Aminiya:
2025-09-17@22:08:06 GMT

Yadda matar gwamna ta sa mata gasar haihuwar ’yan uku

Published: 28th, April 2025 GMT

A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Nijeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato.

Burin wadannan mata ta karu ne sakamakon yadda farin ciki nau’i uku ya lullube Malama Bela’u Sabo da iyalanta, bayan da ta haifi ’yan uku a garin Kaurar Yabo da ke Karamar Hukumar Yabo ta jihar.

Rasha ta ayyana tsagaita wuta ita kaɗai a yakinta da Ukraine Shekara 10 ina sayar da sassan jikin ɗan Adam — Wanda ake zargi

A yayin da mai jego da angon karni da ’yan uwa suke tsaka da murna, wannan karuwar haihuwa ta kara jawo musu sha-tara ta arziki, inda matar gwamnan jihar, Hajiya Fatima Ahmad Aliyu, ta taso takanas zuwa kauyen ta domin yin barka.

Zuwa barkan wadannan ’yan uku ya faranta ran ba ma iyalan mai jegon ba, har ma da daukacin al’ummar garin Kaurar Yabo, domin kuwa, shi ne ziyarar farko da matar gwamnan Jihar Sakkwato ta taba kawo musu.

A yayin gaisuwar ne matar gwamnan ta gwangwaje Malama Bela’u da akwatuna uku cike da kayan fitar suna da tufafin jarirai da ragunan suna guda uku da buhuna 10 na hatsi da kuma tsabar kudi naira dubu dari biyar.

Ta kuma yi alkawarin bayar da irin wannan tallafi ga duk matar da ta da samu karuwar ’yan uku a jihar, lamarin da ya sa mata neman Allah Ya sa su a danshin wannan mai jego.

Haihuwar ’yan uku ta zo min da sauƙi — Mai jego

Malama Bela’u Sabo a tattaunawa da wakilinmu ta ce “a lokacin da na samu karuwar na yi tawakkali da Allah, kuma yaran da na samu Allah Ya yi masu albarka.”

Wakilinmu ya nemin jin yadda yanayin cikin da kuma haihuwar ’yan ukun ya kasance wa maji jegon, idan aka kwatanta da ’ya’ya takwas da ta haifa kafin su, inda ta shaida masa cewa, “akwai bambanci gaskiya don su ba su motsi, dayan ma ke dan motsi can ba a rasa ba.

“Na haife su babu wata matsala ko wahala, cikin sauki suka fito, kan haka ina fatan sake samun ’yan uku in Allah Ya ba ni don suna sanya farin ciki.

“Matar gwamna ta zo ta yi min barka, zuwan ya zo da muhimmanci, ta ba ni kudi dubu 500 da buhu 10 da akwati uku da kwalin sabulu da kwalin Klin da jirgin wanka.

“Yara ta kawo masu kala 42, ta ba ni kala 10 turame da leshi da sauran kayan shafawa, na gode Allah, Ya kuma saka da alheri,” in ji mai jego.

‘Na samu fiye da abin da na roka’

Angon karni, Malam Sabo Kaurar Yabo, ya ce “A lokacin da na samu labarin na samu karuwar yaro uku a lokaci guda, sai na ji kamar an yi min kyautar Aljanna, farin ciki ya mamaye ni.

“Ina buri da rokon Allah Ya ba ni tagwaye sai na samu uku gaba daya, wannan ita ce haihuwa ta tara, yanzu ina da ’ya’ya 11 da mace guda.

“Har yanzu in zan sake samu ’yan uku zan yi maraba da su ganin yadda suke da dimbin alheri, don matar gwamna ta kawo min raguna da kimarsu ta kai naia miliyan biyu. Sun share min hawayena.

‘Zan so in sami ’yan uku’

Ganin wannan irin kabakin arziki da kuma alkawarin mai tsoka da matar gwamnan ta sa wasu matan jihar kara kwadayin haihuwar ’yan uku.

Wata matar aure mai da daya da ke burin haihuwar ’yan uku, Suwaiba Sani ta shaida wa wakilimu cewa, “Abin akwai farin ciki! Matar gwamna ta kawo maka kaya don haihuwa, ka ga ’yan uku wasu mutane ne na musamman. Zan so in same su, matar gwamna ta hidimta min, na samu daukaka nima.”

A ranar Litinin da ta gabata wakilinmu ya samu labarin an sake samun karuwar ’yan uku a garin Addam da ke Karamar Hukumar Shagari.

Sai dai har zuwa kammala wanann rahoton, matar gwamna ba ta kai ga zuwa garin ba don cika alkawarin da ta dauka.

‘Kayan barka ba sa raino’

Wasu matan jihar da wakilin namu ya zanta da su don jin ko za su so su haifi ’yan ukun, bayan wannan da matar gwamnan ta yi, sun nuna sabanin haka.

Maryam Ibrahim mai ’ya’ya huɗu ta ce ta sha wahalar rainoni tagwaye don haka ba ta son ’yan uku.

“Na samu ’yan biyu a haihuwa ta biyu, kula da su da wuya, ba na burin haihuwar ’yan uku gaskiya, don biyun na san yadda na sha wahalarsu, kayan barka ba su ne raino ba, ni kam hakan bai sauya ra’ayina.”

Sadiya Muhammad ta ce, “Ni ba ni da burin na haifi ’yan uku a rayuwata, amma idan Allah Ya ba ni zan yi murna, yanzu haihuwata biyu ta uku na kan hanya.”

“Alkawarin matar gwamna bai tura ni zuwa sanya raina ga abin da ban gani ba, kuma ita abin buki ne kawai za ta kawo, sauran kula da su har su girma ba ruwanta da shi fa.

“Amma da ta yi wani tsari na daukar nauyin karatun yara zuwa jami’a, da zai sa wasu kwadayin samun yaran don ganin za a rage masu wani nauyi ba harkar buki ba.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Uku Haihuwa Jihar Sakkwato da matar gwamnan matar gwamna ta

এছাড়াও পড়ুন:

Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya

JMI ta zama zakara a gasar damben girgajiya ta kasa da kasa bayan ta fara shiga gasar shekaru 12 da suka gabata .

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana taya tawagar yan damben murna da nasarar da suka samu, ya kumakara da cewa  wannan shi ne nasara ta wasannan kasa-da kasa har guda 6 wadanda Iran take samun lambobin zakara a cikinsu a wannan shekarar.

Labarin ya kara da cewa yan damben Iran sun sami wannan nasarar kwana guda kafin a kammala gasar.

An bayyana nasarar da yan damben Iran suka samu ne a jiya Litinin da yamma a birnin Zagreb inda aka gudanar da gasar. Sun sami lambobin yaboguda 5 a gasar wanda ya basu damar lashe gasar.

Labarin ya kara da cewa tawagar yan damben Iran sun shiga gasar ne shekaru 12 da suka gabata, kuma Amir Hussain Zare ya fita da lambar zinari a dambe mai nauyin kilogram 125.

Bayan ya sami nasara a kan dan wasan Amurka. Ahmad Mohammadnejad-Javan Azurfa daya sannan  Kamran Ghasempour (86kg), da Amirhossein Firoozpour (92kg). Mohammad Nahodi da

tagulla 3.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka An Fara Taron Hukumar Makamashin Nukliya Ta Duniya IAEA Karo Na 69 A Birnin Vienna September 16, 2025 Espania Ta Soke Cinikin Makamai Na EUR Miliyon 700 Da HKI Saboda Kissan Kiyashi A Gaza September 16, 2025 Makaman ‘Drons’ Na Yemen Sun Fada Kan Wurare Masu Muhimmanci A  HKI September 16, 2025 Taron Doha: Daga matakin Allawadai zuwa matakan kalubalantar laifukan Isra’ila September 16, 2025 Ministan Tsaron Venezuela Ya Gargadi Amurka Game Da Yunkurin Juyin Mulki A Kasar September 16, 2025 Pezeshkian: Ya kamata kasashen musulmi su yanke alaka da gwamnatin sahyoniya September 16, 2025 Bayanin Bayan Taron Doha Ya Yi Kira Da A Kafa Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kare Kai September 15, 2025 Fira Ministan Spain: Bai Kamata A Rika Barin “Isr’ila” Tana Shiga Gasar September 15, 2025 Shugaban Kasar Iran Ya Gana Da Sarkin Kasar Qatar A Birnin Doha September 15, 2025  Dan Kasar Iran Mai Kirkira Ya Sami Kyautar Yabo A Kasar China September 15, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
  • Gwamna Namadi Ya Taya Malaman Makarantu Da Suka Yi Fice A Jihar Murna
  • Jihar Jigawa Ta Amince Da Karin Kasafin Kuɗi Na Naira Biliyan 75 Na Shekarar 2025
  • DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya
  • Shawarwarin Sin: Ingantattun Hanyoyi Masu Sauki Na Warware Sabani
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Tawagar Yan Wasan Damben Gargajiya Ta Iran Ta Zama Zakara A Damben Ta Duniya
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Samu Ci Gaba Ba Tare Da Tangarda Ba A Watan Agusta