An Naɗa Farfesa Adamu Muƙamin Mataimakin Shugaban Jami’ar Yakubu Gowon, Abuja
Published: 9th, August 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta naɗa Farfesa Mathew Adamu a matsayin sabon mukaddashin Mataimakin Shugaban Jami’ar Abuja, wadda aka sake wa suna zuwa Jami’ar Yakubu Gowon. Farfesa Adamu zai maye gurbin Farfesa Patricia Manko Lar, wadda ta riƙe wannan muƙamin na tsawon watanni shida tun daga Fabrairu 2025. Farfesa Adamu zai fara aiki daga ranar Litinin, 11 ga Agusta, 2025, inda zai riƙe wannan muƙami na tsawon watanni uku.
Farfesa Adamu ƙwararren masani ne a fannin likitancin dabbobi wanda ya fara karatunsa da digiri daga Jami’ar Maiduguri a 1998, sannan ya samu digirin digirgir a Jami’ar Pretoria, Afrika ta Kudu a 2012, an ɗaga darajar shi zuwa cikakken Farfesa a 2019.
Farfesa Yilwatda Ya Zama Sabon Shugaban Jam’iyyar APC Na Ƙasa Gwamnatin Tarayya Za Ta Farfaɗo Da Noman Dabino – ShettimaA cikin shekaru 27 na aikinsa, Farfesa Adamu ya yi fice a koyarwa, da bincike, da gudanarwa a fannin ilimi. Ya taɓa aiki a matsayin likitan dabbobi na hukumar Youth Corps, sannan ya samu damar koyarwa a Jami’ar Noma ta Makurdi inda ya kai matsayi na Farfesa. Haka kuma ya rike muƙamai da dama ciki har da Mataimakin Tsangaya na Kwalejin Likitocin Dabbobi.
Sanarwar ta bayyana cewa sabon VC zai tallafa wa Kwamitin Gudanarwa don kammala zaɓin cikakken Mataimakin Shugaban Jami’a bisa ga ƙa’idojin doka, kuma an gode wa Farfesa Lar kan jajircewarta a lokacin da ta riƙe mukamin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Farfesa Farfesa Adamu
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisa Ta Amince Da Ɗaurin Shekaru 14 A Gidan Yari Ga Malamai Masu Cin Zarafin Mata A Jami’o’i
Majalisar Dattawa a ranar Laraba ta amince da kudirin da ke kayyade hukuncin daurin shekaru 14 ga malamai da aka samu da laifin cin zarafin dalibai mata a manyan makarantu. Wannan matakin ya zo ne a daidai lokacin da rahotanni ke ci gaba da cewa, malamai suna amfani da damar dalibai masu neman maki ko wata alfarma sai su yi lalata da su – wannan matsalar ta tabbata a wani bincike da aka yi a jami’o’in Nijeriya tsawon shekaru, ciki har da binciken sirri na 2019 mai taken “Lalata don samun maki”, wanda ya fallasa cin zarafin da ake yi a wasu jami’o’i. Dokar mai taken ‘Dokar Cin Zarafin Dalibai ta 2025’ (HB.1597), Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta tsakiya) ne ya gabatar da ita domin amincewa. Bamidele ya bayyana cewa, an gabatar da kudirin ne don kare dalibai daga duk wani nau’in cin zarafin jima’i da cin zarafi a rayuwar makaranta, wadda ta tanadi dokokin shari’a don aiwatar da hukunci da hukunta masu laifi. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa November 5, 2025
Labarai Malam Triump: Ƙungiyoyin Ɗariƙun Sufaye Sun Maka Gwamnan Kano A Kotu November 5, 2025
Labarai Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai November 5, 2025