Jakadan Kasar Sin A Najeriya Ya Gana Da Ministar Kula Da Masana’antu Da Cinikayya Da Zuba Jari Ta Kasar
Published: 10th, August 2025 GMT
Jakadan kasar Sin da ke Najeriya, Yu Dunhai, ya gana a kwanan nan da ministar kula da harkokin masana’antu, da cinikayya, da zuba jari ta tarayyar Najeriya, madam Jumoke Oduwole.
Jakada Yu ya bayyana cewa, tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci kasar Sin tare da halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC a watan Satumban bara, zuwa yanzu, Sin da Najeriya na kara samun fahimtar juna ta fuskar siyasa, tare da fadada hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi masana’antu, cinikayya da zuba jari, har ma kwalliya ta biya kudin sabulu.
A nata bangaren, madam Jumoke Oduwole ta ce, matakin kasar Sin na soke buga haraji da kashi 100 bisa 100 a kan kayayyakin kasashen Afirka da suka kulla dangantakar jakadanci da ita, ya samu karbuwa sosai daga sassan kasa da kasa, inda Najeriya take matukar yabawa da cikakken goyon-bayan kasar Sin gare ta a fannin raya zaman rayuwar al’umma da tattalin arziki. Haka kuma, Najeriya tana fatan kara tuntubar kasar Sin, da aiwatar da manufofi a zahiri, ta yadda matakin na soke haraji zai amfani al’ummar Najeriya. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cewar masana harkar kiwon lafiya, rashin tantancewa balle a bayar da kulawar da ta dace a kan lokaci na cikin dalilan ta’azzarar barazanar da Zazzabin Lassa ke yi ga bangarori da dama na rayuwar al’ummar Najeriya, musamman a yankunan karkara.
Wani bincike a kan tasirin Zazzabin Lassa a kan rayuwar ‘’yan Najeriya wanda aka wallafa bara a mujallar Springer ya nuna gudunmawar da jahilci yake taimakawa wajen yaduwar cutar a kasar.
A sassan Najeriya da dama dai, ba kasafai mutane ke iya bambance Zazzabin Lassa da sauran nau’ukan zazzabi ba.
Shin yaya za a iya gane Zazzabin Lassa a kuma bambance da sauran nau’ukan zazzabi?
Wannan shi ne batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan