Majalisar Kaduna Ta Amince da Dokokin Yawon Buɗe Ido da Zartar da Shari’a
Published: 8th, August 2025 GMT
Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta amince da dokoki guda biyu masu muhimmanci da nufin ƙarfafa harkar yawon buɗe ido da hanzarta gudanar da shari’a a faɗin jihar.
Shugaban majalisar, Yusuf Dahiru Liman, ne ya sanar da amincewar majalisar yayin zaman, ta wanda aka gudanar a harabar majalisar da ke Kaduna.
Dokar farko mai taken “Dokar Kafa Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido, Gidajen Tarihi, Shata Wurare, Lambuna da Wuraren Hutu na Jihar Kaduna, 2024”, na da nufin bunƙasa harkar yawon buɗe ido da raya al’adu a jihar.
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Yusuf Dahiru Liman
Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Shugaban Kwamitin Haɗin Gwiwa na Harkokin Fasaha, Shari’a da Ilimi, Magaji Suleiman, ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da cikakken bincike kan kudirin kuma ya fahimci cewa yana da amfani wajen haɓaka yawon buɗe ido da al’adu.
Magaji Suleiman ya ce idan aka fara aiki da hukumar, za ta inganta shata wurare, lambuna da wuraren shakatawa a jihar, wanda hakan zai ja hankalin masu zuba jari daga cikin gida da waje.
A nasa jawabin, wanda ya dauki nauyin gabatar da kudirin, Mr. Henry Marah, ya bayyana cewa hukumar za ta taka rawa wajen farfaɗo da al’adun gargajiya na jihar Kaduna wacce ke da yawan kabilu daban daban.
Ya ƙara da cewa dokar za ta taimaka wajen samar da kuɗaɗen shiga ga jihar, ƙirƙiro guraben ayyukan yi ga matasa da kuma cusa tarbiyar al’adu ga matasa masu tasowa.
Barista Emmanuel Kantiyok
Har ila yau, Majalisar ta kuma amince da gyara dokar gudanar da shari’ar laifuka ta Jihar Kaduna ta shekarar 2017.
Da yake gabatar da rahoton, Shugaban Kwamitin Shari’a na Majalisar, Barista Emmanuel Kantiyok, ya bayyana cewa gyaran dokar zai taimaka wajen gudanar da shari’a a kan lokaci da kuma tabbatar da adalci ba tare da la’akari da matsayin mutum ba.
Barista Kantiyok ya ce gyaran dokar zai taimaka wajen rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma ƙara wa talakawa kwarin gwiwa ga tsarin shari’a.
Majalisar ta amince da dokokin ne ta hanyar ƙuri’ar murya da ‘yan majalisar suka kada, karkashin jagorancin Shugaban Majalisar, Yusuf Dahiru Liman.
Daga ƙarshe, majalisar ta tafi hutu kuma za ta dawo zaman ta a ranar 9 ga Satumba, 2025.
Shamsuddeen Mannir Atiku
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: jihar Kaduna Jihar Kaduna
এছাড়াও পড়ুন:
Kotun Ta Umurci Gwamnatin Neja Ta Janye Hukuncin Da Ta Dauka Akan Gidan Rediyon Badeggi
Babbar Kotun Shari’a ta Minna a Jihar Neja ta bayar da wani umarnin na wucin gadi game da gidan rediyon Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd, inda ta hana Gwamnatin Jihar ɗaukar duk wata matsaya da za ta dakatar da ayyukan gidan rediyon.
Mai Shari’a Mohammed Mohammed ne ya yanke hukuncin bisa ƙorafin gaggawa (motion ex-parte) da Badeggi Radio Broadcasting Services Ltd da Daraktan gudanarwarta, Mohammed Shuaibu Badeggi, suka gabatar a kotun da ke Minna.
A cikin ƙorafin, lauyoyin masu ƙara sun jingina hujjoji da sassa daban-daban na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara), da kuma Dokar Hukumar Kula da Watsa Labarai ta Ƙasa (NBC Act).
Hukuncin kotun ya hana wadanda ake ƙara, ciki har da Gwamnan Jihar Neja, Antoni Janar da Kwamishinan Shari’a, da Hukumar Raya Birane ta Jihar Neja, daukar duk wani mataki da zai kawo cikas ga lasisin watsa shirye-shirye ko ayyukan kasuwancin kamfanin dake cikin harabar gidan talabijin na N.T.A a Uphill, Minna.
A yayin yanke hukuncin, Mai Shari’a Mohammed Mohammed ya ce yana da matuƙar muhimmanci a bar komai yadda yake (status quo) har sai an kammala sauraron babbar ƙarar gaba ɗaya.
Umarnin na wucin gadi ya haramta ayyuka kamar soke lasisi, janye lasisi, kwacewa, ko kai farmaki da rushe wurin da kamfanin ke gudanar da ayyukansa.
Lauyan masu ƙara, Barista Philip Emmanuel, ya bayyana jin daɗinsa da hukuncin kotun, yana mai cewa hakan babbar nasara ce wajen kare haƙƙin abokan aikinsa.
An shirya cigaba da sauraron ƙarar a wani lokaci domin zurfafa bincike kan batutuwan da ke gaban kotu.
Daga Aliyu Lawal