Aminiya:
2025-08-10@07:45:36 GMT

Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Published: 9th, August 2025 GMT

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno.

A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann.

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi

Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi.

Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196.

Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa Rann daga Kamaru, ya mutu tare da wasu ’yan ta’addan.

An kuma samu nasarar ƙwato bindigogi, harsasai, bama-baman roka da sauran abubuwan fashewa.

Harin ya faru daga ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, zuwa safiyar Juma’a, 8 ga watan Agusta, 2025, tare da taimakon bayan jiragen sojojin sama.

A cewar jami’an tsaro, an gano gawarwakin ’yan ta’adda bakwai a wajen, kuma akwai yiwuwar sama da hakan sun rasu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Boko Haram hari kwamanda Rann

এছাড়াও পড়ুন:

Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno 

Fashewar gurneti ya salwantar da rayukan yara mata uku a garin Pulka da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno.

A wani rahoto da ma’aikacin Sibiliyan JTF Buba Yaga ya fitar, ya ce ɗaya daga cikin ƙananna yaran suna wasa da gurnetin da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne, suka yi watsi da su a lokacin da gurnetin ya tashi da misalin ƙarfe 2:20 na ranar Alhamis.

An garzaya da yaran zuwa Babban Asibitin Gwoza, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.

Daga nan ne aka miqa gawarsu ga iyalansu domin yi musu jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja Yadda ma’aikatan gwamnati ke gina gidaje da kuɗin sata a Abuja

Haɗaɗɗiyar tawagar ’yan sandan da suke tantance bama-bamai (EOD-CBRN), da dakarun Operation Hadin Kai, CJTF, da mafarautan yankin sun ziyarci wurin, inda suka gudanar da aikin share wasu na’urori.

Ba a samu ƙarin ko ɗaya ba, kuma an ayyana yankin a matsayin keɓantaccen wurin da za a kauce wa bi zuwa wani lokaci.

Hukumomin tsaron sun bukaci mazauna yankin da su gaggauta kai rahoton abubuwan da suke zargi ga jami’an tsaro domin hana afkuwar irin wannan bala’i.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno 
  • Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Kashe Ƴan Ta’adda A Borno
  • Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno
  • Jirgin Shugaban Ƙasa Ya Laƙume Naira Biliyan 26.38 Cikin Wata 18 Ƙarƙashin Tinubu
  • An Kashe ‘Yan Ta’adda Fiye Da 30 A Wani Harin Jirgin Sama A Wurin Daurin Aure A Zamfara
  • Gwamnatin Kwara Ta Horar Da Manoma Sama Da 500 Tare Da Basu Tallafi
  • ‘Hayakin janareta’ ya kashe mutum 4 ’yan gida daya a Borno
  • Masu Ƙwacen Waya Sun Kashe Ɗalibin BUK A Kano
  • Jami’an Tsaro Sun Daƙile Harin ‘Yan Bindiga A Zamfara, Sun Ƙwato Bindigogi