Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II
Published: 7th, August 2025 GMT
Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya ce bai dace a riƙa bai wa mutanen da suka wawure dukiyar ƙasa manyan muƙaman gwamnati kamar ministoci ba.
A cikin shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Sanusi II, ya bayyana damuwarsa game da yadda ’yan Najeriya ke son dukiya fiye da gaskiya da tarbiyya.
Ya ce al’umma na girmama masu kuɗi, ko da kuwa an san kuɗin haram ne.
“Ƙasar da ke bai wa mutanen da aka san sun wawure dukiyar ƙasa muƙamin minista, za ta ci gaba da tafiya a doro mara kyau,” in ji Sanusi.
“Ba ma jin kunya idan wani ɗan siyasa ya tara dukiya ta hanyar da ba ta dace ba, sai ma mu yi masa tafi.”
Sanusi ya ce mutane da dama yanzu na shiga siyasa ne don su tara kuɗi, ba don su yi wa jama’a aiki ba.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan shugabanni suna auna darajarsu ne da adadin gidajen da suke da su, jiragen sama masu zaman kansu, ko kuɗaɗe a asusun banki.
Ya ce ba su damu da irin kyakkyawan tasirin da suka yi wa al’umma ba.
Ya kuma ce rashin tarbiyya da gaskiya a tsakanin shugabanni na ƙara raunana tsarin gwamnati gaba ɗaya.
A cewarsa, wasu ba su damu da abin da mutane za su ce game da su ba muddin sun mallaki dukiya.
Yayin da yake tunawa da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja, Murtala Muhammed, Sanusi ya ce Najeriya na buƙatar dawo da kyawawan ɗabi’u irin na shugabannin da suka gabace mu.
“Muna buƙatar daidaita ɗabi’unmu gaba ɗaya,” in ji shi.
“Ba wai shugaban ƙasa ko gwamnoni kaɗai ba ne za su canja ƙasa, kowa na da rawar da zai taka.”
Ya ƙara da cewa ’yan siyasa sun lalata tsarin aikin gwamnati, kuma Najeriya na buƙatar gina tsari mai ƙarfi da zai bai wa ma’aikatan gwamnati damar ƙin amincewa idan suka nemi su karya doka.
Sanusi, ya jaddada cewa kamata ya yi al’ummar Najeriya ta bai wa ɗabi’u kamar gaskiya, aiki tuƙuru, da tausayawa fifiko sama da tara dukiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan siyasa Ɓarayi Rashin Gaskiya Sarki Sanusi II
এছাড়াও পড়ুন:
Cinikin Kamfanoni a Kasar Sin Ya Ci Gaba Da Habaka Cikin Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Bana
Bayanin da Hukumar Haraji ta Kasar Sin ta fitar ya nuna cewa, a rabin farko na wannan shekara, kudaden cinikin da kamfanoni a duk fadin kasar suke samu ya ci gaba da karuwa cikin kwanciyar hankali. Masana’antu sun sami ingantaccen ci gaba yayin da manufofin “sabunta manyan kayan aiki na kasa” da “Maye gurbin kayan amfani da suka tsufa da sababbi” suka yi tasiri sosai.
Kudin da aka samu a bangaren sana’ar kere-kere ya karu da sauri fiye da matsakaicin karuwar dukkan kamfanoni da kashi 1.5%.
Wannan ya tabbatar da cewa masana’antu su ne tushen karfafa tattalin arzikin kasar.
Kazalika, masana’antun kirkire-kirkire sun kara habaka, inda kudaden da aka samu a bangaren sayar da kayayyaki na masana’antun kimiyya mai inganci ya karu da kashi 14.3% idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Abin da ya nuna ci gaba mai sauri a wadannan bangarori. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp