Araghchi: Mataimakin Shugaban IAEA Zai Ziyarci Tehan َA Gobe Talata
Published: 11th, August 2025 GMT
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa a gobe talata mataimakin shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya zai ziyarci kasar, amma ba tare da zuwa cibiyoyin nukliya na kasar ba.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa wannan shi ne ziyarar aiki na farko wanda wani jami’in hukumar ya kawo ziyara Tehran bayan yakin kwanaki 12 wanda HKI ta dorawa JMI.
Gwamnatin JMI dai tana shakkan ma’amatar da hukumar, inda take ganin babu gaskiya a cikin mu’amalarta da ita, da farko saboda tabbacin cewa hukumar tana bawa makiyanta, musamman HKI wasu bayanai wadanda ta karba a wajenta dangane da shirinta na makamashin nukliya, inda HKI ta sami damar kashe masana fasahar nukliyar kasar da dama a cikin shekarun da suka gabata.
Banda haka hukumar ta IAEA ta tara gwamnoninta suka kada kuri’ar rashin amincewa da shirin makamashin nukliya da rana guda sai HKI ta kawowa Iran hari. Wannan ya nuna kamar akwai aiki tare tsakanin hukumar da HKI.
Wannan matsalolin da kuma debe kauna kan cewa hukumar zata yiwa Iran adalaci majalisar dokokin kasar Iran ta fidda doka wacce ta jingine mu’amala da hukumar.
A wannan ziyarar dai bangarorin biyu zasu fidda sabbin hanyoyin mu’amala da hukumar tare da lura da korafe-korafen JMI a ayyukan hukumar a yanzu.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Tehran: Kasar Lebanon Tana Da yencin Kare Kanta Da Makamanta August 11, 2025 A Mali An Kama Sojoji Fiye da 40 Saboda Zargi da Kokarin Juyin Mulki August 11, 2025 Larijani Ya Gana Da Firai ministan Kasar Iraki A Bagdaza August 11, 2025 Mafi yawan Kasashen Duniya Sun Amince Da Samarda Kasar Falasdinu August 11, 2025 Mahukuntan Iraki Sun Bayyana Cewa: Akwai Yiwuwar Masu Ziyarar Arba’een Na Imam Husaini {a.s} Zasu Zarce Miliyan 4 August 11, 2025 Sojojin Mamayar Isra’ila Sun kai Wasu Munanan Hare-Hare Kan Yankunan Zirin Gaza August 11, 2025 Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Ya Gudanar Da Zaman Taro Kan Aniyar ‘Yan Sahayoniyya Kan Gaza August 11, 2025 Shugaban Iran: Dole ne duniya ta kawo karshen laifukan yakin Isra’ila a Gaza August 11, 2025 Israila Ta Kashe ‘Yan Jarida 4 A Harin Da Ta Kai Kan Tantinsu A Gaza August 11, 2025 Iran: Ba a yanke wani abu game da tattaunawa da Washington ba August 11, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa Da Jamus Da Kuma Birtaniya Sun Bayyana Aniyarsu Ta Ganin An Farfado Da Tattauna Da Iran
Shugabannin Faransa, Jamus, da Biritaniya: Sun kuduri aniyar farfado da tattaunawa da Iran
Kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya sun bayyana aniyarsu ta farfado da shawarwari da Iran da Amurka dangane da shirin makamashin nukiliyar Iran da nufin cimma cikakkiyar yarjejeniya mai dorewa.
A cikin wata sanarwa ta hadin gwiwa, kasashen uku sun yi la’akari da Shirin kunna yarjejeniyar fahimtar juna. A baya dai Faransa da Birtaniya da Jamus sun sanar da cewa za su ci gaba da neman hanyar diflomasiyya don warware rikicin, amma Iran ta tabbatar da cewa ba ta son ci gaba da tattaunawa a halin yanzu idan dai har za a kakaba mata takunkumi.
A gefe guda kuma shugabannin kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus sun yi maraba da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a zirin Gaza tare da yin alkawarin dawo da taimakon jin kai da zarar an amince da yarjejeniyar.
A cikin sanarwar da suka fitar, shugabannin sun jaddada cewa, sun amince da cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya ba da cikakken goyon baya ga shirin na Gaza, da saukaka aiwatar da shi, tare da sa ido kan matakai na gaba.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kungiyoyin Falasdinawa Sun Fitar Da Sanarwar Hadin Gwiwa Kan Tsagaita Bude Wuta A Gaza October 11, 2025 Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya October 11, 2025 Pakistan Ta Kai Hari Kan Kasar Afganistan, Inda Ake Rade-Radin Kashe Shugaban Taliban Na Kasarta October 11, 2025 Putin: Natanyahu Yana Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba October 10, 2025 Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha October 10, 2025 Sa’o’ii Da Fara Janyewar Sojojin HKI A Gaza An Fara Gano Gawakin Falasdinwa October 10, 2025 Falasdinawa Daga Kudancin Gaza Sun Fara Komawa Gidajensu Da Aka Rusa A Arewacin Yankin October 10, 2025 Rahotanni : Isra’ila ta fara janye dawa wasu yankuna na Gaza October 10, 2025 Amurka ta kakaba wa wasu kamfanoni 50 takunkumi saboda sayen man Iran October 10, 2025 Isra’ila ta ce yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza ta fara aiki October 10, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci