumai mata a Masana’antar Kannywood a shafukansa na sada zumunta, musamman kuma ‘Facebook’? Sai Baba Sadiƙ ya ce; ba komai ba...
    Kungiyar Hamas wacce takr iko da Gaza kuma take gwagwarmaya da HKI tun shekara ta 2023 a baya-bayan nan, ta bayyana cewa ba za ta ajiye makamanta ba sai an kafa kasar falasdinu mai zaman kanta, wanda yin watsi ne da bukatar HKI na shafe kungiyar daga doron kasa. Shafin labarai na Internet Arab News na kasar Saudiya ya nakalto kungiyar tana fadar haka bayan da taron tattaunawa ta tsagaita budewa juna wuta na kwanaki 60 ya tashi baram-baram a birnin Doha na kasar Qatar. Labarin ya kara da cewa, a ranar Talatan da ta gabata ce, kasashen Qatar da Masar suka amince da ra’ayin samar da kasashe biyu a kan kasar Falasdinu da aka mamaye, a matsayin hanya Tilo...
    Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa. Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana cewa a jiya Asabar yahudawan sun kashe mutane 38 masu neman abinci. Labarin ya kara da cewa, duk tare da sanarwar da gwamnatin HKI ta bayar na tsagaita wuta a wani bangar na zirin gaza, saboda bawa Falasdinawan dama samun agaji daga wasu wurare amma sojojin HK sun ci gaba da kashe Falasdinawan . Zuwa ranar jumma’an da ta gabata, sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa...
    Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka ta tanada.   Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan lamarin ta ce: “Saboda haka, ministan yana maraba da matakin da Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka na kai koken da ta ke da shi kan zargin rashin ɗabi’a da Badeggi FM ta yi a hukumance zuwa ga NBC domin a warware batun.”   Idris ya roƙi dukkan ɓangarori da su kwantar da hankalin su, yana...
    “daidaita farashin ya kasance hanya daya tilo da za a iya amfani da ita wajen tafiyar da harkokin kasuwa da kuma tabbatar da gaskiya,” in ji shi. Edun ya nuna ƙalubale a tsarin biyan ciniki a Nijeriya, tare da lura da cewa har yanzu ana samun yawan hada-hadar kasuwanci ta hanyoyin da ba kamata ba. Ya bayyana cewa gwamnati na binciken gyare-gyare da nufin ƙara bayyana gaskiya, ciki har da yiwuwar gudanar da cinikin danyen mai daga ƙasashen waje da na naira. “Yawancin mu’amalar kasuwancinmu ana gudanar da su ne a waje da tashoshi na yau da kullun. Muna aiki kan gyare-gyaren da za su inganta tsarin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
    Ya danganta mutuwar ta ƙanana da matsakaitan sana’oi a ƙasar, kan rashin samun rancen kudaɗen da za su ci gaba da ka kasuwancin su da rashin kayan aiki, da rashin kasuwa da ba a samu sosai da kuma rashin gudanar da ingantaccen shiri, kafin su fara gudanar da kasuwancinsu. Ya sanar da cewa, ya zama wajibi, ƴan kasuwa musamman ƙanana da matsakaitan sana’oi a su sani cewa, bab wani batun yin wani holewa, na jin daɗi Ya bayyana cewa, sama da ƙanana da matsakaitan sana’oi 40 a ƙasar nan, burin su ba shi ne, na ƙara yawan adadin alƙaluma ba, anna burin shi ne, na ƙarfafa zurewar kasuwancinsu. “Alƙaluma sun nuna cewa, akwai ƙanana da matsakaitan sana’oi 40 a ƙasar...
    Sai dai tuni masu sanatoci da dama, kamar Sanata Shehu Buba, da Sanata Abdul Ahmad Ningi da ke wakiltar Bauchi ta tsakiya suka ƙaryata labarin da cewa babu gaskiya a cikinsa tare da neman jama’a da su yi watsi da shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’, wato lashe kofin a karo na 10 a tarihi kuma ta ci gaba da jan zarenta na tawagar mata wadda babu kamarta a wannan nahiyar. Nijeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya. A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Nijeriya...
    Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta ce Gwamnatin Tarayya ta yi sakaci game da ɓacewar ɗan gwagwarmaya Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata. A wata sanarwa da ta fitar, Amnesty, ta ce abin takaici ne ganin cewa shekara shida kenan da Dadiyata ya ɓace ba tare da wani sahihin bayani ba. Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a Abuja Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Dadiyata ya ɓace ne a ranar 2 ga watan Agustan 2019, bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun shiga gidansa da ke unguwar Barnawa a Jihar Kaduna, suka tafi da shi. Tun daga wannan lokacin, iyalansa da abokansa ke jiran jin...
    “Kazalika sarkin ya bayyana cewa, mun kuma duba yanayinmu. Me muke da shi? Me za mu iya yi? Me ya kamata mu yi domin inganta rayuwar mutanenmu? Allah ya albarkaci ƙasarmu, ƙasa ce mai faɗi sosai, kuma ta dace da ayyukan noma. Mun kuma yi la’akari da fannin ilimi. Jihar Neja, an san tana gaba a fannin ilimi. To, kwatsam, sai wannan mataki ya samu tasgaro, yara ba su iya cin jarabawar WASC, zuwa makaranta ya yi ƙasa da ƙasa, ba a kula da malamai yadda ya kamata. Wasu makarantun ba su da malamai. Za ka ga makaranta mai yawan dalibai 300 tana da malami daya ko biyu, hakan ba abu ne mai yiwuwa ba,”in ji shi. Ya ci gaba...
    Wani mutum ya rasu, yayin da wasu biyu suka jikkata sakamakon rikici da ya ɓarke tsakanin mazauna ƙauyen Kuchibiyi da jami’an ’yan sanda a Ƙaramar Hukumar Bwari da ke Babban Birnin Tarayya, Abuja. Wani mazaunin ƙauyen, Samuel Dangana, ya shaida wa wakilinmu ta waya cewa rikicin ya samo asali ne yayin da wasu da ake zargin masu ƙwacen fili ne suka zo ƙauyen tare da ‘yan sanda daga ofishin Byazhin, suna ƙoƙarin ƙwace wani fili a ƙauyen. Zulum zai mayar da ’yan gudun hijira 5,000 Bama Yadda binciken zargin tallafa wa Boko Haram ke tafiyar hawainiya a Majalisa Dangana, ya ce lokacin da mazauna ƙauyen suka gan su, sai suka taru suka toshe hanya don hana su zuwa wajen filin....
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce gwamnatinsa na shirin mayar da mutum 5,000 gida daga sansanin ‘yan gudun hijira kafin wucewar damina domin su samu damar yin noma. Mutanen za su fito ne daga garuruwan Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram, da Darajamal. Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Gwamnan, ya bayyana hakan ne lokacin da ya kai wa Mai Martaba Shehun Bama, Dakta Umar ibn Kyari Umar El-Kanemi, ziyara a fadarsa da ke Bama. Ya ce an riga an kammala gina matsuguni 1,000 a Darajamal, sannan kuma aikin gina wasu a sauran garuruwan hudu. “Mun ƙudiri aniyar dawo da ‘yan gudun hijira gida. A Mayanti,...
    A’isha ƴar shekara uku da suke zaune a ƙarƙashin inuwar bishiyar ɗogoyaro a wani ƙauye mai nisa a yankin Arewa maso Gabas (sansanin gudun hijira). Babu takalmi a ƙafarta, ta yi shiru, saboda radaɗi da take ji. ƙafafuwanta sirara sun yi rauni, cikinta ya dan kumbura saboda yunwa, idanunta sun fito tana cikin halin da bai kamata a ce mai shekaru irinta na ciki ba. Aisha Abdullahi ba ta iya yin kuka ba, domin babu ƙarfin halin yin hakan Mahaifiyarta, Maryam Abdullahi, tana girgiza ta a hankali a cinyarta, ta hada man gero mai ruwa da dakakken ganye a cikin wani ƙaramar roba. Abincin da suke ci a cikin kwana biyu. Ta shaida wa LEAɗERSHIP Weekend cewa, “wani lokaci ta...
    Bayan mutane da dama sun nuna ɓacin ransu kan al’amarin, gwamna Abba Yusuf ya kafa kwamiti domin bincikar lamarin, tare da umarnin a miƙa masa rahoton cikin mako guda. Gwamnan, ya taɓa goyon bayan jami’an tsaro wajen kama Danwawu, kuma ya umarci NDLEA ka da su sake shi. Wani jami’i ya ce: “Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ɗauki wannan aiki na Kwamishina a matsayin cin fuska ga gwamnatinsa da kuma yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.” An ruwaito cewar gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani shiri a ɓoye domin kama Danwawu, wanda Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Bakori ya jagoranta. Me Ya Sa Gwamnan Bai Kore Shi Ba? Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya yi niyyar korar Namadi nan take, amma ya dakatar...
    Fiye da shekaru goma da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya dora samun ci gaba marar gurbata muhalli a matsayin wata muhimmiyar manufar raya kasa. Ya taba fitar da manufar raya kasa ta hanyar bayar da muhimmnci ga “Muhalli”, wadda ta yi nuni da cewa ingantaccen yanayin muhalli abu ne mai matukar daraja don samun ci gaba. Tun daga wannan lokacin, kasar Sin ta ci gaba da yin sauye-sauye masu kiyaye muhalli, inda ta zama kasa mafi girma a duniya wajen kera batir na lithium da motocin masu amfani da lantarki. Game da hakan, a yayin da ake tattaunawa da Jorge Moreira da Silvas, babban darektan ofishin kula da ayyuka na MDD, a wani shiri mai suna “Leaders Talk” da...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Suna fatan haɓakar musayar kasuwanci tsakanin Iran da Pakistan ta haura dala biliyan 10 Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bar birnin Tehran a wannan ranar Asabar din zuwa Islamabad na Pakistan a wata ziyarar aiki a kasar bisa gayyatar da fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi masa. Shugaba Pezeshkian a cikin wata sanarwa da ya fitar kafin ya bar Tehran ya ce: “Zasu ziyarci Pakistan ne tare da tawaga bisa gayyatar da dan uwansu fira ministan Pakistan Shehbaz Sharif ya yi musu.” Ya kara da cewa: “Akwai kyakykyawar dangantaka, mai karfi da kuma zurfafa a tsakanin Iran da Pakistan. Wannan alakar ba ta shafi tattalin arziki, kimiyya, al’adu, masana’antu, da kan iyaka...
    Jaridar Ma’arif ta Isra’ila ta bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fuskantar daya daga cikin manyan shan kashi a tarihinta Masanin harkokin soji na jaridar Ma’ariv ta Isra’ila Avi Ashkenazi ya amince da cewa: Isra’ila na fuskantar matsala ta gaske bayan shafe kusan watanni 22 ana yakin Gaza, yana mai cewa gazawar tsarin siyasar Isra’ila na yanke kwakkwarar shawara da kuduri da suka kamata ya sa Isra’ila ta kai ga daya daga cikin manyan shan kaye a tarihinta, na siyasa da kuma dabaru.” Avi Ashkenazi, wani manazarcin harkokin soji na jaridar Ma’ariv, ya amince cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na fuskantar “matsala ta gaske” bayan shafe kusan watanni 22 na yakin Gaza. Ya kara da cewa, “Rashin iyawar tsarin siyasar Isra’ila...
    Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta jaddada kudurin ta na bada managartan shawarwari da za su yi wa kananan hukumomin jihar jagoranci wajen gudanar da ayyukan su kamar yadda yakamata. Shugaban Kwamatin Kananan Hukumomi na Majalisar, Alhaji Aminu Zakari, ya bada wannan tabbacin lokacin rangadin kwamatin majalisar a sakatariyar karamar hukumar Birniwa. Alhaji Aminu Zakari Wanda shi ne wakilin mazabar Gwiwa, yace ziyarar Kwamatin na daga nauyin da aka dorawa bangaren majalisa wajen bibiyar yadda Gwamnati ta ke aiwatar da manufofi da shirye shirye domin tabbatar da shugabanci nagari. Alhaji Aminu Zakari yace haka kuma Kwamatin yana la’akari da batun zamantakewar jama’ar da tattalin arziki a matsayin ma’aunin ci gaban rayuwa da koma bayana domin baiwa bangaren zartaswa shawarwari dan bullo...