UNICEF Ya Samar Da Abinci Mai Gina Jiki Ga Yara Sama Da 17,000 A Kano
Published: 8th, August 2025 GMT
Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa yara miliyan 11 da ke ƙasa da shekaru biyar a Najeriya na fama da rashin abinci mai gina jiki, lamarin da ke ƙara yiwuwar wani yanayi mai barazana ga rayuwa saboda rashin kuzari.
Shugaban Ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahma Rihood Mohammed Farah, ya bayyana haka yayin mika kayan kayan abincin na musamman da aka sayo ta hanyar haɗin gwiwar gwamnati da UNICEF a shirin Child Nutrition Match Fund, wanda aka gudanar a Cibiyar Kiwon Lafiya (PHC) ta Karamar Hukumar Takai.
Mista Rahma, wanda Daraktan Lafiya na UNICEF, Dakta Serekeberehan Seyoum Deres ya wakilta, ya ce kashi 51.9 bisa 100 na yaran Kano suna fama da mat girma saboda rashin abinci mai gina jiki, yayin da sama da kashi 10 suke fama da matsalar rashin nauyi da zai ba su kuzari.
A cewarsa, Child Nutrition Match Fund shiri ne da UNICEF ke kula da shi, tare da goyon bayan masu bayar da tallafin ƙasashen waje, inda ake bayar da kuɗi daidai-da-daidai (1:1 match funding) domin ninka jarin da gwamnatoci ke sakawa wajen samar da muhimman kayan abinci mai gina jiki.
Ya bayyana cewa Jihar Kano ta zama jagora a ƙasa wajen wannan ƙoƙari, inda ta bayar da gudummawar Naira miliyan 500 – mafi girma daga jiha guda – zuwa wannan asusu. Haka kuma shi ma asusun na UNICEF ya ƙara Naira miliyan 500, wanda ya kawo jimillar Naira biliyan 1. Wannan kuɗin aka yi amfani da shi wajen sayen kwalaye 12,948 na hadin abinci mai gina jiki da zai warkar da yara sama da 17,000 masu fama da matsanancin rashin abinci mai gina jiki.
Dakta Deres ya bayyana cewa UNICEF na fassara child food poverty a matsayin rashin damar samun abinci mai gina jiki, mai yalwa, da kuma bambancin sinadaran gina jiki ga yara ‘yan ƙasa da shekaru biyar – wani lokaci mai matuƙar muhimmanci wajen haɓakar jiki da kwakwalwa.
Ya jaddada cewa UNICEF tare da hadin gwiwar masu tallafi sun samu gagarumar nasara wajen inganta abinci mai gina jiki a faɗin Najeriya, musamman a Kano.
Ya yabawa jagorancin gwamnati tare da kira ga Gwamnan Jihar Kano da ya ware ƙarin kuɗi a shekarar 2025, wanda UNICEF za ta sake bada kwatankwacinsa domin a sake sayen sinadirai da kayayyakin abincin.
Haka kuma ya bukaci a amince da manufofin bayar da hutun haihuwa na tsawon watanni shida mai ga matan da suka haihu, domin ƙarfafa shayar da jarirai nono zalla da kuma kare lafiyar jarirai da abincinsu.
Asusun na UNICEF ya sake jaddada aniyar sa ta tallafawa Jihar Kano ta hanyar haɗin gwiwar dabaru masu faɗi a fannoni daban-daban domin inganta abinci mai gina jiki da lafiyar al’umma musamman ga mata da yara.
Daga Khadijah Aliyu
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
Dantsoho ya bayyana cewa, a taron Tashoshin Jiragen Ruwa na Duniya da aka yi a Kobe, Kasar Japan, shugabannin tashoshin jiragen ruwa na Afirka sun yi alƙawarin haɓaka ci gaban Tashoshin yankin ta hanyar tsarin dabaru uku – aiwatar da manufofi, sabunta haɗin gwiwa, da sauƙaƙe ciniki, wanda wannan shi ne abin da NPA ta ƙuduri aniyar aiwatarwa.
Shugaban na PMAWCA ya kuma yaba wa gwamnati da mutanen Jamhuriyar Congo saboda ɗaukar nauyin taron kuma ya yaba wa sakatariyar ƙungiyar bisa jajircewa wurin tabbatar da dandamalin tattaunawar tsakanin yankunan da kuma yadda ake samar da sabbin tsare-tsare a shugabancin kungiyar mai kula da teku.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA