An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a
Published: 9th, August 2025 GMT
Sin ta ci gaba da tabbatar da matsayinta na babbar kasuwar mutum-mutumin inji masu ayyukan masana’antu a duniya, wanda ta rike tsawon shekaru 12, kuma ita ce babbar kasa mai kera mutum-mutumin inji a duniya. Sin daya ce daga cikin kasashe masu samar da mutum-mutumin inji dake sahun gaba a duniya, kuma ana sa ran za su taka muhimmiyar rawa a fannonin hidimar gida da masana’antu da kayan ajiya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwalara ta kashe mutum 10 a Ƙaramar Hukumar Adamawa
Kwamishinan lafiya na Jihar Adamawa, Dokta Felix Tangwami ya bayyana cewa, cutar kwalara a Ƙaramar hukumar Mubi ta yi sanadin mutuwar mutane 10, inda ya buƙaci mazauna yankin da su kula da tsaftar jikinsu.
Da yake yi wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya (NAN) bayani a Yola ranar Laraba, Tangwami ya ce marasa lafiyan sun mutu ne a gida maimakon a cibiyoyin lafiya.
Majalisar Dokokin Amurka na neman a hukunta ’yan kungiyar Miyetti-Allah An kashe babban limami a Kwara saboda zargin maitaYa ƙara da cewa, gwamnatin jihar tare da haɗin gwiwar hukumar lafiya ta duniya (WHO) sun ɗauki matakin gaggawa don daƙile ɓarkewar cutar.
“Tun daga farko, mun ɗauki matakin gaggawa a kan lamarin, kasancewar mu a can, kuma ba za a iya musanta hakan ba,” in ji shi.
Kwamishinan ya ƙara da cewa, waɗanda suka ziyarci cibiyoyin kiwon lafiya sun samu kulawa, inda aka kwantar da majinyata 25 a ranar Talata 4 ga watan Nuwamba, yayin da wasu da dama kuma an sallame su tare da wayar da su kan harkokin tsafta.
Ya bayyana cewa, an tura jami’an kula da cututtuka na jihar, da Daraktan kula da cututtuka a Hukumar kula da kiwon lafiya a matakin farko, da masu aikin sa-kai zuwa Mubi domin gudanar da ayyuka da kuma wayar da kan jama’a.
Sun kuma gano waɗanda abin ya shafa a cikin unguwanni don tabbatar da sun samu kulawar lafiya.
Tangwami ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya da su goyi bayan ƙoƙarin gwamnati ta hanyar ƙarfafa gwiwar mazauna yankin da su gaggauta neman magani a cibiyoyin lafiya.