Iran Ta Yi Maraba Da Sulhuntawa Tsakanin Armenia Da Azerbaijan
Published: 9th, August 2025 GMT
Gwamnatin kasar Iran ta yi maraba da sulhuntawa da kasashen Armedia da Azarbaijan a fadar white House, amma ta yi gargadin shishigin kasashen waje a yankin Caucasus, da ke makobtaka da Iran.
Tashar talabijinn ta Presstv a nan Tehran ta ta nakalto wani bayani wanda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a yau Asabar na cewa, sasantawa tasakanin kasashen biyu wani ci gaba wanda zai iya kaiwa ga tabbataccen zaman lafiya a yankin da kuma ci gaba ga dukkan kasashen yankin.
Amma a wani bangare kuma bayanin ya bayyana cewa akwai tsoron kasashen waje musamman Amurka tana iya amfani da wadannan kasashen don cutar da yankin ko wasu kasashe. Don haka ta yi kira ga wadannan kasashe biyu su yi hattara.
Kafin haka dai kasashen Azarbaija da Armenia sun shiga yake-yake sau da dama dangane da yankin n Karabakh wanda a yakinsu na karshe-karshen nan jumhuriyar Azarbaijan ta kwace shi daga hannun Armenia.
Sai dai gwamnatin kasar Iran ta bayyana cewa shirin samar da wani babban titi a yankin zangon kasa ne da tsaron kasar Iran. Ba don kom,e ba sai don Amurka ce take son samar da wannan titin.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Falasdinawa 11 Ne Suka Rasa Rayukansu Saboda Yunwa A Gaza August 9, 2025 Shugaban Kwango, Tshisekedi Ya Shigar Yan Tawaye A Gwamnatinsa August 9, 2025 Iran: ‘Yan Sahayoniyya Na Shirin Share Falasdinawa Daga Kan Doron Kasa August 9, 2025 Iran: Amurka Ta Sha Kaye Daga ‘Yan Gwagwarmayar Kasar Yemen August 9, 2025 Guterres: Dole Ne Gwamnatin ‘Yan Sahayoniyya Ta Gaggauta Janye Shirinta Kan Gaza August 9, 2025 Kasashen Larabawa Da Kungiyoyinsu Sun Yiu Allah Wadai Da Shirin ‘Yan Shayoniyya Kan Gaza August 9, 2025 Iran Da Iraki Sun Jaddada Goyon Bayan Kungiyoyin ‘Yan Gwagwarmaya August 9, 2025 Kwamitin Sulhu na MDD na Shirin gudanar da zaman gaggawa kan batun Gaza August 9, 2025 Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza August 9, 2025 Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza August 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD”
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, ta bayyana cewa “Kisan kare dangi da ake ci gaba da yi a zirin Gaza ya zama babban gwaji ga Majalisar Dinkin Duniya.
Idan muna son kungiya mai inganci kuma mai amfani, dole ne mambobinta su dauki matakin gaggawa tare da tsayin daka wajen dakatar da wannan zalunci da hukunta masu laifi.”
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmail Baghai ya ce zasu hadu a birnin New York domin halartar taron shekara-shekara na Majalisar Dinkin Duniya.
Wannan zaman dai na gudana ne a daidai lokacin da MDD ke bikin cika shekaru 80 da kafuwa, a daidai lokacin da muhimman ka’idojinta da manufofinta ke fuskantar barazanar da ba a taba ganin irinta ba da suka hada amfani da karfi, da rashin mutunta dokokin kasa da kasa, da rashin hukunta manyan laifuka na take hakkin bil’adama.
Kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza yana wakiltar mafi munin gwajin ingancin Majalisar Dinkin Duniya, inji kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Kwamandan Sojan Iran: Ba Za Mu Taba Wasa Da Manufofinmu Na Kasa Ba September 22, 2025 Korea Ta Arewa Ta Sanar Da Kera Wani Sabon Makami Na Sirri September 22, 2025 Jirgin Ruwan “Umar Mukhtar” Na Agaji Ya Kama Hanyar Zuwa Gaza Daga Kasar Libya September 22, 2025 Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci Ya Jinjinawa Tawagar Kokawar Greco-Roma Ta Iran Murnar Lashe Gasar Cin Kofin Duniya September 22, 2025 Pezeshkian: Kasashen Da Ba Su Cika Alkawura Da Suka Dauka Ba Suke Zargin Iran Kan Rashin Mutanta Yarjejeniyar Nukiliya September 22, 2025 Dakarun IRGC: Iran Za Ta Tarwatsa Makiya Tare Da Mayar Da Martani Kan Duk Wani Zalunci September 22, 2025 Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen: ‘Yan Koren Amurka Da Isra’ila Suke Neman Wargaza Hadin Kan Larabawa Da Na Musulmi September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci