Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon
Published: 9th, August 2025 GMT
Kungiyar Hizbullah ta yi gargadin cewa Lebanon da yankin gabas ta tsakiya na fuskantar daya daga cikin yanayi mafi hadari a tarihin baya-bayan nan, inda al’ummar yankin ke fuskantar barazanar wanzuwa da kuma ‘yancinsu.
A cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taronta na yau da kullun, kungiyar ta yi Allah wadai da yadda Isra’ila ke ci gaba da ruruta wutar rikici a yankin gabas ta tsakiya tare da goyon bayan Amurka da wasu kasashen yammacin duniya da na larabawa, a wani bangare na yunkurin sake fasalin yankin da kasar Lebanon.
Babban abin da kungiyar tafi nuna takaicinta akansa shi ne amincewar da gwamnatin Lebanon ta yi a baya-bayan nan da shawarar da manzon Amurka Tom Barrack ya gabatar.
Kungiyar ta bayyana matakin a matsayin wani sabon salo na saba alkawuran ministocin gwamnati da kuma karya rantsuwar da shugaban kasa ya yi. Ta nanata cewa takardar ta sabawa ka’idojin yarjejeniyar Taif, wadda ta tabbatar da ‘yancin kare kai da kuma kiyaye ‘yancin kasar Lebanon.
Kungiyar ta bayyana amincewar da gwamnatin kasar ta yi wa takardar Amurka a matsayin rashin gaskiya,” tana mai gargadin cewa irin wannan matsayi a file yake kan cewa ya keta yarjejeniyar kasa” tare da yin barazanar kwace wa kasar Lebanon daya daga cikin manyan hanyoyin karfinta, wato gwagwarmayar sa kai domin kare kasa.
Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa, karfinta na soji wani babban jigo ne kuma ginshiki a fagen tsaron kasar Lbanon, musamman ma ganin yadda ake samun karuwar barazana da kuma rashin wani tabbataccen lamuni na kasa da kasa.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6 August 8, 2025 Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Nukiliyar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba August 7, 2025 Manjo Janar Mousawi: Martanin Iran Nan Gaba Zai Kasance Mafi Muni Kan Makiya August 7, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Kungiyar ta
এছাড়াও পড়ুন:
Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025
Hukumar Ƙididdiga a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da kasar ke samu ya karu da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.
Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu karin kashi 3.48 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantar tattalin arzikin kasar.
Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da karuwar arzikin kasar, wannan ya karu zuwa kashi 2.82 sabanin kashi 2.60 a 2024.
Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da fan fetur da kuma fannin ma’adinai.
NBS ta ce a rubu’i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna karin kashi 19.23 cikin 100.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci