Leadership News Hausa:
2025-08-09@01:14:33 GMT

Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe

Published: 9th, August 2025 GMT

Sin Ta Mika Sabon Kason Tallafin Abinci Ga Zimbabwe

Gwamnatin kasar Sin ta mika sabon kason tallafin abinci ga Zimbabwe, a wani mataki na bunkasa ikon kasar na samar da isasshen abinci ga al’ummarta, bayan matsanancin tasirin yanayin El-Nino da ya haifar da fari a shekarar bara.

Yayin bikin mika kayan abincin a jiya Alhamis, wanda aka gudanar a birnin Harare fadar mulkin Zimbabwe, mataimakiyar ministan ma’aikatar kyautata rayuwa, kwadago da walwalar al’umma a kasar Mercy Dinha, ta jinjinawa tallafin na Sin, wanda ya kunshi kimanin tan 3,000 na shinkafa da alkama, kayan da ta ce za su taimakawa ‘yan kasar mafiya fama da kunci.

A nasa bangare kuwa, jakadan Sin a Zimbabwe Zhou Ding, ya jaddada aniyar kasar Sin ta taimakawa Zimbabwe, wajen cimma nasarar wadatar da al’umma da abinci da rage talauci, yana mai cewa, tallafin bangare ne na amsa kiran Zimbabwe ga kasashen duniya, na samar mata da tallafin abinci, biyowa bayan fari da ya daidaita wasu sassan kasar.

Jakada Zhou Ding, ya ce har kullum Sin na dora muhimmancin gaske ga ayyukan samar da abinci da rage fatara. Ya kuma yi fatan kasashen biyu za su ci gaba da karfafa kawance don bunkasa samar da isasshen abinci ga al’umma. (Saminu Alhassan)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi

Majalisar Dokokin Bauchi ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a fadin jihar domin haɓaka ci gaba, inganta shugabanci, da kawo sauƙin gudanar da mulki.

Wannan na ƙunshe ne a wani ƙudiri da dan majalisar mai wakiltar mazabar Disina, Sale Hodi Jibir, ya gabatar a yayin zaman da Kakakin Majalisar, Abubakar Y. Sulaiman, ya jagoranta.

Gwamna ya yi wa iyalan ’yan wasan Kano da suka rasu a hatsari goma ta arziki Ministocin Ghana biyu sun rasu a hatsarin jirgin sama

A cewar Jibir, ƙudurin yana dogaro ne da tanadin kundin tsarin mulki na 1999 wanda ya bai wa majalisun dokokin jihohi damar fara shirin ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi, matuƙar an cika wasu sharuɗa da suka haɗa da goyon bayan kashi biyu bisa uku na mambobin majalisa, da mincewar ƙananan hukumomin da abin ya shafa da kuma gudanar da zaɓen raba gardama.

Jibir ya bayyana cewa ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi zai sauƙaƙa rarraba albarkatu cikin adalci da inganta shugabanci da gudanarwa a matakin ƙasa da ƙarfafa haɗin kan al’umma da ci gaban tattalin arziki.

Ya kuma ce yankuna da dama a Jihar Bauchi sun gabatar da buƙatar a ware musu ƙaramar hukuma, musamman duba da girman yankunansu, yawan al’umma, bambancin al’adu da kuma ƙalubalen gudanar da mulki.

Jibir ya buƙaci a kafa kwamitin wucin gadi na musamman domin tattarawa da tantance buƙatun al’umma, da tuntuɓar sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma da nazarce-nazarce kan fadin ƙasa, da yawan jama’a da yanayin tattalin arziki na yankunan da ake neman a samar musu da ƙananan hukumomi.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, ƙudirin wanda ya samu goyon bayan wasu mambobin majalisar da suka buƙaci a gaggauta aiwatar da shi domin amfanin jama’a sun haɗa da Jamilu Umaru Dahiru da Musa Wakili Nakwada da Ibrahim Tanko Burra da Sa’idu Sulaiman Darazo da Dokta Nasiru Ahmed Ala.

A wani ɓangare na zaman, majalisar ta amince da rahoton kwamitinta na ma’aikata, dangane da ƙorafe-ƙorafen rashin biyan ’yan fansho da albashin ma’aikatan ƙananan hukumomi a faɗin jihar.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Hallaka Manomi, An Kashe Shanu Da Tumakai A Wani Sabon Rikici A Bogoro
  • Obi ya ziyarci Bauchi, ya ba da tallafin N15m don inganta ilimi
  • UNICEF Ya Samar Da Abinci Mai Gina Jiki Ga Yara Sama Da 17,000 A Kano
  • Tallafin Kammala Makarantun Share Fagen Shiga Firamare Na Gwamnatin Kasar Sin Zai Amfani Mutane Kimanin Miliyan 12
  • An Bude Bikin Fina-Finan Kasar Sin A Zimbabwe
  • Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan
  • Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi
  • Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan Daya Domin Ayyukan Jin Kai Sakamakon Ibtila’in Ambaliyar Ruwa
  • Remi Tinubu Ta Bai Wa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa A Neja Tallafin N1bn