Madugun adawa a Nijeriya, Atiku Abubakar ya bukaci a gaggauta sakin fitaccen ɗan gwagwarmayar, Omoyele Sowore da ke tsare a hannun ’yan sandan kasar.
Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriyar wanda ya yi Allah-wadai da lamarin ya ce abin kunya ne cin zarafi da tawagar sa ido ta sufeto janar na ’yan sandan ƙasar suka yi wa Sowore.
“Bai dace a tsare Sowore ba, kuma hakan ya saba wa ka’ida. Dole ne a yi tur da lamarin,” in ji Atiku.
Ya ce laifin ɗan gwagwarmayar kawai shi ne don ya fito ya yi magana kan rashin shugabanci nagari da ake yi a Nijeriya.
Wasu rahotanni ma na bayyana cewa ana zargin ’yan sandan sun lakaɗa wa Sowore duka har ma an ƙarya masa hannu.
Wazirin na Adamawa ya ce wannan abin da ƴa nsanda suka aikata ba ga Sowore kaɗai ba ne, inda ya ce hakan ya nuna cewa za a far wa kowane ɗan Nijeriya da ya yi ƙoƙarin fitowa ya faɗi gaskiya.
“Don haka muna buƙatar a saki Sowore cikin gaggawa ba tare da gindaya wasu sharuɗa ba,” in ji Atiku.
A ranar Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan da ya amsa gayyatar jami’an ’yan sanda domin amsa wasu tambayoyi.
A jiya Laraba ne dai aka bayar da rahoton tsare Sowore bayan amsa gayyatar da ofishin Babban Sufeton ’Yan sanda ya yi masa don ya amsa wasu tambayoyi da suke da alaka da zanga-zangar da tsofaffin ’yan sanda suka yi a makon jiya.
Haka kuma, an son Soworen ya bayar da bahasi kan zargin da ya yi na cewa, Babban Sufeton ya kara wa jami’an ’yan sandan da ke aiki a gidansa girma ba bisa ka’ida ba.
Sai dai ya yi watsi da zarge-zargen, inda ya bayyana su a matsayin borin kunya da hukumar ‘yan sandan take don “dauke hankalin jama’a daga abin kunyar da Babban Sufeton Kayode Egbetokun da kuma hukumar ‘yan sandan ke aikatawa.”
Tuni dai Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ta Amnesty International ta fitar da sanarwar Allah wadai da kamun da aka yi wa Sowore wanda ta ce ya saba wa ‘yancinsa na fadin albakacin baki.
Haka kuma, Amnesty International ta bukaci a saki Omoleye Sowore nan take ba tare da gindaya masa wasu sharuda ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Atiku Abubakar
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ya Kaddamar Da Wasu Tashoshin Talabijin Uku A Dandalin FAST
Kafar yada labarai ta CGTN da ke karkashin babban rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, ta kaddamar da wasu tashoshi uku a dandalin FAST yau Alhamis 6 ga watan Nuwamba, da ke kunshe da tashar CGTN Global Biz, da ta China Travel, da ta Discovering China. Wadannan tashoshin za su gabatar da shirye-shiryen talabijin zuwa ga masu kallo kusan miliyan 200 a duk fadin duniya, bisa wasu manyan dandalolin FAST guda 15, alamarin da ya shaida babban ci gaban da CMG ya samu a bangaren gabatar da shirye-shirye zuwa sassan kasa da kasa.
Shirin talabijin bisa dandalin FAST, sabon salo ne wanda ya bulla cikin sauri a ’yan shekarun nan a kasuwar shirye-shiryen bidiyo ta duniya, shirin da ya kunshi nau’o’in abubuwa daban-daban bisa goyon-bayan tallace-tallace, kana, babu bukatar masu kallo su biya. (Murtala Zhang)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA