Kissoshin Rayuwa: Imam Al-Hassan 114
Published: 28th, April 2025 GMT
114-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi.
///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah(s) diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.
A cikin shirimmu da ya gabata, mun yi maganar yadda Khalifa Uthman ya wanye da Ammar dan Yasir ( R), mun ji yadda Ammar ya tashi da shi da iyayensa suka fara karban musulunci a Makka, da kuma yadda suka yi shahada a hannun Abu Jahal, sannan yadda Ammar ya kubuta daga sahrrinsa bayan ya fadi abinda suke so, ba da sonsa ba. Amma alkur’ani ya sauka yana tabbatar masa da Imani.
Sannan munji yadda manzon All…(s) yake himmantuwa da al-amarin Ammar don Yasir ba don iyayensa su ne shahidar na farko a makka ko a musulunci ba, sai har da cewa yana da Ikhlasi da kuma tsoron All… don haka manzon All..(s) yana girmama Ammar dan yasir ne saboda tsoron All…da kusancinsa da shi. Saboda a hadisan da aka karbo daga gareshi (s) dangane da Ammar suna maganane a kansa, kamar . Inda yake cewa. All..kayi fushi da wanda yayi fushi da Ammar. Sannan manzon All..yayi masu alkawali da shiga aljanna tun suna Makka, inda yake cewa: Ya ku yan gidan yasir kuyi hakuri laillai makomarku aljanna ce.
Sannan munji yadda ya narke a cikin son Aliyu dan Abitalib (a) bayan wafatin manzon All… Da kuma yadda Khalifa Uthman ya sa aka dakeshi har ya suma, har sau biyu.
A cikin shirimmu nay au zamu yi magana kan yadda aka yi wa Imam Alhassan (a), dangane da wai yana son Khalifa Uthman, kuma yana bakin ciki da kissansa, wanda Taha Hussain ya kawo a cikin littafinsa –Fitnatul Kubra.
Wasu malaman tarihi sun ruwaito hadisan kariya sun jinginawa Imam Alhassan dan Aliyu dan Abitalib (a) dangane da Khalifa Uthman, sun riya cewa Imam Alhassan (a), yana daga cikin masoyan khalifa Uthman, kuma yana sonshi har cikin zuciyarsa. A cikin rayuwarsa da kuma bayan kashe shi.
Dr Taha Hussain yana daga cikin wadanda suka tafi a kan wannan ra’ayin, inda yake fada cikin littafinsa Ftnatul Kubra, yana cewa” Hassan (a) bai gushe ba yana son Uthman, ya kasance masoyin Uthman ne da gaske, sai dai bai zare takobi don neman fansar jininsa ba, don bayan ganin hakan hakkinsa ne, wasu lokutan yakan wuce gona da sonsa Uthman har sai da a fadawa babansa (Imam Ali) abinsa dai dace ba. Kamar yadda, masu ruwaye sun ruwato daga Ali (a) ya wuce dansa Imam Hassan (a) yana alwala, sai ya ce masa, ka kyautata alwala, sai ya bashi wannan amsar mai daci, inda wai yana ce masa (hakika kun kashe wani mutum a jiya yana kyautata alwala). Sannan Aliyu (a) bai kara wani abu ba sai wannan Kalmar, (hakika All..ya tsawaita sonka ga Uthman).
Sai dai idan muka dubi wannan ruwayar wanda Taha Hussain ya kawo shi don karfafa ra’ayinsa, hakaka Balaziri ya ruwaitoshi, dada Mada’in, a cikin littafinsa ‘Al-ansabul Al-ashraaf JZ 5 sh 81, Shi wannan Mada’ini an sanshi da kin iyalan gidan manzon All..(a) , wato nasibi ne, sannan an sanshi da kirkiro hadisai na yabo da goyon baya ga banu umayya, yana jinginawa manzon All..(s).
Kuma manufarsa da kirkiro wannan hadisin ita ce tsarakaka banu Umayya, ta jikan manzon All..(s) mai tsari Imam Hassan (a). Don ya nuna cewa salihan bayi kamar Jikan manzon All..(s) yana son Uthman. Banda raunin sanadin wannan hadisin, ga wasu karin abin lura a cikinsa.
01- Idan har da gaskiya ne, Imam Ali (a) ya na son yi wa dansa gyara a alwalarsa, to me yasa Imam Hassan (a) zai fada masa wannan kalmomi masu daci?, Sannan A lokacinda aka kashe Khalifa Uthman, Imam Hassan (a) yana dan shekara 32 a duniya bai iya alwala ba? Imam Hassan (a) ya tashi a gaban manzon All..(s) yana dan shekara 7 a duniya, kakansa manzon All..(s) ya kaura daga wannan duniya, amma bai koyawa jikansa na farko, alwala ba?
Sai ya yana dan shekara fiye da 30 ne babazansa zai koya masa al-walah, ? ko way a san wannan ba haka yake ba.
Sannan ina hadisin nan da aka bayyana cewa Imam Hassan da Hussain (a) suka ga wani dattijo bai iya alwala ba, sai tunda su yara ne a lokacin sai suka yi dubara ta kyautata masa al-walansa, inda dayansu yayi alwala irin na dattijo sai dayan kuma yayi alwala mai kyau, sai dattajan ya gano cewa da shi ake nufi sai ya gyara alwalansa. ?
Wanda ya nuna cewa Imam AlHassan da Alhussain (a) suna koyawa mutane alwala tun kakansu manzon All..(s) ya na da ransa a duniya.
02-Sun ce Imam Alhassan (a) yana daga cikin masu kare khalifa Uthman a lokacinda yan tawaye suka yiwa gidansa kofar rago, kuma yana haka tare da Umurnin babansa Imam Ali(a) ne, to ta yaya a wannan hadisin Imam Hassan yana zargin babansa da kashe Uthman? .
Al-hali mun san cewa Imam Hassan yana tare da mahaifinsa, a yakin Jamal da kuma yakin siffin, a lokacinda yayi wadanda suke tuhumarsa da kashe Khalifa Uthman, suna cewa suna yakarsa ne don daukar fansar jinin Uthman. Imam Alhassan da Alhussain duk suna tare da mahaifinsu a wadannan wurare suna goyon bayansa, kuma basa tuhumarsa da kashe Khalifa Uthman.
Wannan ya tabbatar mana cewa, Mada’ini ya kirkiro wannan hadinsin ne tare da manufar da muka bayyana.
03-Ayyukan Uthman ne suka kasheshi, ya dorawa mutanen Masar da Kufa danginsa suka yi ta kashe su da kuma zaluntarsu, sun kawo kokari a Madina ya ki amsa korafe-korafensu, a lokacinda ya amsa kiran mutanen masar, daga baya ya warware.
A nan sai suka ce ko ya sauka daga khalifanci ko kuma su kasheshi, da yaki sauka suka kashe kashe. Imam Ali (a) bai da hannu ko kadan wajen kissan Khalifa Uthman, ta yaya dansa Imam Hassan (a), kamar yadda ya zo a cikin Hadisin Mada’ini, zai tuhum- babansa da kissan Uthman, kamar yadda wannan hadisin yake cewa, ya san cewa ba haka ne ba.?
Amma abinda ya faru kafin kissan Khalifa na uku, shi ne cewa, Khalifa Uthman ya aikata abubuwan da dama wadanda basu dace ba, har sai ya kai ga ba wani kare shi a cikin sahabban manzon All..(s) a Madina.
Hatta, talha da zubai da Abdurrahman bin Auf, wanda ya dorashi kan khalifancin, kuma wadanda ya yi masu ni’imoni, masu yawa, sun dawo daga rakiyarsa.
Duk sun dawo suna fushi da shi. Ta yaya wadannan sahabban manzon All..(s) da salihan bayi daga cikinsu wadanda muka ambata a baya, kamar Abuzar, Ammar, Abdullahi dan Mas’ud da Aliyu dan Abi talib da sauransu duk suna aibata shi. Amma sai Imam Hassan (a) ya zama ya na sonsa?. Ba zai yu ba.
Don haka tare da wannan zamu ga cewa, ba kuma wata kima ga wannan Hadisin a sanadinsa da mataninsa. Abin mamaki shi ne, ta yaya Taha Hussain bai yi bincike mai zurfi a cikin wannan hadisin ba har ya zo ya fada cikin wannan tatsuniyar.
Don haka a lokacinda ayyukan Uthman suka zama abin tattaunawa a ko ina a Madina da sauran manya manyan garuruwan musulmi, sai zabubbu cikin sahabban manzon All..suka taro suka yi shawara, suka kuma yanke shawara kan cewa dole ne su sauya shugabancin musulmi. Don haka suka aika wasiku zuwa manya manyan kasashen musulmi suna neman taimakonsu da makamai da kuma sojoji.
Ga Nassin abinda ya zo cikin daya daga cikin wasikun da suka rubuta. Wannan wasikar zuwa ga mutanen Masar.
{Daga muhijiruna na farko, da sauran shura, zuwa ga wadanda suke kasar Masar, daga sahabbai da kuma masu binsu wato (tabi’ina), Bayan haka:
Da ku zo wajemmu, ku kawo dauki ga khalifancin manzon All..(s) kafin ma’abutanta, su kwaceta su kwaceta, to lalle lillafin All.. an sauya shi (ba’a aiki da shi),kuma sunnar manzon All..(s) an sauya ta, kuma hukunce, hukuncen khalifofi biyu an sauyasu, Muna hada All…kan cewa duk wanda ya karabta wannan takardan, daga cikin sahabban manzon All…(s) da suka saura, da mabiyansu da kyautatawa, face ya taho mana, don ya karbo mana hakkimmu, kuma mu bashi hakkinsa, to ku zo mana idan har kunyi Imani da All..da ranar lahirah, (ku zo ku) ku tsaida gaskiyar bisa tafarki bayyananniya wanda manzonku (s) ya barku a kanta, kuma wacce khalifofi suka barku a kanta, an rinjayemu kan hakkimmu, an mamaye dukiyarmu, kuma an shiga tsakanimmu da al-amarimmu, kuma khalifanci bayan bayan bayan manzon All..(s) ta kasance khalifancin annabi, kuma mai rahama, amma a yau ta zama mulki na zalunci, wato wanda ya sami rinjaye ya ci.. …}.
Wannan kadan Kenan daga wasikar da sahabbai muhajirun suka rubutawa suran sahabban a wasu wurare, kuma Ibn Kutaiba ya kawo ta a cikin littafinsa Al-imama wassiya shafi na 35.
Sannan wadan wasikar ta ambaci abubuwa da dama wadanda suka fadawa daular musulunci da musulmi saboda mulkin Uthman.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: wannan hadisin
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda ’yan Tifa da baƙin direbobi ke haddasa haɗari a Abuja
Rayukan al’umma gami da dukiya musamman na ababen hawa na ci gaba da salwanta a Mahadar hanya ta yankin Tipper-garage da ke Dutse-Baupma, da ke kan titin da ya tashi daga garin Dutsen-Alhaji ya nufi garin Bwari, a yankin Birnin Tarayya Abuja.
Titin da ke mastayin tagwaye ya haɗa yankin da garin Jere da ke Jihar Kaduna.
Hanyar na ci gaba da ganin ƙaruwar kwararan motoci a sakamakon ingancinta da kuma karancin matsalar tsaro, idan a ka kamanta ta da babban titi Abuja zuwa Kaduna.
Rawar da Arewa za ta taka a Zaɓen 2027 An ɗaure ’yar shekara 80 a kurkuku saboda dukan jikarta da silifasAdadin motoci da ke bin titin ya kara dagawa a bayabayan nan a dalilin mummunan cunkushewar hanya da ake fuskanta a garin Zuba Abuja da kuma Madalla da ke Jihar Neja, a sakamakon rufe hannu guda na hanyar biyo bayan fara aikinsa da wani sabon kamfani ke yi, bayan karbe aikin daga kamfanin Bega.
Baya ga motoci na matafiya da ke yawan ratsawa ta hanyar, akwai kuma motocin tifa da ke daukar duwatsu daga kamafanonin fasa duwatsu biyu da ke kusa da mahadar hanyan suna kai wa yankuna daban-daban na Abuja dama kewaye.
Aminiya ta ba da labarin cewa hatsarin mota na baya bayan nan da a ka fuskanta a hanyar su ne wanda ya auku a ranar Asabar 5 ga wannan watan na Afrilu, 2025, inda a ka rasa rayukan mutum biyar, bayan wata babbar mota tirela da ta fito ta kusurwan Bwari ta fuskanci matsalar tsinkewar birki a yayin da ta ke gangarowa daga hayin madatsar ruwa na Usuma dam da ke kan titin.
Tirelar ta taka kekunan adaidaita sahu guda biyar da ke daukar fasija a gefen hanayar, baya ga wani adadi na baburan acaba.
Kwana biyu bayan aukuwar hatsarin, an sake fuskantan wani a ranar Litinin da ta biyo baya inda wata babbar mota irin ta daukar bulo da ke dauke da albasa daga wata jiha ta Arewa ta rasa birki a yayin saukowa daga gangarar hanyar.
Ta buge kekunan kafin ta kife a kusa da wani magudanan ruwa da ke jikin hanyar.
An bada labarin rasa mutum biyu a yayin hatsarin, baya ga wasu da su ka tsira da raunuka.
Asarar rayuka da ta dukiya da muka yi — Masu tukin adaidaita sahu
Malam Fahad Musa na cikin shugabannin kungiyar ’yan yuniyon na masu sana’ar tukin Keken Adaidaita sahu da ke aiki a wurin.
Ya ce hatsarin farko ya faru ne da misalign karfe 7 na dare inda ya ce sun rasa mambobinsu uku, sai kuma dan acaba guda, a yayin da mutum na biyar din kuwa ya rasa ransa ne a dalilin harbinsa da bindiga da ake zargin wasu da suka taho cikin ayarin motoci suka yi, kamar yadda majiyoyi daban-daban suka shaidawa Aminiya.
Shugaban na ’yan yuniyon ya shaida wa wakilinmu a yayin ziyara a wajen cewa an kuma rasa kekune biyar a yayin hatsarin bayan motar ta bi ta kansu.
Ya ce faduwar motar ta farko ta yi sanadiyyar rufe hannu guda sannan ba a kai ga cire ta ba sai bayan hatsari na biyu a ranar Litinin.
Ya ce, a lokacin da ake kokarin zakulu mutane da suka mutu da kuma wadanda suka yi raunukan daga karkashin ababan hawan a ranar Asabar, an rufe daukacin tagwayen titin biyu da lamarin ya kai ga jawo takaddama bayan ayarin jami’an tsaro sun bulla ta wajen.
Wani da ya shaidi lamarin, ya shaida wa Aminiya cewa, a lokacin da ayarin motocin suka bullo, wani babba a cikin tawagar ya fito daga cikin mota tare da neman da a bude masu daya hanyar, amma sai ’yan asalin al’ummar yankin suka ki amincewa da bukatar hakan.
Ya kara da cewa, matasan sun bi motocin ayarin da jifa bayan sun kutsa ta daya hanyar da nufin wucewa, kuma a nan ne sai wasu daga cikin jami’an tsaron suka yi harbi cikin iska, a yayin da wani kuma ya harbi daya daga cikin matasa ’yan asalin yankin mai suna Timothy John, da ya mutu nan take.
Bayan nan, ayarin sun wuce da motocinsu cikin hanzari, kamar yadda aka bayyana wa Aminiya.
A yayin zantawarsa da Aminiya shugaban n ’yan yuniyon na masu sana’ar tukin adaidaita sahu ya ce, daya daga cikin direbobinsu mai suna Yusuf Auwal na cikin wadanda harsashin bindiga ya bi ta jikinsa.
Ya ce, bayan nan an garzaya da shi zuwa garinsu inda yake cigaba da jinya a yanzu.
Babban Kwamandan Hukumar Kare Hadurra na FRSC mai kula da yankin Dutsen-Alhaji, Mista Luka Wuna, ya tabbatar da faruwan haduran biyun, da kuma rasa rayukan, a yayin zantawarsa da wakilinmu a kan lamari.
Akwai bukatar ilimantar da direbobin Tifa
Binciken Aminiya ya bayyanan cewa, matsalar da tifofi ke samu ta shanyewar burki a yayin da suka ɗauko kaya kuma suka sukwano gangarar da daga ita sai marabar titin ita ce a mafi yawan lokaci ke haddasa munanan hadurra a wannan mahada.
Da yawan direbobin tifa matasa ne da basu san dokokin tuki ba sannan kuma suna tukin da ganganci tamkar suna tuka kananan motoci.
Don haka mafi yawa ba sa kula da yadda suke shawo wannan gangara ta la’akari da cewa, burkin tifa iska ce.
Wani masanin harkokin sufuri da ba ya son a ambaci sunansa ya ba da shaara cewa, ya kamata hukumomin da abin ya shafa su rinka shirya wa direbobin musamman na Tifa bita kan ka’idojin tuki da alamomin hanaya da kuma hatsarin da ke tattare da burkin mota mai dauke da iska.
Abinda ke jawo hatsari a wajen
Malam Anas Mu’azu na cikin ma’aikatan tattara haraji na Karamar Hukumar Bwari da ke ba da tikiti a wajen.
Ya ce, yawancin direbobi da ke fuskantar hatsarin baki ne da ke bi ta gangaren hanyar ba tare da cikakken masaniya a kan yadda wajen yake ba.
Ya ce, ”wutar ba da umarnin wucewa a wajen da ke da kusurwa 4 na bukatar tsayawar mota na wani lokaci a duk ta inda ta fito saboda dogon layi da motoci ke yi, sannan indan wutar ta haska don wucewa, adadi kadan ne na motoci ke iya wucewa kafin ta sake bukatar tsayar da mota,” in ji shi.
Malam Anas ya kara da cewa yawancin bakin direbobi da ke bin hanyar ba su da masaniya a kan tsarin wutar da kuma yanayin hanyar kasancewar babu allunan alamomi na hanya da ke fadakarwa a kan titin.
Ya ce, haka kuma a baya an cire kunyar kan titi da ke sa motoci rage gudun mota. ”A baya akwai kunyar titi na rage gudun da adadinsu ya kai kamar guda biyar, amma sai a ka cire su a lokaci guda ta hanyan kankare su daga kan hanyar,” in ji shi.
Ya ce, ko da Ministan Birnin Abuja Mista Nyesom Wike ya ba da aikin sake gina hanyar a bayabayan nan, ba a maida kunyar titin ba, har zuwa lokacin da haduran baya-bayan nan su ka auku..
Yadda za a magance matsala —Masu Tifa
Haka kuma Aminiya ta zanta da daya daga shugabannin masu motocin tifa da kuma harkar sayar da duwatsu daga kamfanoni biyu na fasa dutsi da ke yankin mai suna Kwamred Ose Idasho inda ya ba da shawarwaari kan yadda ya ke ganin za a magance yawaitar haduran, da ya ce sun bayar a yayin wani zama na musamman da Jami’an Hukumar Magance Hadurra ta FRSC a yankin.
Ya ce, “abu na farko shi ne bukatar a sa alamomin hanya tun daga kamar kilo mita uku kafin mahadar hanyar da zai rika sanar da direba hatsarin wajen tare da bukatar da ya yi takatsantsan.
“Sai kuma a sa abubuwa da ke sa rage gudun mota na kunyar hanya samfurin roba ba na siminta ba, da zai rika yin kara idan direba ya yi yunkurin yin gudu sosai. Hakan zai kara wa direba karsashi ko da ya fara yin gyangyadi.
“Mun kuma bukaci jami’an na FRSC da nemi dauki daga Hukumar Kula da Gine-gine ta Abuja kan su kawar da wuraren da ke sa mutane na tsayawa ta wurin, tare da mayar da shi sarari, sai kuma samar da wurearen yin lodi da kuma hana yin lodi a gefen titin.
“Haka kuma akwai bukatar a gyara wasu daga cikin fitilun ba da hannu da suka daina yin aiki, kamar wanda ya shiga ta bangaren Bamuko ta inda motocin tifa ke shiga da kuma yawan fita.
Sai kuma uwa-uba a gina gadar sama a wajen da zai rage girman gangarowar motoci da ke fitowa ta kusurwar Bwari ko DutsenAlhaji inda motocin za su bi ta saman gada,” in ji jagoran masu motocin tifa.
Ya kamata a gina gadar sama
Shi ma a zantawarsa da Aminiya, Sakataren Hakimin yankin na Dutse-Baupma mai suna Simon Luka da ya yi bayani a madadin hakiminsu, ya ce, hatsarin motoci a wajen ya jima yana jawo masu fargaba da kuma asarar rayuka da dukiya.
Ya buƙaci Ministan Birnin Tarayya Mista Nyesom Wike da ya taimaka wajen yin aikin gadar sama a wajen don magance matsalar.
Ya ce, tarihin farawar matsalar ba za ta gaza shekara 20 bayan an yi aikin hanyar.
Ya ce, matashin da aka kashe bayan jami’an tsaro sun buɗe wuta a wajen mai suna Timothy John, bai wuce shekara 20 ba kuma lamarin ya faru ne kasa da mako guda bayan mai gidansa ya yaye shi daga aikin walda da ya ke yi, inda yake shirin buɗe na kansa.
Ya kara da cewa, “sai dai har zuwa lokacin ziyarar nan babu wata ta’aziyya ko ta jaje da muka samu daga jamiu’an tsaro ko kuma hukuma, kan mutuwar matashin.”
Aminiya ta tuntubi Babbar Jami’ar Hulda da Jama’a a Sakatariyar da ke Kula da Sufuri a yankin Birnin Tarayya Abuja mai suna Misis Lecita Wogu, inda ta buƙaci lokaci don yin tsokaci a kan lamarin.