Ana Alhinin Tunawa Da Harin Nukiliyar Nagasaki Shekarau 80 Da Suka Gabata A Japan
Published: 9th, August 2025 GMT
Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani.
Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.
Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima.
An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin.
Bayanai sun ce a yau mutane sama da 2,600 daga ƙasashe sama da 90 sun halarci taron tunawa da wannan rana a bikin da aka gudanar da filin taro na garin Nagasaki.
Firai ministan ƙasar Shigeru Ishiba ya fara buɗe taron da jawabi da misalin ƙarfe 11:02 dai-dai lokacin da makamin ya dira a garin, a wani ɓangare na girmama waɗanda suka rasa rayukansu, kafin !bisani kuma aka rika kaɗa ƙarararwa don tunawa da ruhinsu.
An saki gwamman tattabaru da ke alamta zaman lafiya bayan da shugaban ya kammala jawabi, inda ya ce wannan taro ya shiga cikin kundin tarihin ƙasar wanda za’a gajeshi ƴaƴa da kakanni.
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Hari
এছাড়াও পড়ুন:
Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
An kashe wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan a wani hari da ’yan bindiga suka kai wani shingen bincike, inda suka ɗauke bindigarsa bayan sun halaka shi a Jihar Taraba.
Wata majiyar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na dare a garin Tella, cikin Ƙaramar Hukumar Gassol, lokacin da ’yan bindigar suka yi wa shingen binciken ƙwanton ɓauna.
An ce maharan sun harbi ɗan sandan ne a kansa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa nan take, lamarin da ya sa sauran abokan aikinsa da ke wurin suka tsere.
Bayan sun yi kisan, ’yan bindigar sun ɗauke bindigar marigayin sannan suka tsere daga wurin.
Kakakin rundunar ’yan sandan Taraba, ASP Leshen James, bai ɗaga wayar kiran da aka yi masa ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa dangane da lamarin ba.